Al’ummar Jihar Kano dai har yanzu na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu game da yadda aka yi Murja ta fita daga gidan gyaran hali, bayan gurfanar da ita a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Gama PRP.
Ana ci gaba da samun rudani a tsakanin al’ummar Jihar Kano a daidai lokacin da ake zargin fitacciyar ’yar TikTok din ta tsere daga gidan gyaran hali na Jihar Kano.
- Zanga-Zanga saboda tsadar rayuwa ba mafita ba ce — Sarkin Musulmi
- Haƙƙoƙin ma’aikatan lafiya a wurin marasa lafiya
Aminiya ta ruwaito cewa, Kotun Shari’ar Musulunci da ke Gama PRP a Jihar Kano ita ta bayar da umarnin tsare jarumar a gidan gyaran hali na Kurmawa.
Tun dai a ranar Talatar da ta gabata ce Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kama jarumar, wanda a cewarta ta yi hakan ne bayan ta samu korafe-korafe daga wurin al’ummar Unguwar Tishama da Murja ke zaune a kan halayen da take aikatawa na tayar da hankali da kuma bata tarbiyyar ’ya’yansu.
A lokacin da aka gurfanar da ita a gaban kotun ana zargin ta da koya wa kananan yara karuwanci.
Sai dai bayan karanto mata laifukan da ake zargin ta da su jarumar ta musanta aikata laifukan.
Alkalin kotun Mai shar’ia Nura Yusuf Ahmad ya bayar da umarnin tisa keyarta zuwa gidan gyaran hali tare da dage shar’iar zuwa ranar 20 ga watan Fabrairu, don yanke hukunci game da batun bayar da belinta kamar yadda lauyanta ya nema.
Yayin da yake mayar da martani a kan wannan zargi, mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali na Kasa, Musbahu Lawan K/Nassarawa ya tabbatar da cewa tun a ranar Alhamis aka saki Murja.
A cewarsa, “Gidan gyaran hali yana tafiya ne bisa doka. Wuri ne kamar banki da takarda ake amfani.
“ Takardar ce take kawo mutum, haka kuma takarda ce ke fitar da shi. Idan da a ce da wani kuskure to ba za a karba ba.
“A takaice kotu ce ta kawo Murja, ita ce kuma ta fitar da ita.”
Da yake bayani kan batun, mai magana da yawun kotunan Shari’ar Musulunci, Muzammil Ado Fagge ya ce, ba su masaniyar ficewar Murja daga gidan yari.
Ya kara da cewa, “mun ji labari cewa ta fita daga gidan gyaran hali. Mu dai a iya saninmu Alkali ya kai ta ajiya. Ba mu san abin da ya faru ba.”
Wata majiya mai karfi a Hukumar Hisbah ta ce ita aikinta shi ne ta kama, amma ba ita ce mai hukunci ba, haka kuma ba ita ce za ta fada wa alkali abin da zai yi ba.
Haka kuma Hisbar ta ce wannan abu da ya faru ba zai sanyaya mata gwiwa wajen kokarin da suke yi na ganin an kawar da badala a fadin jihar ba.
Al’umma dai na ci gaba da lugudan labba, musamman a shafukan sada zumunta na zamani a kan yadda aka yi Murja ta tsere da kuma wanda ya fitar da ita daga gidan gyaran hali.
Majiyar Aminiya ta shaida mata cewa, kwana daya kacal Murja ta yi a gidan gyaran hali ba kamar yadda ake cewa an fitar da ita daga gidan gyaran halin bayan ta shafe kwana uku ba.
Wasu mutane a Jihar Kano suna ganin cewa, Murja ta nuna matsayinta kamar yadda take ikirari a shafukanta na sada zumunta.
Wasu kuma na ganin cewa ta samu fita daga gidan gyaran hali ne bisa gargadin da ta sha yi cewa idan an matsa mata to fa za ta fasa kwai.
