Kashe jagoran ISWAP, wato reshen Afirka ta Yamma na kungiyar ISIS, lamari ne da ka iya kawo gagarumin sauyi a bangaren tsaro a Najeriya.
An dai samu bambancin bayanai game da hakikanin yadda Al-Barnawi ya rasa ransa – yayin da wani kaulin ke nuna cewa sojoji ne suka kashe shi yayin wata musayar wuta, wani kaulin kuma na cewa fadan cikin gida ne ya yi ajalinsa, ma’ana, an kashe shi ne yayin rikicin shugabanci tsakanin bangarori biyu na ISWAP.
Ko ma dai yaya aka yi, mutuwar Al-Barnawi za ta taimaka wajen haifar da karin hatsaniya a tsakanin ’yan kungiyar, da kuma rashin tsayayyen shugabanci wanda za a rika daukar umarni na kai tsaye daga gare shi.
Wannan ya bai wa jami’an tsaron Najeriya wata babbar dama ta karya lagon mabiyansa da kuma gano sabuwar maboyarsu.
– Kwarewar jami’an tsaro
Sannan wannan shi yake haska cewa lallai jami’an tsaron Najeriya na amfani da kwarewa da sabuwar fasahar zamani don kawo karshen mayakan kungiyoyi irin su ISWAP da Boko Haram a bisa hujjoji kamar haka:
-
Hana su samun damar zirga-zirgar da suke yi a baya.
Takura ’yan ta’adda da hana su sakewa su yi yawo kamar yadda suka saba ya taimaka wajen takaita damar da suke da ita ta kai hare-hare.
Misali, abin da ya taimaka aka kama kakakin Boko Haram Abu Qa’qa’ a Kano shi ne hana shi alaka da wadanda suke ba shi labari — ma’ana, wadanda suke ba shi labari da wadanda suke jinyar sa (saboda ya yi rauni) an kama su, saboda haka bai samu damar arcewa kamar yadda ya saba idan jami’an tsaro sun gano maboyarsa ba.
-
– Toshe hanyoyin kawo musu kayan abinci da sauran kayan more rayuwa.
Wannan ma ya taimaka wajen takaita abin da suke iya yi.
Sun sha wahala saboda sun dogara da kayan abincin da ake kai musu – yanke hanyar samun abinci ya sa sun fito, lamarin da ya sa aka sake kama wasu manyan.
-
Kame manyan masu ba su rahotanni.
Wannan ya sa an gano maboyarsu, har sojoji ke iya shirya musu kwanton bauna.
- Hana su damar samun layin sadarwa, wato network, don yanke alakarsu da ’yan ta’addar da na kasashen waje da sauran boyayyun bayanai wadanda ba zai yiwu na fade su a kafafen yada labarai ba, saboda dalilan tsaro.
- Makamai sun kusa karewa
Misali, kama wasu daga cikin kwamandojinsu wadanda suke shiga gari su ji ko su ga abin da jami’an tsaro ke yi su sanar da su ta waya da toshe layukan waya sun taimaka wajen yin nasara a kansu.
A karshe wannan lamari yana nuna cewa makaman ’yan ta’adda na fuskantar barazanar karewa sakamakon hana masu samun tallafi daga wasu rassan ISWAP.
Wannan ya biyo bayan wani babban aikin kama wasu matane da ake zargin ana amfani da asusunsu na kasar waje don tallafa wa ’yan ta’adda ba tare da galibin mutanen sun san hakan ba.
Detective Auwalu Bala Durumin lya masanin harkar tsaro ne a Najeriya da kasashen waje