An nada shahararren dan TikTok, Alhaji Umar Dan Kawu, wanda aka fi sani da Umar Bush, a matsayin mai ba da shawara a Fadar Shugaban Kasa Bola Tunubu.
Tuni dai Umar Bush ya karbi takardarsa ta fara aiki, wadda ta bayyana cewa ayyukansa sun danganci hulda da jama’a da kuma yada ayyukan ofishin mai gidansa.
An nada Umar Bush a karkashin karkashin ofishin Babban Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Nakasassu da Samun Dama ta Bai-Daya.
Umar Bush, wanda dan Jihar Kano ne, ya shawara ne a TikTok, inda yake fitowa a fusace a kowane lokaci.
Akasarin bidiyonsa a TikTok na rikici ne a tsakaninsa da wani abokinsa Sadiq.
Rikicin nasu da ya ki ci ya ki cinyewa, ya yi silar ganawar Bush da Sadiq da fitattun mutane da manyan attajirai a Najeriya.
A baya-bayan nan, fitattun ’yan TikTok da sauransu daga Kudancin Najeriya sun fara kulla alaka tare da yin bidiyo da Umar Bush.
Lamarin ya kai ga ya fara samu tallace-tallace daga kamfanoni, hadi da gayyatar liyafa daga masu ido da kwalli.
A makon jiya ne aka ga Umar Bush da Sadiq a Fadar Shugaban Kasar Najeriya.
A lokacin ziyarar ce Umar Bush da Sadiq suka hadu da babban attijirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote.