Da wuya ka samu wani marubuci da ba a taɓa yi masa yaudarar nan ta kan-ta-waye ba, inda ake samun wasu baragurbi a cikin masu harkar wallafa littattafai da kasuwancinsu suna cutar sabbin marubuta da kansu bai gama wayewa da harkar bugawa da cinikin littattafai ba.
Galibi irin wadannan marubutan kan ƙarbi ɗan jarin da suka ƙullo za su fara buga labaran da suka yi wahalar rubutawa da nufin bugawa a yaɗa shi ga masu karatu, amma sai su yi ta shirya musu gadar zare da yaudara, har su karya musu ɗan jarin nasu, a ƙarshe ma su kashe musu gwiwa.
- Kotu ta dakatar da Yakubu Dogara saboda sauya sheka zuwa APC
- A Kannywood ne zaka ga ’ya’yan da iyayensu suka kasa kula da su – Sarkin Waka
Irin wannan na faruwa ne a inda marubuci ko marubuciya suka shiga harkar wallafa da ka, ba tare da yin cikakken bincike don gano yadda harkar wallafa littattafai da kasuwancin su take gudana, da kuma gano mutane nagari da aka san mutuncin su a harkar ba. Saboda zumuɗin son ganin littafin su a kasuwa, da kwaɗayin samun suna a riƙa labarin su cikin fitattun marubuta.
A cewar Aisha Asas, wata ’yar jarida kuma marubuciya daga Jihar Kaduna wacce ta wallafa littafin ‘Wa Da Ƙi’, wannan mummunar halayya ta kan-ta-waye ta cutar da sabbin marubuta da dama a wancan lokacin, inda za ka ga marubuci ya ƙullo ’yan kuɗaɗen sa sai a fara gaya masa, littafin da ya kamata a buga masa a Naira biyar-biyar, sai shi a ce masa goma goma ne, shi kuma saboda rashin sanin dawan garin sai ya amince a haka, idan ya shiga kasuwa da littafin sai ýan kasuwa su ƙi yarda da farashin da zai sa masa, saboda tun a wajen bugawa ya buga da tsada. Idan ma ya yi sa’a an karɓa to, fitar kuɗin sai ya zama masa babban jidali!
Abdullahi Jibrin Ɗankantoma wanda aka fi sani da sunan Larabi marubuci ne daga Jihar Kano, wanda ya wallafa littafin ‘Komai Daɗinki Da Miji’, na daga cikin fitattun marubutan adabi da littattafan su suka yi fice a shekarun baya, amma ya ce kafin ya kai ga fara buga littafin sa na farko mai suna ‘Buwaya’ a shekarar 2000 sai da ya shafe tsawon shekaru biyar yana ta bincike da bibiyar wasu marubuta da ya san idanun su sun buɗe a harkar, da masu buga littattafai, don ya fahimci yadda tsarin yake, kafin ya yi ƙundumbala ya shiga harkar.
Kuma cikin luɗufin ubangiji Allah ya ba shi nasara har ya buga littattafai goma sha ɗaya, kafin daga bisani ya jingine harkar rubuce rubuce saboda wasu dalilai.
Sai dai kuma ita Hajaru Baba Abdullahi wata marubuciya daga Jihar Sakkwato ba ta yi nasara kamar Larabi ba, saboda kuwa ita tun a littafin ta na farko ‘Kishiyar Mafalki’ gwiwar ta ta yi sanyi, domin yadda ýan kasuwa suka riƙa yi mata kan-ta-waye, babu uwar kuɗi ba riba. Wannan ya sa take ganin kamar dai ba ta shiga harkar da ƙafar dama ba, duk kuwa da shauƙin da take da shi na son rubutun adabi.
Shi ma Zaidu Ibrahim Barmo daga Jihar Katsina, wani marubucin littattafan faɗakarwa da ya rubuta littafin, ‘Tarihin Garin Jibiya’, ya ce rashin dawowar kuɗaɗen da yake kashewa wajen buga littattafan da yake rubutawa ya sa shi dakatar da harkar rubutu, saboda yadda ýan kasuwa suka bar shi ba wan ba ƙanin.
