Fitaccen Malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya ce raina addini ne da raina Alkur’ani a kori makaranta Alkur’ani daga wani gari a kasar nan.
Shehin Malamin ya bayyana haka ne a martanin da ya mayar cikin wani jawabin da aka yada a kafafen sadarwar zamani, kan kama almajiransa a gidansa da Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi a ranar Alhamis din makon jiya a Kaduna.
- Matar aure ta kashe budurwar da mijinta zai aura
- Gobara ta tashi a masana’antar rigakafin COVID-19
- Dattijuwa mai shekara 60 ta kashe kanta
Ya ce kowane dan Najeriya duk inda yake zaune gidansa ne, babu wanda ya isa ya kore shi.
Don haka ina aka samu damar korar makaranta Alkur’ani a mai da su gidajensu?
Kama almajiran Shehin Malamin ta jawo cece-ku-ce tare da shan suka daga almajirai da masana a kafafen watsa labarai da na sadarwar zamani.
“Wannan raina Kur’ani ne da raina addini da rashin sanin girman Kur’ani da rashin sanin addinin ya sa ake haka.
“Mu masu karatun Alkur’ani ’yan kasa ne muna da hakki muna da ’yanci,” inji shi.
Sheikh Dahiru Bauchi, ya ce abin da ke bata rai gwamnatin da ta wuce ta gina wa almajirai Tsangaya alhali shugabanta ba Musulmi ba ne.
“Sai kuma aka samu wata gwamnati, shugabanta Musulmi ne, masu iko tare da shi yawancinsu Musulmi ne, amma ya zamo wuraren da aka tanada don almajiran wani wurin sai jakuna ko awaki ko wadansu marasa galihu ne aka zuba a ciki, ba dakunan karatu ba,” inji Shehin.
Ya ce wannan yana bata musu rai, suna ganin ba a kyauta musu ba.
“Ai in an dauki hanya kamata ya yi a dora, amma ba daina ginin za a yi ba, a mai da shi ba komai ba,” inji shi.
Ya ce gine-ginen makarantu wasila ne, karatu shi ne makasid.
“A addini akwai makasid akwai wasa’il. Wasa’il suna tafe tare da zamani, zamani ba ya tsere musu komai gudunsa.
“In ya tsaya su tsaya a bayansa komai dadewa. Amma makasid ba ruwansu da zamani.
“Haka zamani ya same su haka zai tafi ya bar su. Misali masallaci wurin Sallah, to wurin Sallar nan a fili ne ba a samu jera duwatsu ko kafa kara ba, Sallar da ake yi a wurin da Asuba da Azahar da La’asar da Magariba da Isha’i, yadda ake Sallar nan a fili inda za a zo a gina masallacin ya zama gidan sama Sallar da ake yi a wurin ba za a sake ta ba.
“Wadda aka sani raka’a biyu har yanzu raka’a biyu ce, wadda aka sani uku da wadda aka sani hudu ce haka ne ba a canja ba.
“Su ne makasid, ba ruwansu da zamani, zamani nan ya same su kuma nan zai tafi ya bar su,” inji shi.
Ya ce “Ya kamata jama’a su gane rayuwa kamar hannaye biyu na mutum ne, daya yana aiki a sama, daya yana aiki a kasa.
“Daya na cin abinci da sauransu, shi ne na sama. Dayan na wanke kashi da fitsari da sauransu, shi ne na kasa. Amma duk suna taimaka wa juna.
“Idan mutum ya zama mai hannu daya, ba ya da kamala, in ba ka da hannun dama, to, hannun hagun da shi za ka ci abinci ka wanke kashi.
“In ba ka da hannun hagu, hannun dama da shi za ka abinci da shi za ka wanke kashi, shin akwai kamala?”
Lallai ne a nemi ilimi a rayuwa
Shehin Malamin ya nanata cewa lallai ne a yi wadannan ilimomi biyu, mutum ya yi ilimin boko gwargwadon yadda zai dade a duniya, ya yi ilimin addini gwargwadon yadda zai dade a Lahira.
“Kun taba jin wani ya je Lahira don ya dade ya dawo? Babu dawowa in an je.
“Kuma ba za ka tafi tsirara ba, dole kana neman sutura, ba za ka kwanta a fili ba kamar dabbobi be, dole ka nemi daki.
