Wasu kararraki da aka shigar a biranen Landan da New York sun yi karin haske kan zargin yadda wasu kamfanoni suka ba wasu dillalai cin hanci don samun kwangiloli daga Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) kuma aka yi amfani da kudaden wajen yakin neman zabe a zabukan 2015 da 2019 a Najeriya.
Rahoton, wanda Bloomberg ta wallafa, ya ambato jerin wasu tuhumce-tuhumce da wasu tsoffin ma’aikatan Kamfanin Mai na Burtaniya (BP) suka yi kan zargin cewa an biya $300,000 a 2014 da kuma $900,000 a 2018 a matsayin cin hanci domin samun kwangiloli masu tsoka, daga bisani kuma aka karkatar da su wajen yakin neman zabe.
- Yadda matafiya da dama suka makale a Jihar Neja
- Abin da zai kawo mafita daga kalubalen rashin tsaro —Masari
Masu rajin kare Dimokradiyya a baya dai sun sha nuna alamar tambaya kan yadda ake kashe kudade yayin yakin neman zabe da kuma yadda Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ba ta bin diddigin ’yan takara.
A cewar rahoton, wani tsohon ma’aikacin kamfanin Glencore Plc a watan Yuli ya amince ya biya wani dillali $300,000 don samun kwangilar dakon mai daga NNPC, kafin daga bisani ya fahimci cewa an yi amfani da kukaden ta wata hanyar.
Shi kuwa Jonathan Zarembok, wanda ya bar ofishin kamfanin BP shiyyar Afrika a bara, a cikin karar, ya yi zargin cewa kudaden da suka ba NNPC an yi amfani da su ne wajen yakin neman zaben 2019.
Ya dai shigar da kamfanin na BP kara ne kan zargin cewa an kore shi daga aiki ne saboda ya yi magana a kan manyan kudaden da aka tura wa wasu dillalai domin samun kwangiloli a Najeriya.
Zarembok, a cikin shaidar da ya bayar a gaban kotu ya ce wasu sakonnin email da wani babban jami’in kamfanin BP ya aike da su zuwa Najeriya wata babbar ’yar manuniya ce kan badakalar.
“Sakonnin sun tattauna shirye-shiryen da ake yi na yakin neman zabe a 2018, mun san abin da hakan ke nufi,” inji shi.
Daga nan ne kuma kamfanin ya aike wa da wani dillali $900,000 bayan ya sami wasu kwangilolin daga NNPC.
Bloomberg ta kuma rawaito cewa makamantan wadannan bayanan sun bulla watanni biyu gabanin haka lokacin da Anthony Stimler, wanda ya bar Glencore a shekarar 2019 ya amsa zarge-zargen rashawa da almundahanar kudaden ake masa.
A baya dai Bloomberg ta rawaito cewa jami’ar da aka bayyana a cikin rahoton da sunan gwamnatin Najeriya ita ce Diezani Alison-Madueke, wacce ta kasance Ministar Mai ta Najeriya kuma wacce ta kula da harkokin NNPC tsakanin shekarar 2010 da 2015.
Sai dai jam’iyyarta ta yi rashin nasara a zaben 2015 a hannun jam’iyyar APC.
Babu kamshin gaskiya a rahoton – NNPC
To sai dai jabban jami’in NNPC mai kula da Sashen Hulda da Jama’a, Garbadeen Muhammad ya ce zarge-zargen ba gaskiya ba ne.
Shi kuwa da aka tuntube shi, Sakataren Yada Labaran jam’iyyar APC na kasa, Yekini Nabena cewa ya yi, “A yanzu dai rahoton soki-burutsu ne har sai sun fito da kwararan hujjoji.”
Sai dai yunkurin jin ta bakin PDP bai kai ga gaci ba sakamakon Sakatarenta na Yada Labarai, Kola Ologbondiyan bai amsa kiran wayarsa ko sakon kar-ta-kwana da na WhatsApp din da aka tura masa ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.