✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda kashin kaji ya samar da ayyuka ga matasa

Dagwalon shara da kamfanonin kiwon kaji suke zubarwa a cikin bola ya samar da ayyukan dogaro da kai ga wasu gungun matasa ‘yan Arewacin kasa…

Dagwalon shara da kamfanonin kiwon kaji suke zubarwa a cikin bola ya samar da ayyukan dogaro da kai ga wasu gungun matasa ‘yan Arewacin kasa da suka yi zaman dirshan a cikin babbar bolar kauyen Arapaja, da ke kusa da birnin Ibadan, suna tara sharar waje daya da rairaye ta da kunshewa cikin buhuna da suke daure su, tare da safararsu zuwa wasu garuruwa da suke sayarwa ga manoma a matsayin taki. Aminiya ta gana da Ummar Sa’idu, jagoran tawagar wadannan matasa. G ayadda hirar ta kasance:
Aminiya: Me ya kawo ku cikin wannan bola da kuka tube riguna kuna aikin kwasar kazanta?
Ummar: Da ni da wadannan abokan aiki da yawanmu ya kai 35, mun kawo kanmu wannan wuri ne, domin gudanar da wannan aiki da muka sa kanmu, tunda muka gano cewa, wannan kashin kaji da ake zubarwa yana da amfani, shi ne, yasa muke zuwa mu kwashe, mu kai Legas da muke sayarwa ga matan sojoji da suke noman ganyen miya, kamar alayaho da shuwaka da ewedu a cikin bariki. Suna yin amfani da shi ne a matsayin taki, kuma suna rububin sayenshi daga hannunmu. Haka kuma da zarar an fara noman gero da dawa a Arewacin kasa sai mu juya akala zuwa can.\
Aminiya: Ya ya kuke safarar wannan kashin kaji zuwa garuruwan da kuka ambata a Legas da Arewacin kasa, kuma nawa kuke sayar da buhu daya ga manoma?
Ummar: Idan muka tara wannan shara muka rairaye ta, sai mu cunkusa a cikin manyan buhunan leda da muke sayowa, mu dinke mu tara su waje daya, sai mu fita kan babbar hanya a cikin gari mu nemo babbar motar tirela, mu yi jinga su kwashe mana zuwa garin da muke bukata. Kuma muna sayar da buhu daya a kan Naira 500 ne, amma a wani lokaci kudin sun zarta haka idan an samu karin kudin mota.
Aminiya: Kamar buhu nawa kuke lodi a kullum?
Ummar: Ba kullum muke lodi ba, muna yin lodi sau uku ko hudu a cikin mako daya. Kuma ana samun yin lodin motaci uku da kowace mota take daukar buhu 50 zuwa 70.
Aminiya: To wadanne ranaku kuke zuwa yin wannan aiki?
Ummar: Ai mu kullum muke zuwa mu riga kowa shigowa, saboda mun dogara da wannan aiki ne wajen samun abin da muke biyan bukatun rayuwa ta yau da gobe. Kuma al’amarin sai godiya ga Allah, domin akwai riba a cikinsa wanda ya fiye mana zaman banza babu sana’a, balle aiki ana korarmu, tare da kama mu a kan hanyoyi ba gaira ba dalili.
Aminiya: A cikin wannan bola mai girman gaske Gabas da Yamma, Kudu da Arewa ko’ina doyin kazanta ke tashi. Ba kwa tsoron kamuwa da wata cuta a daklilin kasancewarku cikin kazanta a kowane lokaci?
Ummar: To, ai dukkan abin da ka saba da shi, kuma ka yarda da Allah, to, kuwa babu abin da zai same ka. Idan ka ga wani abu ya same ka, to, da ma daga Allah ne.
Aminiya: Wacce irin dadewa ka yi a kan wannan sana’a?
Ummar: Yau shekaru 10 da wucewa ke nan da nake yin wannan sana’a kuma ba ni wata sana’a da ta wuce wannan da nake yi a yanzu, domin a cikin wannan sana’a na yi aure da biyan bukatun iyayena.
Aminiya: Wane kira za ka yi ga matasa irin ka da ba su yi ilmin boko ba suke zaune ba aiki ba sana’a?
Ummar: Ina fatan duk wanda ya karanta labarinmu a cikin wannan jarida (Aminiya) ya sanar da irin matasanmu, kuma ya wayar musu da kai su rungumi irin wannan sana’a ta mu, domin tana da muhimmanci sosai ga rayuwarmu. Ina so ka gane cewa, yanzu fa an samu ci gaba a wannan sana’a domin a shekarun baya a Legas kawai muke gudanar da neman wannan kashin kaji; kuma a Legas kawai muke sayarwa, amm yanzu kuwa ka ga muna kaiwa zuwa Arewacin kasa suna saye da daraja, domin sun san amfaninshi ga noman da suke yi.