“Ba za ka zauna ba hukuma ba kamar namun daji, to wannan rumfar dole su ma ka yi musu aikinsu, don masu hikima suna cewa: ‘Ka yi aiki don duniyarka, kamar za ka dawwama. Ka yi aiki don Lahirarka, kamar za ka mutu gobe.’
“Saboda haka mu zauna a kan haka, mu bai wa hannun dama hakkinsa mu bai wa hannun hagu hakkinsa,” inji shi.
Ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya tura Zaidu bn Sabit ya je ya koyo masa rubutun Nasarawa ko Yahudawa, wato ilimin da ba namu ba ne, domin ya zo ya karanta masa wasikun da za a aiko ko ya rubuta amsar da za a bayar.
“Ashe daga gaban Annabi (SAW) aka fara karatun boko tare da na Musulunci ana hadawa.”
Dole kowane da ya yi karatu a gaban iyayensa –Manjo Rimi
Da yake kare samamen da aka kai ga gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi a garin Kaduna da tsakar dare aka kwashe almajiransa da dama daga makarantar a lokacin da suke barci, Shugaban Kwamitin Tabbatar da bin Dokokin Yaki da Cutar COVID-19 na Jihar Kaduna, Manjo Garba Yahaya Rimi (mai ritaya) wanda kwamitinsa ne ya kai samamen ya shaida wa Aminiya cewa suna gwajin cutar COVID-19 ga wadansu daga cikin almajiran da aka kwashe daga gidan.
Wadansu kuma tuni sun mika su ga shugabanin kananan hukumomi, musamman ’yan asalin jihar, wadanda ba ’yan kasa ba kuma sun mika su ga jami’an Hukumar Shigi-da-Fici.
Da aka tambaye shi ko an samu wadansu da cutar, sai ya ce bai sani ba, domin wannan alhakin ma’aikatar lafiya ce.
A kan ko hakan wani yunkuri ne na hana karatun allo ake yi a jihar, sai ya ce, “Ai abin da doka ta ce shi ne kada ku shigo da yara daga wasu jihohi.
“Su gwamnoni 19 ba shugabanninmu ba ne ba? Idan suka tattauna suka yarda da wannan, me ya kamata mu yi?
“Ai addini ya ce ka bi shugabanninka ko? Idan (malamai) suna da korafi sai su nemi gwamnonin Arewa su ce su fa ga korafinsu sai a ga yadda za a gyara.
“Amma ba za a saka doka wani ya zo ya karya dokar ba, bai kamata ba.”
‘Malaman ma sun yi rashin gaskiya’
Ya kare kai samamen cikin dare da cewa: “Waccan lokaci da ake bi ana kwashe almajiran ai boye su (malaman) suke yi, idan aka boye su aka je makarantar babu kowa, me aka yi ke nan?
“Su ma ya kamata su rika yin gaskiya domin Allah Ya ce a yi gaskiya.
“Idan ba ka yi gaskiya ba, an ce ka dauke almajiran nan ka mayar da su gaban iyayensu ka ki, ka dauke su ka kai su wani wuri ka boye su ba ka yi gaskiya ba.”
Shugaban ya ce, “Idan muna maganar mu Musulmi ne sai mu yi abin da addinin Musulunci ya gaya mana.
“Kuma idan akwai wani korafi sai su nemi shugabanninmu, su gaya musu ga abin da su suka gani ta yadda za a gyara, amma ba su yi haka ba.
“Ita gwamnati Allah ke kawo ta kuma Allah Ya ce a bi shugabanni.”
Shin yunkurin hana karatun allo ne?
Kan zargin ko manufarsu hana karatun allo ne sai ya ce: “Da ma an ce ko a cikin gari yaro ya je ya yi karatunsa ya koma gida, ba wai ya zo ya yi karatu ba, kuma ya hau kan titi yana bara, shi ne gwamnati ba ta yarda da shi ba.
“Kai kanka danka na makaranta, me ya sa yake komawa gida idan an tashi ba ya yawo a kan titi yana bara.
“Kuma dukkanmu muna da ’ya’ya da jikoki, ba za mu so mu ga ’ya’yanmu na bin kan titi suna bara ba.
“Yaran nan yaranmu ne kuma Allah ne kadai Ya san me za su zama gobe, idan suka rayu cikin natsuwa.