Barista Badiha Abdullahi Mu’az lauya ce mai zaman kanta a Jihar Kano, ta shaida wa Aminiya cewa shi bayar da belin dama ce ta alkali, don haka alkali yana da ikon ya bayar da beli a duk lokacin da ya so matukar laifin da ake tuhumar mutum ba na bayar da beli ba ne.
Al’ummar Jihar Kano na ganin cewa, Gwamnatin Jihar Kano ce ta wuce gaba wajen fitar da Murjar, zargin da gwamnatin ta musanta ta hannun Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar, Baba Halilu Dantiye, inda ya ce babu hannun Gwamnatin Kano a cikin batun fitar da Murja daga gidan gyaran hali.
Kwamishinan Shari’a, Barista Isah Dederi bai amsa kiran da wakiliyarmu ta yi masa ba.
Tambayar da wasu suke yi ita ce, shin gaskiya ce batun da ake cewa masu gabatar da kara, wadanda tun a lokacin da aka gurfanar da Murja a kotun Gama suka karbe lamarin daga hannun dan sanda mai gabatar da kara, inda suka yi ikrarin cewa Kwamishinan Shari’ar ne ya turo su kotun, su ne suka wuce gaba wajen fitar da Murjar, cewa wai akwai wasu sababbin tuhume -tuhume a kanta wanda suke son su fadada bincike a kai?
Wannan tambayar da wasu tambayoyin ma Aminiya ta yi kokarin samun karin bayani daga Kwamishinan Shari’ar, amma hakan bai samu ba.
Sai dai duk wannan turkaturka da ake yi Hukumar Hisba ta jihar wacce ita ce ta kama Murja ta yi shiru a kan batun, lamarin da ya jawo aka yi ta yada labarin cewa,
Babban Kwamandan Hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi murabus daga kan kujerarsa, zargin da mukaddashinsa kuma Mataimakinsa a bangaren ayyuka, jagoran operation kau da badala, Dokta Mujahideen Aminudden ya musanta.
Sai dai wata majiya a Hukumar Hisba da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa Aminiya cewa, wannan abu ya karya musu gwiwa domin sun yi kokarin kama Murja domin yi mata hukuncin da ya dace da ita, amma aka yi watsi da wahalarsu.
Majiyar tamu ta kara da cewa, sun sha matukar wahala a wajen kamun Murja domin sai da suka shafe awa uku kafin ta fito daga gidanta.
A tattaunawar da Aminiya ta yi da wasu al’ummar Jihar Kano sun nuna cewa, tun farko mutane ne suke goya wa Murja da mukarrabanta baya ta hanyar bibiyarsu a shafukansu na sada zumunta, lamarin da ya jawo suke kara baje-kolinsu.
Kwamared Aminu Naganye na daga cikin wadanda ke da wannan ra’ayi, inda ya shaida wa Aminiya cewa, “Idan ba don ana bibiyar Murja ba ta yaya za a yi ya zama tana da masu bibiya sama da mutum miliyan biyu?
“A ra’ayina, da a ce ita ma Hisba ta gudanar da wannan gyara da take kokarin kawo wa ta wata hanyar, amma ba ta wannan hanyar ba, domin ba abin da take yi illa kara wa Murja karbuwa da yawan jama’a a bangaren masu amfani da kafafen sada zumunta na zamani.”
Ita ma wata da ta nemi a boye sunanta ta shaida wa Aminiya cewa, “mutane suna jin dadin irin barnar da Murja take yi shi ya sa suke bibiyarta.
“Da za a ce mutane su daina kallon ta tare da bibiyarta, wallahi da tuni ta daina abin da take yi.”
A ranar Talatar da ta gabata wato 20 ga watan Fabarairu ce ranar da Alkali ya sanya domin mayar da Murja gaban kotu, inda tun da sassafe jami’an ’yan sandan farin kaya suka kawo ta kotun.
