Kayan masarufi sun karye warwas a kasuwanni sakamakon karancin takardun kudi a sassan Najeriya.
’Yan kasuwa na kokawa kan irin asarar da suke tafkawa, a yayin da farashin kayan abinci, hatsi da dabbobi ya fi kowanne karyewa, sakamakon sabon tsarin CBN na takaita amfani da tsabar kudi da kuma sauya takardun N1,000, N500 da kuma N200.
Binciken da muka gudanar a sassan Najeriya ya kuma gano cewa masu harkar kudi ta POS sai rufe shagunansu suke yi saboda karancin kudin da kuma matsalar intanet da kwastomomi za su tura kudi.
A halin yanzu dai ’yan Najeriya na jiran ganawar Majalisar Shugabannin Kasa, wadda shugaban kasa, tsoffin shugabannin kasa da kuma gwamnoni masu ci za su halarta a ranar Juma’a’.
Bayan zaman ne Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, zai bayyana inda aka kwana kan sabbin tsare-tsaren da suka tayar da kura tare da jefa jama’a cikin tsaka-mai-wuya.
Karyewar kaya a Kano
Farashin hatsi da sauran kayan abinci ya yi mummunar faduwa a kasuwar Dawanau da ke Jihar Kano, inda dole ta sa ’yan kasuwar suka fitar da farashin kaya iri biyu —farashin mai biya da tsabar kudi daban, na mai biya ta intanet daban.
Aminiya ta gano cewa a kasuwar Dawanau, wadda babbar kasuwar hatsi ce a Yammacin Afikra, babban buhun masara da ake sayarwa N22,000 a makon jiya ya koma N14,000 da tsabar kudi, ko kuma N18,000 ga mai biya ta intanet.
Babban buhun gero da ke N25,000 a makon da ya wuce kuma ya koma N15,000 da tsabar kudi, ko N18,000 ga mai tura kudi ta intatet.
Buhun shinkafa mai buntu mai nauyin 100kg kuma ya koma N13,000 daga N23,000 da aka sayar a satin da ya gabata.
Wani dan kasuwar, Malam Inuwa Bello, ya ce a kan dole suke sayar da kaya, ko da faduwa za su yi don su samu abin da za su kula da iyalansu.
Ya ce rashin takardun kudi ya sa kaya sun karye, ko ma ta wace hanya za a biya.
A kasuwar kayan gwari ta ’Yankaba kuma, kwandon tumatir da ke N8,500 a makon jiya ya koma N4,000 saboda rashin ciniki.
Sai dai abin ya sha bamban a Kasuwar Singer ta kayan tireda inda farashin kaya bai sauya daga yadda yake a baya ba.
Farashin dankalin turawa ya karye a Jos
A kasuwannin Jos da ke Jihar Filato kuma farashin dankali, dankalin taurawa da sauran kayan gwari sun fadi warwas.
A kasuwar Farin Gada da ke Jos, kwandon tumatir da a baya ake sayarwa N1,500 zuwa N2,000 ya wuce ya koma N700.
A kasuwar Maikatako, wadda ta yi fice wajen kasuwancin dankalin turawa a Karamar Hukumar Bokkos, farashin dankali ya fadi warwas.
Hauwau Musa, da ke sayar da dankali a kasuwar ta ce yanzu “buhu mai nauyin 50kg na dankali ya koma N6,500 daga farashinsa na N10,000 a makon jiya”.
Kananan manoma sun koka
Wani dan kasuwa a Karamar Hukumar Dukku ta Jihar Gombe, Lukman Umar Mai Besha, ya ce kananan manoma sun fi kowa shiga matsala a wannan yanayin.
Ya ce, “A kauyen Jamari, ranar Juma’a da ta gabata – wadda ranar kasuwa ce — an sayar da buhu mai nauyin 100kg na gero N7,000 sabanin N20,000 da ake sayarawa a baya. Amma duk da haka akwai wadanda suka yi kwantai.
“Masara ta koma N8,000-N10,000 amma kusan babu mai saya; Wake ya koma N19,000 daga N40,000; abin gwanin ban tausayi, kusan babu wanda bai shafa ba, saboda rashin takardun kudi.”
Kaya sun yi kwantai a Legas
Karancin kudi ta sa rashin ciniki a kasuwar Alaba Rago da ke Jihar Legas, inda ’yan kasuwa ke ta korafi kan gazawar kwastomomi wajen samun tsabar kudi don yin sayayya.
Wani mai sayar da kaji, Ahmadu Abdullahi, ya ce kajin da aka sayar N10,000 a watan Disamba da farkon watan Janairu sun koma N6000, amma duk da haka babu mai saye.
Wasu ’yan kasuwa a kauyen Oke-Aro da ke kan iyakar jihohin Legas da Ogun sun bayyana irin asarar da suka tafka sakamakon rashin takardun kudin.
Misis Josephine Onwu da ke sayo kaya miya daga kasuwar Agbado don sayarwa a Oke-Aro ta bayyana cewa farashin kayan ba su canza ba, amma matsalar ita ce tashin farashin abin hawa.
Misis Bosede Lawal da ke sayar da tumatir da barkono ta ce kayanta sun kusa karewa, kuma dole ta rage yawan ranakun da take zuwa kasuwa.
Wani dan tireda a Kasuwa Mile One market, James Obinwa ya ce tun da aka fara karancin takardun ba ya samun ciniki sosai.
A Jihar Kwara, wata ’yar kasuwa mai sayar da waken suya a Karamar Hukumar Kaiama, mai suna Amina ta ce lamarin ya sa ba su da zabi sai dai su koma su zauna a gida.
Wata mai sayar da hatsi mai suna Maimuna a Kaiama, ta ce ta bar sana’ar a halin yanzu saboda rashin uwar kudi da kuma abin kula da kanta.
“Dillalan da ke ba da kudade su ma ba su da shi; yanzu ba mu san yadda za a yi ba, ba mu san yadda za mu rayu ba”, in ji ta.
Wata mai shinkafa da wake, Salamat, a Kasuwar Mandate da ke Ilorin ta ce duk da cewa ba asara suke yi a kayan da suke sayarwa ba, matsalar ta rage yanayin cininkinsu da ma harkar hatsi.
Daga: Sagir Kano Saleh, Sunday M. Ogwu, Kamarudeen Ogundele, Simon E. Sunday, Dalhatu Liman, Muideen Olaniyi (Abuja), Eugene Agha, Yvonne Ugwuezuoha (Legas), Victor Edozie (Fatakwal), Mumini Abdulkareem (Ilori), Ado A. Musa (Jos), Ibrahim M. Giginyu, Lubabatu Garba (Kano), Titus Eleweke (Awka) & Maryam Ahmadu-Suka (Kaduna).