✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda kalaman Nnamdi Kanu suka fusata tsofaffin Shugabannin Najeriya

Najeriya ta ce ba za ta kau da kai ga kalaman Nnamdi Kunu ba.

Tsofaffin shugabannin Najeriya sun ce kasar ba za ta kawar da ido ta kyale irin kalaman da ake zargin shugaban kungiyar ’yan awaren Biafra ta IPOB da furtawa ba.

Shugabannin, wadanda suka halarci wani taron gaggawa ta intanet da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta ranar Juma’a, sun fusata ne da kalaman na Nnamdi Kanu, wadanda ake zargin sun haifar da kazancewar zanga-zangar #EndSARS ta hanyar haddasa kone-kone da sace-sacen dukiyoyin gwamnati da na al`ummar kasa, da kuma kashe-kashe na ‘ba gaira ba dalili’, musamman a Legas da sauran jihohin kudancin Najeriya.

Tuni dai gwamnatin Najeriya ta daura aniyar rubuta takardar korafi ga gwamnatin Birtaniya a kan lamarin.

Tsofaffin shugabannin kasar da suka halarci taron da sun hada da Janar Olusegun Obasanjo da Janar Yakubu Gawon da Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Abdulsalam Abubakar da Cif Earnest Shonekan da kuma Dokta Goodluck Ebele Jonathan.

Sai dai kawo yanzu ba a samu cikakken bayani a kan abin da aka cimma a taron da tsoffin shugabannin kasar suka yi ba, duk da dai wata majiya da ta cancanci a gaskata ta ta kara haske cewa sun tattauna sosai a kan umurnin da Kanu bayar, wadanda suka rura watar rikicin na Legas, da kuma nemo hanyoyin shawo kan lamarin.

Majiyar ta ce tuni gwamnati ta fara magana da kasashen waje domin bin diddigin fitintinun da kalaman suka haifar.

Kalaman Nnamdi Kanu 

A cikin kalaman jagoran na IPOB da suka rinka yawo a kafofin sadarwa na zamani, Kanu ya umurci magoya bayansa da su yi basaja cikin masu zanga-zangar #ENDSARS su kuma yi amfani da wannan dama su kashe sojoji da ’yan sanda, tare da salwatar da kadarorin gwamnati da na Bola Ahmed Tinubu.

Ya kuma yi ikirarin cewa shi ya aiwatar da wasu abubuwan ta`asar da suka faru a Legas, wadanda suka jawo cece-kuce a tsakani kabilun Yarabawa da na Ibo.

Umurnin Kanu ya tabbata

Mutane da dama sun tabbatar da cewa kusan duk umurnin da Kanu ya ba magoya bayansa na a lalata kadarorin Bola Ahmed Tinubu su faru.

Idan ba a manta ba, an kai wa wani gwamna hari cikin makon da ya gabata, har aka fasa masa mota.

Akwai rahoton da aka bayar da ya tabbatar cewa an fille wa wani dan sanda kai ranar Alhamis, aka kuma kone gawarsa a lokacin zanga-zangar #EndSARS a yankin Nnewi na Jihar Anambara.

Sai kuma kone ofisoshin ’yan sanda da dama a fadin kasar nan.

Kanu ya karyata zargin

Tuni dai Nnamdi Kanu ya karyata zargin da ake yi cewa ya furta kalaman, amma wata majiya da kusa da gwamnati ta tabbatar wa Aminiya cewa an tantace sahihancin umurnin da ya bayar, tare da tabbatar da cewa daga bakinsa kalaman suka fito.

A cikin takardar da Kanu ya fitar, ya ce bai bayar da umurnin a lalata kadarorin Yarabawa da na Gwamnati Jihar Legas ba.

Ya ce masu bakin ciki ne da hadin kan da ke tsakanin Yarabawa da Ibo ke fitar da bayanan karya domin kawo rashin jituwa da yaki a tsakanin kabilun biyu.

Najeriya ta fara daukar mataki

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce an tura sautin muryar kalaman da umurnin da Kanu ya bayar zuwa Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya, wadda ta shirya rubuta wa gwamnatin Birtaniya takardar korafi.

A takardar, kamar yadda majiyar ta bayyana, gwamnatin Najeriya za ta so ta san matakin da za ta dauka kan shugaban haramtaciyar Kungiyar ‘yan awaren wanda ke zaune a kasar ta Birtaniya, saboda yada kalaman kiyayya da fitina a Najeriya.

Birtaniya ta bukaci sautin

Da aka tuntubi sakatare mai kula da bangaren siyasa da watsa labarai na Ofishin Jakadancin Birtaniya a Najeriya, Dean Hurlock, ya bukaci a tura masa kafar da aka yada sautin muryar da aka nada ta umurnin da Kanu ya bayar.

Ya kuma yi alkawari zai tuntubi hukumar da ta dace kafin ya amsa tambayoyin da aka yi masa.

A nata bangaren, Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya ta ce har yanzu Ofishin Jakandancin Birtaniya bai tuntube ta ba a kan abubuwan da suka shafi jagoran na IPOB.

Daukar mataki

Kakakin Ma’aikatar, Mista Ferdinand Nwonye, ya fada wa wakilinmu ta waya cewar mai yiwuwa za a bai wa Ofishin Jakadancin Najeriya a Birtaniya umurnin ya tuntubi gwamnatin Birtaniyar.

“Babu abin da ya zo daga Ofishin Jakadancin mu na Landan sai dai za mu bincika ko sun san da maganar inda daga mako mai zuwa za a dauki mataki.

“Zan yi magana da manya na in kuma ja hankalinsu kan maganar don zai yiwu a ce Ofishin Jakadancin ya tuntubi gwamnatin da ta ba Kanu mazauni kan maganar.

“Babu dalilin yin irin wadannan maganganu da za su harzuka mutane a daidai lokacin da Najeriya da sauran kasashen duniya ke yaki da annobar COVID-19 da matsalolin tattalin arziki,” inji shi.