Haka kuma ba a ga fuskokin lauyoyin gwamnati masu gabatar da kara ba, wadanda a baya suka ce Kwamishinan Shari’a na Kano ne ya turo su don su karbe shari’ar daga hannun ’yan sanda.
Haka kuma rashin zuwan nasu ya hana a ji sababbin tuhume -tuhumen da aka yi ta yadawa cewa lauyoyin suna yi wa Murja, wadanda kuma za su gabatar wa kotu a wannan rana.
Bayan kotun ta zauna, dan sanda mai gabatar da kara, Aliyul Abidin ya gabatar wa kotu Murja Kunya tare da ambaton laifukan da ake tuhumar ta da su.
Daga nan ne Alkalin Kotun, Mai shari’a Nura Yusuf Ahmad ya bayar da umarnin a kai Murja asibiti domin gwada kwakwalwarta, inda ya kara da cewa duba da yadda Murjar take amsawa kotun ya nuna cewa tana da matsalar a kwakwalwarta, wanda watakila ke da alaka da shaye-shaye.
Haka kuma alkalin ya ce, Hukumar Hisba za ta ci gaba da kulawa da Murja, inda kuma ya bukaci ce da ta rika sanar da kotun halin da ake ciki, sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 20 ga Mayu, 2024 don ci gaba da shari’a.
A nasa bayanin, Kwamared Salisu Ado ya ce, “Idan ya kasance an same ta da lalurar kwakwalwa shi ke nan Murja ta ci banza na laifukan da ake tuhumar ta da su, ma’ana ba za a yi mata hukunci ba, tunda dai ba a shari’a da ‘mahaukaci’?
“Ko kuma shi ke nan Murja za ta ci gaba da abubuwan da take yi na sakin layi tunda dai likita ya tabbatar da cewa ita “mahaukaciya ce?”
Za mu maka Gwamnatin Kano a Kotu — Lauyoyin Murja
Lauyoyin Murja sun ba Gwamnatin Jihar Kano wa’adin awanni 24 da ta ba su izinin ganinta ko kuma su maka ta a gaban kuliya.
Hakan na kunshe ne cikin wata takarda da lauyoyin Murjar — Aliyu Usman Hajji da Saddam Sulaiman — suka fitar suna kalubalantar matakin ci gaba da hana su ganin wadda suke karewa.
Wadanda lauyoyin suka zarga da hana su ganin Murjar sun haɗa da Asibitin Muhammad Abdullahi Wase da ke karkashin kulawar Hukumar Asibitocin Jihar Kano da Hukumar Hisbah ta jihar da Magatakardan Kotun Shari’ar Musulunci ta Kwana Hudu PRP.
A cewar lauyoyin Murja, “bisa bincikenmu wacce muke karewa ta yi biyayya ga umarnin kotu inda a halin yanzu tana Asibitin Kwararru na Muhammad Abdullahi Wase (Asibitin Nassarawa) karkashin kulawarku.”
Lauyoyin sun kara da cewa, “sai dai a ranar 22 ga watan Fabarairun mun nemi ganin ta don tattaunawa da ita, amma an hana mu ganin ta wanda hakan ya ci karo da Kundin Tsarin Mulkin Kasa na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima.
“A matsayinmu na lauyoyi mun sani cewa kowane mutum yana da ’yancin ganin lauyansa musamman a lokacin da ake tuhumarsa da aikata laifi kamar yadda take kasancewa da Murja a yanzu.
“Don haka daga wannan lokaci mun ba Asibitin wa’adin awanni 24 da su yi gaggawar janye matakin da suka ɗauka na hana mu ganin ta domin hakan keta haƙƙin biladama ne.”
A wata takarda da Aminiya ta sami kwafin ta gano cewa takardar gargadin ta isa ga Asibitin Kwararru na Muhammad Abdullahi Wase da kuma Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, inda wasu jami’an hukumomin biyu suka rattaba hannu akan takardar da ke nuni da cewa sun karɓi takardar a hannunsu.