Tsakanin shekarar 1990 zuwa 2010 wato tsawon kimanin shekaru 20 ko fiye, kasuwar littattafan Hausa ta yi shuhura sosai, marubutan labaran adabi sun ci duniyar su da tsinke, sakamakon yadda harkar rubutun adabi ke samun bunƙasa da karɓuwa a wajen masu karatu musamman matasa waɗanda a lokacin irin labaran da ake bugawa ke ɗaukar hankalin su saboda labarai ne da jigon su ya fi ƙarfi kan soyayya da jarumta. Ko da yake ko a lokacin akwai masu ganin adabin kasuwar Kano ba komai yake ƙunshe da shi ba, sai labarai na ɓata tarbiyya da ɗauke hankalin matasa daga harkar neman ilimi.
A lokacin da ta fara buga nata littafin a shekarar 2010, Aisha Asas ta samu kasuwar da kwarjininta sosai, har ta samu ta ci gajiyar guminta, abin da ya sa har ta buga wasu ƙarin littattafai guda biyar bayan na farko. A ganinta a lokacin idan marubuciya ta ce harkar rubutu ba ta yi mata kyau ba to, wataƙila ba ta faɗa hannu nagari ba ne.
A cewar ta, a lokacin da kasuwar littattafai ke tafiya, matuƙar marubuci ko marubuciya za su yi rubutu mai ma’ana da zai jawo hankalin masu karatu to, babu shakka ba za ta rasa mamora ba, ko da kuɗin da mutum ya kashe bai dawo duka ba, ba zai dai rasa jarin da zai riƙa juya harkar ba, yana fitar da wasu littattafan.
Sai dai daga baya kasuwar ta fara lalacewa, inda wasu da ba harkar su ba ce buga littattafai ko sayarwa suka shiga cikin kasuwar suka dagula al’amura. Kamar yadda fitaccen marubuci kuma mai harkar buga littattafai Kabiru Yusuf Fagge da aka fi sani da Anka, ɗan Jihar Kano ya koka da wasu masu harkar ɗab’i da ba su san yadda kasuwar adabin Kano take ba, sai su yi ruwa da tsaki su karɓi aikin buga littafin marubuci da bai san harkar ba, su buga masa littafin da ba irin sa ake bugawa ba, wanda kuma farashin sa zai haura fiye da na sauran littattafai da aka saba sayarwa, kuma a dalilin haka sai ya jawo wa marubuci asara.
Ya ce, wasu marubutan gaggawar son su fitar da littafin su kasuwa na hana su haƙurin tsayawa su gyara rubutun da bin ƙa’idojin rubuta labari ta yadda za su fitar da aiki mai inganci, sai su fitar da shi a yadda suka yi kawai. Kuma hakan yana ragewa littafi daraja da kima, saboda masu karatu ba za su ji daɗin sa ba.
Ko da yake wasu na danganta tsadar rayuwa da cigaban zamani ya mayar da harkar rubutu yanar gizo, abin da ya dakatar da marubuta da dama daga harkar, saboda katsewar samun hanyoyin shigar da littattafan da yadda kuɗaɗen su za su dawo, idan sun shiga kasuwar bayan fage ta Online. Kabiru Yusuf Fagge na daga cikin marubutan da suke ganin komawar harkar rubuce rubuce a yanar gizo cigaba ne na abin a yaba saboda duk duniya harkar rubutu ta koma yanar gizo wato online, don yanzu ba kasafai mutane suke cire kuɗi su sayi littafi ba, saboda batun neman na abinci ake yi.
Wata hikima da wasu marubuta suka ɓullo da ita domin rage yawan asarar da suke yi wajen buga littafi ba tare da sun mayar da kuɗin su ko sun samu ciniki ba, ita ce ta amfani da salon ƙaddamar da littafin, inda ake shirya babban taro da gayyatar manyan mutane masu hali, domin sayen littafin da kuɗi mai yawa. A irin wannan lokaci idan marubuci ya yi sa’a ya gayyato masu kishin harkar rubutu, waɗanda kuma suke da ƙarfin aljihu to, a nan yake fanshe wahalar da ya sha. Domin a kwafi ƙalilan sai ya mayar da kuɗin sa har da samun riba, bayan ya ware kuɗaɗen da ya ranta da abubuwan da aka yi masa lamunin su kafin ƙaddamar da littafin.
