✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya ƙaddamar da shirin tallafa wa manoma a Yobe

Gwamnatin ta samar da kayan tallafin ne don inganta samar da abinci a jihar.

Shugaba Bola Tinubu, ya ƙaddamar da tallafin noma na biliyoyin Naira ga manoman Jihar Yobe da aka zaɓo daga mazaɓu 178 a jihar baki ɗaya.

Gwamnatin Jihar Yobe, ta samar da tallafin kayayyakin aikin noman don inganta samar da abinci a jihar.

Shugaban wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya wakilta, ya nuna cewa noma muhimmin abu ne da ya kamata a bai wa muhimmanci a kowane mataki.

“Na yi farin ciki da na shiga Yobe bisa manufar samar da abinci, kuma babu hanyar da za mu iya cimma burinmu da manufofinmu ko a jiha ko ƙasa har sai mun tallafa wa manomanmu, kuma mu tabbatar da cewa sun mallaki kayan aikin noma na zamani don inganta nomansu.”

A jawabinsa mai masaukin baƙi, Gwamna Mai Mala Bunu, ya bayyana cewa shirin rabon ya ƙunshi manoma 30 daga gundumomin zaɓe 178 da ke jihar, wanda adadin manoma 5,340 ne za su ci gajiyar shirin.

“Sai dai tarakta guda 100 da aka samar da kuma taki duk za a bada su ne a ofisoshin ma’aikatar noma da ke ƙananan hukumomi da shiyyoyin da ke jihar yayin da duk sauran kayan aikin noma da kayayyakin amfanin gona za a bayar kyauta za a bayar da su ga manya da matsakaitan manomanmu da ke jihar kamar yadda aka tsara.

“Ƙoƙarin da muke ganin zai ƙara haɓaka ci gaban aikin  noma mai yawan gaske a jihar shi ne a gabanmu.

“Saboda haka ina ƙara tabbatar muku cewa mutanen Jihar Yobe nagari za su ci gaba da ba gwamnatinku goyon baya yayin da kuke ƙoƙarin inganta tattalin arziƙi, tsaro, da sauran ƙalubalen ci gaban ƙasa da ke addabar al’umma baki ɗaya.”

Gwamnan ya bayyana cewa: “Jihar Yobe kamar yadda kuka sani na ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar tsaro.

“Rashin isa ga filayen noma sakamakon barazanar tsaro da sauran abubuwan da suka shafi yanayi kamar zaizayar ƙasa, kwararar hamada, ƙarancin ruwan sama da sauransu ya yi tasiri matuƙa ga ayyukan noma tare da samar da babban sakamako ga rayuwar al’ummarmu da suka fi yawa a fannin noma, da kuma tattalin arziƙin jihar gaba ɗaya.

“Duk da ƙalubalen da ake fuskanta, aikin noma shi ne babban abin da ‘yan Yobe ke damuwa da shi lura da cewar, akasarin al’ummar jihar manoma ne.”

Don haka, ya sanya aikin noma ya zama muhimmin fanni na shirin farfaɗo da tattalin arziƙin bayan shuɗewar ayyukan ‘yan tada ƙayar baya.

Gwamnatin Jihar Yobe ta yi amfani da waɗannan dabaru don farfaɗo da fannin noma bayan shirya muhimman taro kan harkokin aikin gona domin tsara wani sabon tsari na inganta samar da kayayyakin abinci.

Gwamnatin jihar tana da kundin tsarin mulki na kwamitin gudanarwa kan farfaɗo da aikin gona, da samar da tsare-tsare na sassan jihar tare da haɗin gwiwar gidauniyar Bill and Melinda Gates.

Ta kuma samar da daftarin manufofin noma don cimma nasarar samar da abinci da bayar da gudunmawa ga haɓaka tattalin arziƙin ƙasa baki ɗaya.