✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda kasafin 2021 zai samar wa matasa ayyuka —Lawan

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya yi wa matasan Najeriyar albishir cewa kasafin 2021 zai samar musu karin ayyukan yi. Ahmad Lawan ya bayyana haka…

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya yi wa matasan Najeriyar albishir cewa kasafin 2021 zai samar musu karin ayyukan yi.

Ahmad Lawan ya bayyana haka ne a tsokacinsa kan zanga-zangar #EndSARS, yayin zaman Kwamatin Majalisar kan Harkokin Noma kan kasafin 2021 na Ma’aikatar Noma ta Tarayya.

“Kwanan nan wasu matasan kasar nan sun yi zanga-zanga, wasunsu da kyakkyawar manufa don su karkato da hankulan shugabanni kuma sun yi nasarar jawo hankalin na su.

“Saboda haka, kasafin kudinmu na 2021 zai mayar da hankali ne wurin samar wa matasan Najeriya damar ayyukan yi.

“Matasan sun yi zanga-zanga saboda iya abun da za su iya yi ke nan, wasunsu kuma ba su iya shiga an yi da su ba amma suna tare da masu yi.

“Ba za mu yi kasa a gwiwa ba har sai mun same su a duk inda suke ba tare da sun sake sha’awar yin zanga-zanga ba.

“Galibin matasan mazauna karkara ne don haka za mu isa zuwa gare su don kokarin biya musu bukatunsu, wannan ita ce hanya daya tilo da za mu bi”, inji shi.

Shugaban Majalisar ya bayyana Ma’aikatar Noma ta Tarayya a matsayin wadda za ta kawo sauyi a Najeriya.

Ya ce ma’aikatar na da damar samar da ayyukan yi da bangaren mai ba zai iya samar wa mutane ba sai ‘yan tsiraru.