Hajiya Maryam Tsoho Maidoya daga Jos, wacce ta wallafa littafin ‘Hattara Dai Mata’ ta kuma ƙaddamar da shi, ta bayyana takaicin ta na yadda sau da dama waɗanda ake gayyata taron ƙaddamar da littafi suke yaudarar marubuta, domin kamar yadda akasarin su ýan siyasa ne da ýan kasuwa, za ka ga sun zo sun ambaci wani babban kuɗi wajen sayen kwafin littafin, amma da ƙyar suke iya ba da rabin abin da suka ambata. Wasu ma sai dai ka yi ta kashe kuɗin katin waya ko kuɗin motar zuwa neman su a gida ko ofis, amma haka za ka gaji ka rabu da su da takaici.
A wajen wasu marubutan ba haka abin yake ba, domin kuwa Malama Maryamerh Abdul daga Jihar Borno, da ta wallafa littafin ‘Duhun Damina’ ta kuma samu nasarar ƙaddamar da shi a Babban Birnin Tarayya Abuja a shekarar da ta gabata, ta bayyana irin karamcin da ta samu daga mutanen da ta gayyata, ko da yake ta fuskanci matsalar rashin samun Babban Mai Ƙaddamarwa da ya kamata ya jagoranci taron wajen sayar da littafin makonni biyu kafin taron, wadda ya kamata ta ja ragamar ƙaddamarwar ta janye, saboda wani uzuri da ta ce ya hana ta. Da ƙyar ta samu wani da ya amince ya shige gaba, shi ma saboda zumuncin da ke tsakanin su ne.
Ko da yake a cewar marubuciyar, ta samu damar mayar da kuɗaɗen da ta kashe, na shirya liyafa da gayyatar baƙi, bayan dama wata ƙungiya ce ta ɗauki nauyin buga mata littafin, amma wasu alƙawuran kam sai dai ko a lahira, don har yanzu ba a maganar su!
Yanzu dai da aka riga aka yi jana’izar adabin kasuwar Kano kamar yadda wasu ke faɗa, marubuta da dama sun ajiye alƙalaminsu, sun zuba wa sarautar Allah ido, ko da yake marubuta irin su Larabi da Anka suna cewa tun da zamani riga ne, su ma za su ɗauki tasu su saka. Tuni dai Larabi ya fara fitar da littafin sa na ‘Gidan Darling’ a yanar gizo, don auna yanayin karɓuwarsa ga masu karatu. Sai dai duk da haka ya ce nan gaba yana da burin buga littafin a takarda.
Sai dai duk da haka, marubuciya Maryamerh Abdul na da ra’ayin cigaba da buga littattafai, saboda a cewar ta buga littafi kamar wani tubali ne da kowanne marubuci ya kamata a ce ya taka! Ko da yake har yanzu littafin ta na ‘Duhun Damina’ yana nan jibge ko rabi ba a sayar ba.
To, fa! Marubuta dai sun shiga tsaka mai wuya. Yaya za a yi a dawo da darajar littattafan adabi, ingancin su da karɓuwarsa ga masu karatu, da kuma samar da kasuwar da za ta zama mai mutunta haƙƙin marubuci, ba tare da an sake shiga wata matsalar ta masu satar fasaha a yanar gizo da wata marubuciyar yanar gizo Nana Khadija Sha’aban ta kira da cutar kansar da ke addabar kasuwancin littafi a online.
Khadija ’yar mutanen Zazzau, marubuciyar littafin ‘So Shu’umi’ ta ce, abin takaici ne ka ga marubuci ya wuni yana rubutu, amma sai wasu mutane marasa imani su zo, su canza masa tsarin labarin, su canza sunan marubucin, wasu shahararrun ma har sunan littafin suke canzawa. Wannan ba ƙaramin ci mana tuwo a ƙwarya yake yi ba gaskiya.
Lallai akwai babban ƙalubale a gaban marubuta ta yadda za su farfaɗo da inganta harkar bugawa da kasuwancin littattafai, ta yadda zai tafi kafaɗa da kafaɗa da masu harkar wallafa a yanar gizo. Idan haka ta gagara samuwa to,…