- Babu wata karuwa da muke da su — Jama’ar gari
- Muna bakin kokarinmu — Kamfanoni
- Ba mu da masaniya — Gwamnatin Kano
Al’ummomi da dama a sassan Jihar Kano da kamfanoni ke aikin fasa dutse na kokawa kan yadda suka ce kamfanonin na ci da guminsu ta hanyar barazana ga muhallansu ba tare da biyan su cikakkiyar diyya ba.
Sun kuma yi korafin cewa irin wadannan kamfanonin, wadanda galibinsu ba ma na ’yan kasa ba ne ba su cika daukarsu aiki ba ko samar musu da ababen more rayuwa kamar asibitoci da famfunan da ruwan sha ko makarantu.
Sai dai kamfanonin sun ce suna iya bakin kokarinsu wajen ganin sun yi abin da za su iya, musamman kasancewar ba su fara aikin ba sai da suka sami izinin gwamnati.
Yayin da wasu daga cikin wadannan kamfanonin, kamar na yankunan unguwar Sauna da ke karamar Hukumar Nassarawa da unguwar Tashar Kulili a karamar Hukumar Rimin Gado, suke zaman na dindindin, wasu kuwa na wucin gadi ne da aka kafa saboda ayyukan gina tituna.
A daya daga cikin irin wadannan yankunan na Tashar kulili, Aminiya ta zanta da mazauna garin, inda suka yi korafin cewa a cikin sama da shekara 10 da irin wadannan kamfanonin suke aiki a yankin su, ba su taba tsinana musu komai ba.
‘Kamfani ya kashe mana hanyar zuwa gona’
Abdullahi Magaji daya daga cikin mazauna garin na Tashar kulili, ya yi korafin yadda daya daga cikin kamfanonin da ke yankin ya kashe musu hanyarsu daya tilo ta zuwa gona a wajen fasa dutsen.
Ya ce, “Ita kadai ce hanyar zuwa gonakinmu, mun zuba amfanin gona amma kuma wannan hanyar ita kadai ce hanyar da muke bi don wucewa da amfaninmu ga shi sun kashe mana ita.
“Muna kira ga mahukunta da su kawo mana dauki dangane da wannan hanyar, saboda Mu bamu da yadda za muyi.
“Bayan wannan kuma, babu wata hanya da muke amfana da wannan kamfanin. A lokuta da dama sukan dauki ma’aikata amma ba sa daukar mutanenmu, in ban da wasu mutum biyu da suka taba dauka direbobi kusan shekara takwas da fara aikinsu.
“Duk da cewa suna daukar direbebo da sauran ma’aikata, amma ba su taba dauka daga cikinmu ba in dai ba wadannan direbobin ba. Mutanen unguwar nan sun je da Mai Unguwa sun yi korafi a kan lamarin, amma har yanzu shiru,” inji shi.
Tun kafin kamfanin su fara aiki muka fara samun matsala da su – Mai Unguwa
A cewar Mai Unguwar Tashar kulili, dan-Azumi Mai Unguwa ya ce tun kafin ma kamfanin ya fara aiki suka fara samun matsala da su kan batun kashe musu hanyar.
Ya ce, “Wannan hanyar ta dade shekara da shekaru, wannan ma’aikatan sun zo za su yi aiki suna so su kashe ta zuwa inda suke aiki, ni da kaina naje na same su mun yi magan sunce min za su yi mana wata hanya wacce tafi wannan. Amma har zuwa yanzu dai babu wani abu.
“Wannan hanyar ta hada mu da wurare da yawa, daga nan har Tofa take zuwa, ban da gonakin mutane da kananan kauyuka da ke hanyar. To ita suke so su toshe ta tsaya iya kamfaninsu.”
Illar da kamfanonin ke yi wa muhallanmu
A cewar Mai Unguwa dan-Azumi, a duk lokacin da kamfanonin suka yi aikin fasa duwatsun, bangwayen gineginensu na tsagewa.
“Akwai kamfanoni uku da ke aiki a yankinmu, daga ciki biyu sukan yi aiki, amma na ukun bai fara ba dai tukunna.
“Kamar yadda na fada maka, mun zauna da su kuma mun yi yarjejeniya da su a kan idan suka fara wuta [fasa dutse], duk ginin da ya sami matsala sun ce a fada musu za su duba su yi abin da ya dace.
“Mun yi haka da su a baya kuma sun yi, amma dai abin bai taka kara ba ballantana ya karya, musamman idan aka yi la’akari da girman barnar. Kawai dai hakuri muke da su.
“Akwai cutarwa a duk lokacin da suka yi aikin fasawar, domin akwai wani hayaki da yake tasowa ja-jawur wanda masana sun tabbatar mana yana da illa.
“Amma saboda ba mu da yadda zamu yi dole sai hakuri. Mun yi duk abin da ya kamata mu jawo hankali na taimako, amma lamarin ya ci tura.”
Basaraken ya yi kira ga gwamnati da ta rika sa ido kan abin da yake faruwa a yankunan nasu.