“Amma sai ka ga yaro ya sanya gari cikin kokon bara yana yawo kan titi yana cewa ka taimaka masa da kudin sukari.
“Yaron nan idan ya tashi a haka zai dauka daidai yake yi, tunda yaro ne don haka mu rika tunawa da Ubangiji.
“Gwamna cewa ya yi idan an kama yaro dan Jihar Kaduna a mika shi ga shugaban karamar hukumarsa shi kuma ya mika shi ga iyayensa a saka shi a muhammadiyya da boko a gaban iyayensa.
Idan ya taso daga wannan sai ya je wancan, idan an tashi ya koma gidan iyayensa ai hakan ya fi ko,” inji shi.
Ya ce wannan aiki da kwamitinsa ke yi a duk kananan hukumomi 23 ake yi, ba don gidan mutum daya ba ne kawai.
Akwai bambanci tsakanin bara da almajiranci –Modibbon Gusau
A wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar 18 ga Janairun nan, Modibbon Gusau kuma Shugaban Kungiyar Jama’atu Tajdidil Islamiy, Sheikh Aminu Aliyu Gusau, ya ce akwai bambanci a tsakanin bara da almajiranci (wanda yake nufin zama dalibin makarantar allo).
Malamin ya ce idan duk an yarda cewa barar kananan yara aba ce marar kyau da ta zama wajibi a kawo karshenta.
“Shin za mu iya cewa tsarin makarantun allo ba ya da kowane irin amfani ga al’ummar Musulmi a kasar nan?” Ya yi tambaya.
Ya ce hujjar da gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa ta kama almajiran Sheikh Dahiru Bauchi a gidansa ta fakewa da dokar da gwamnonin Arewa 19 suka kafa, ya kamata a yi tambayar ko dokar ta iya bambance tsakanin bara da makarantar allo ta kwana?
Sheikh Aminu Gusau wanda tsohon Mashawarcin Gwamnan Jihar Zamfara ne kan Makarantun Allo ya ce, makarantun allo a Arewa suna fama da matsaloli uku ne da suka hada da tsarin barar kananan yara da tsarin makarantun allo da ya zama tsohon yayi a idon wadansu da kuma haramta wa kananan yara karatun boko.
Yayin da ya goyi bayan gwamnatocin su yi dokar hana yara bara, tare da hukunta iyaye da malaman da suke da hannun kan haka, ya bukaci gwamnatocin su fara da wayar da kan jama’a kafin daukar wannan mataki.
Da ya juya kan matsala ta biyu, Modibbon Gusau din ya ce, “Makarantun allo su ne asalin makarantunmu na ilimi tun kafin zuwan Turawa.
“Da Turawa suka shigo ne sai suka kawo nasu tsari na makarantun boko, wadanda suka kasance su ne gwamnati take tallafawa, su kuwa makarantun allon aka bar su a hannun daidaikun malamai.”
Ya ce makarantun allo kashi uku ne da suka hada da zaunannu na kwana da zaunannu na je-ka-kadawo da kuma makarantun ci-rani.
Ya ce makarantun ci-rani su ne wadanda malamai ke yawo da yara gari-gari.
“Gwamnati a nan za ta iya yin dokar hana makarantun ci-rani, domin takaita yawo da kananan yara zuwa wurare masu nisa da kashe barar kananan yara,” inji shi.
Ya ce a yanzu mafi yawan makarantun allo na je-ka-ka-dawo, sun zama na yamma da yara ke zuwa bayan sun dawo daga makarantun boko, sai dai a kauyuka inda iyaye da yawa ba su saka yaransu a makarantun boko.
Ya ce makarantu zaunannu masu tsarin makarantun kwana, akwai masu bara da wadanda ba su yi.
Kuma suna da wasu matsaloli da suka shafi wuraren kwanciya da na zagayawa da yadda za a samu abinci cikin sauki da kiwon lafiya da muhalli da tarbiyya da kuma dakile yara daga samun ilimin boko.
Ya ce irin wadannan makarantu ya kamata ne gwamnatoci su samar da ofisoshi na musamman domin hulda da su. “Sai a shata musu dokokin da za su taimaka ga duk malamin da ke son ya gudanar da makarantar kwanan ta tafi tare da zamani, kuma a rika tallafa musu,” inji shi.