Kabilun Moro’a (Marwa) da na Gworok (Kagoro) dukansu da ke karamar Hukumar kaura da ke Kudancin Jihar Kaduna sun kasance suna gudanar da bukukuwan al’adunsu a kowane watan daya na shekara.
Bukin yana daga cikin dadaddun bukukuwan da ake gudanarwa a Kagoro. Asalin bukin, kamar yadda su ke kiransa da suna Afan, da ke nufin tsauni ko dutse a yarensu, yana da nasaba ne da fitaccen dutsen Kagoro.
Kamar yadda tarihi ya nuna, bayan sun yi girbin, sai su shirya bukin farauta ta yadda suke zuwa su hau saman dutsen, domin a cewarsu, shi ne ke kare su daga harin abokan gaba.
Bukin ya ci gaba da gudana har zuwa lokacin marigayi tsohon sarkin Kagoro Malam Gwamna Awan, wanda ya rasu a shekarar 2008 yana da shekaru 93 a duniya, kuma ya yi sarauta na tsawon shekara 63 (1945-2008), wanda shi ne ya sa aka hade bukin girbin da na sabuwar shekara wanda tun daga nan abin ya ci gaba da bunkasa yana daukan sabon salo ta yadda manyan shuwagabanni na da na yanzu suke halarta.
A kan fara bude bukin ne da karban fareti (maci) wanda ‘yan kungiyar Boys Brigade ke yi, suna tafe suna buga badujala sannan sauran kungiyoyi na makada da maharba da ‘yan rawan gargajiya kowanne zai wuce sannan gwamna ko wakilinsa zai mike don karban faretin.
Bayan kammala wannan kashin, sai a zauna don gabatar da jawabi dabam-dabam tare da sake gabatar da ‘yan rawan gargajiya kowane ya zo ya nuna irin tasa al’adar.
Taken bukin na bana shi ne; Zaman Lafiya, Ginshikin Samun Ci Gaba’. A lokacin da ya ke gabatar da jawabin farko a taron na bana, babban bako mai jawabi, tsohon shugaban Hukumar Kula Da Majalisun Tarayya wato ‘National Assembly Serbice Commission, Abuja, Mista Dare Akau ya bayyana yadda sarakunan gargajiya su ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a kasa, inda ya ce amma abin takaici sai ga shi gwamnatin Jihar Kaduna, karkashin sauye-sauyenta ta yi wa harkar masarautu illa domin a cewarsa, “su ne su ka fi kusa da al’umma.”
Da ya waiwaya kan korar malaman makaranta da sauran ma’aikata, Akau, ya ce “matukar ana bukatar ilmi mai inganci ne da gaske to bayan an duba malaman da ke karantarwa yanzu to a kuma a duba wadanda za su tsinci kansu a cikin aji gobe a matsayin malamai. Dubi yadda gwamnatin jiha ta yi watsi da kwalejin ilmi ta Jihar Kaduna babu kulawa. Na shugabanci makarantar na tsawon shekara biyu amma kalilan ne na tallafi ke zuwa daga gwamnatin Jiha sauran duk daga TETFUND ne.”
A cikin jawabinsa ya sosa inda ya ke yi wa da yawa ‘yan kabilun Kudancin Jihar Kaduna kaikayi inda ya kalubalanci gwamnatin Jihar kaduna da cewa matukar ta ce ba za ta yi magana da kungiyar mutanen Kudancin Kaduna ba (SOKAPU) to bai yi shirin magana da su ba tunda su ita su ka sani. Sai dai ga dukan alamu hakan bai yi wa wakilin gwamnan Jihar Kaduna dadi ba.
Sai dai a lokacin da shi kuma yake jawabinsa, Shugaban riko na karamar hukumar kaura Mista Zitung Basahuwa Agog, yabawa gwamnatin ya yi tun daga matakin jiha har zuwa ta tarayya bisa irin matakan da suke dauka, inda ya yi kira ga gwamnati da kada su bari ayyukan wasu munkirai da ba su kaunar ci gaban al’umma su gurgunta musu kokarinsu.
Shi ma a nasa jawabin, sarkin Kagoro Mista Ufuwai Bonet (OFR) fara yaba wa gwamnatin ya yi wajen kokarin dakile hare-hare sannan ya yi kira ga al’umma da su yi watsi da bambance-bambancen da ke tsakaninsu su rungumi hanyar zaman lafiya.
Shi kuwa a nashi jawabin, Kwamishinan Matasa da Wasani da Al’adu Honorabul Daniel A. Danauta, wanda ya wakilici Gwamnan Jihar Kaduna Mal. Nasir El-Rufa’i, ya ce jami’an tsaro na yin matukar kokarinsu, tare da taimakon gwamnatin jiha don haka ya yi kira ga jama’ar yankin da su rungumi juna su zauna lafiya.
A daya bangaren kuma, a ranar shida ga wata ne su kuma kabilar Moro’a (Marwa) su ka shirya nasu bukin gargajiya na shekara-shekara a garin Manchok, garin mataimakin gwamnan Jihar Kaduna, Bala Banted da ke karamar hukumar kaura.
Shi ma kamar na Kagoro, a kan fara shi ne da yin maci sai gabatar da makadan gargajiya da masu wasanni sannan sauraron jawabi tare da nishadantarwa.
Babban bako mai jawabi a wajen taron shi ne kwamishinan kananan hukumomi, Farfesa Kabir Mato, dan asalin garin Zangon Kataf da ke Jihar kaduna, wanda ya yi magana kan ‘Gudummawar da Harkokin Noma za su Bayar wajen Bunkasa Tattalin Arzikin Kudancin Kaduna’ inda ya bayyana cewa babban illar da aka yi wa kasar shi ne watsi da gwamnatocin baya su kayi da harkar noma tare da dogara kacokan da man fetur wanda yanzu ya zama abin da ya zama.
Farfesa Kabir, ya ce akwai shiri na musamman don samar da filayen noma ga masu bukata a dukanin kananan hukumomin jihar 23, wanda duk mai bukata zai aike da takardarsa don cike sharudan da ake bukata.
A cikin sakonsa, sarkin Marwa Malam Tagwai Sambo, wanda ya cika shekaru 81 a duniya sannan shekara 51 a sarauta, wanda sakatarensa ya karanta a madadinsa saboda tsufa da rashin cikakken lafiya duk da cewa yana zaune a filin. Ya nuna godiya ne kan zaman lafiyan da aka samu sabanin shekarar da ta gabata wanda ba a samu damar yin taron ba saboda rashin zaman lafiya.
Kwamishinan lafiya na Jihar kaduna Paul Manya Dogo shi ne wanda ya yi jawabi a madadin gwamnan jihar, yayinda shi kuma mataimakin gwamnan, Barnabas Bala banted ya yi bayani a matsayin dan kabilar Marwa wanda ya fito daga masarautar inda ya yi wa kowa barka da zuwa sannan ya sake bai wa jama’a hakuri a kan irin matakan da gwamnatinsu ke dauka don tsaftace harkar aikin gwamnati a jihar.
Daga cikin wadanda suka halarci taron na Moroa akwai babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin siyasa, Hon. Gideon Samani da kuma mai taimaka masa kan harkoki na musamman, Hon. Ayuba Malami.
A kan karkare dukkanin bukukuwan Kagoro da Moroa ne ta hanyar buga wasannin sada zumunta na kwallon kafa da yamma.