“Hatta ruwan da muke sha, duk ya kafe dalilin wannan fasa duwatsun. Akwai gulabe biyu duk sun kafe kuma sanadin wannan aikin,” inji shi.
Da Aminiya ta tambaye shi hanyoyin da suke samun ruwan, sai ya ce a famfunan tukatuka suke samu, kuma idan ya lalace wani lokacin ma su suke hada kudi su gyara, ba ruwan kamfanonin da su.
“Mun taba kai musu korafi su gyara mana, amma ba su yi ba, amma dai sun yi a Rimin Gado. Daman ruwan na rafi ne muke sha, amma ko da ana amfani da shi, idan ya zo ruwan yakan yi jawur, sai dai mu ba dabobi. Sai dai mai unguwa danAzumi ya ce akwai wanda ya taba samun matasalr rashin lafiya, amma kamfanin ya yi kokarin kai shi asibiti, kuma ya biya kudin magani.
“Akwai kuma wata mata da dutse ya taba fada mata, haka ita ma suka kai ta asibitin Nasarawa, suka biya komai.”
Ya kuma ce a tsawon sama da shekara takwas, daya daga cikin kamfanin na ’yan asalin kasar China ya yi yana aiki a yankin, akalla sama da gidaje 60 da ke kewaye da su ba su taba amfana da wani abin ku-zo-ku-gani ba.
‘Ba kashe musu hanya muka yi ba, za mu yi musu wata’
Sai dai Aminiya ta nemi jin ta bakin daya daga cikin kamfanonin da ake nuna wa yatsa, musamman kan batun zargin kashe hanya, inda ya ce suna nan suna kokarin yi musu sabuwa, wacce ta fi tasu ta da.
Wani ma’akacin kamfanin da ya yi magana a madadinsa, ya ce, “Lokacin da muka zo nan muka fara aiki, mun fahimci cewar akwai hanya anan. Amma saboda yanayin aikin da za mu yi a wannan wajen sai muka yanke shawarar gina wata sabuwar hanya kada ya zama muna aiki mutane na cutuwa da hakan.
“Amma rashin fahimta da aka samu shi ne duk ya jawo hakan. Da zarar mun kammala wannan aikin za mu gina musu sabuwa.
“Dangane da batun yin wani abu kuwa, mu kamfaninmu yanzu ya fara aiki, kuma da zarar mun fara, za mu rikk yin duk abin da ya dace,” inji shi.
‘Aikinmu na wucin-gadi ne’
Shi ma da yake maida martani kan wasu daga cikin zarge-zargen, daya daga cikin kamfanonin, wanda shi ne yake aikin titin Kano zuwa Katsina, yace su fasa duwatsun nasu ba na kasuwanci ba ne, da zarar sun gama aikin titin za su tashi.
Mai magana da yawun kamfanin, Yahaya Muhammad, ya ce aikin titi ne ya kawo su yankin, “amma duk da haka, duk abin da ya faru a lokacin yin aikin, ko wani wanda aikinmu ya shafi gidansa ko lafiyarsa, za mu biya diyyar barnar.
“Sannan duk da haka, duk abin da ya shafi taimako ga mazauna kauyukan a kan lamarin, Insha Allahu za mu yi.
Malam Garba Sani mazauni kuma ma’aikaci dake yankin Kurosha a unguwar Sauna ta karamar Hukumar Nassarawa a inda ake fasa dutsen, cewa yayi sun tashi sun ga ana aikin fasa dutse a wannan waje, wanda cikin ikon Allah Ya sa suka shiga sahun ma’aikatansu.
Yace kamfanin nayi musu ayyukan jinkai kamar tona rijiyar burtsatse.
Da muka tambaye shi ko akwai wata barazana da aikin yake yi musu, sai ya ce akwai tazara tsakanin gidajen mutane da wajen fasa dutsen, saboda kamfanin ya ma riga mutane zuwa wajen, shi ya sa ba su cika samun korafekorafe ba.
Shi ma Muhammad Abdullahi, mazaunin unguwar Sauna Kawaji, ya ce kalubalen da suke fuskanta ba shi da yawa saboda ana kula da su.
Da aka tambaye shi ko akwai wata barazana ga gine-ginensu, sai ya ce, “Eh, muna samu, amma saboda yawancin mu ma’aikatan kamfanin ne, wasu kuma suna da yara ko yan uwa da ke aiki a kamfanin, hakan ya sa ba ma kai korafi wajensu.
Sani Dauda kuwa, wanda mazauni ne kuma ma’aikacin a wannan kamfanin ya ce dukkan gidajen da ke unguwar suna nesa da kamfanin kuma ba sa fuskantar barazana.
Ba mu da masaniya – Gwamnati
Sai dai da Aminiya ta tuntubi Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Kano, mai magana da yawunta,Malam Sunusi Kofar Na’isa, ya ce sam ba su da masaniya a kan korafekorafen saboda ba a taba kawo musu koke a kai ba.
Sai dai ya ce za su bincika idan akwai bukatar daukar mataki.