Masallacin Haramin Ka’aba da ke Makka
Fassarar Salihu Makera
Godiya ta tabbata ga Allah. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Annabi (SAW).
Bayan haka, ya ku Musulmi! Ku bi Allah Madaukaki da takawa ku sani bin Allah da takawa shi ne zai kare mu daga dukkan bala’o’i.
’Yan uwa a imani! Tun lokacin da Allah Ya halicci duniya ake fafata yaki a tsakanin sassa daban-daban domin a mallake zukata da tunanin mutane; kamar yadda ake neman mallakar dan Adam a jikinsa. A yau ana yakar dan Adam ta wajen tunani da fikirarsa fiye da kowane lokaci; ana yakar tunaninsa ta dukkan hanyoyi fiye da yaki irin na soji. Wannan yaki, shi ne yakin farfaganda.
Farfaganda wata muguwar hanya ce, kuma makami mafi hadari da ta fi ruguza dan Adam. Hadarinta babba ne kuma ba za a iya misalta barnarta ga dan Adam ba, saboda mugun illarta. Don haka wajibi ne a samu yunkuri daga Musulmi don nazartarta ta yadda za a gano tushenta a tuttuge ta, kafin ta jawo mummunar illar da ba za a iya magance ta ba ga dan Adam.
’Yan uwa a Musulunci! Idan dayanmu zai yi dubi da idon basira game da tarihin dan Adam, zai ga cewa farfaganda da jita-jita sun taka rawa tare da yin tasiri a dukkan zamunna; bilhasali ma sun samu gurbi babba wajen ci gaban masu da’awar wayewa irin na Turawan Yamma, kuma su suke jawo rudu da bala’o’i ga kasashe da dama. An bi dukkan matakan shigar da wannan muguwar dabi’a, domin juya akalar duniya kafin bayyanar Musulunci. Musulunci a matsayinsa na addinin da ginshikinsa shi ne tabbatar da rahama da adalci da zaman lafiya ga dan Adam, ya dauki kwararan matakai domin yaki da wannan muguwar dabi’a, ta hanyar bin matakan haramta ta a cikin Alkur’ani da Sunnah. Musulunci ya haramta ta ce, ta hanyar haramta furta kowace kalma da za ta kawo rashin jin dadi ko rigima a tsakanin mutane. Musulunci ya haramta zunde da karya da rada da kage da annamimanci da yada jita-jita, kuma ya yi tattalin azaba ga wadanda suke yada karya tare da alkawarin azaba mai radadi a Lahira. Sai Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai ne wadanda suke son alfasha ta watsu ga wadanda suka yi imani, suna da azaba mai radadi a cikin duniya da Lahira.” (K: 24: 19).
Kuma Alku’ani Mai girma ya yi umarni a rika bincike kan labari: “Ya ku wadanda suka yi imani! Idan fasiki ya zo muku da labari, to, ku nemi bayani (ku bincika), domin kada ku cuci wadansu mutane a cikin jahilci, saboda haka ku wayi gari a kan abin da kuka aikata kuna masu nadama.” (K: 49: 6). Har wa yau Allah Madaukaki Ya jawo hankalin dan Adam cewa zai hadu da sakamakon duk wata kalma da ya furta. Sai Allah Ya ce, “Kuma (mutum) ba ya lafazi da wata magana face a like da shi akwai mai tsaro halartcce.” (K: 50: 18).
A gaskiya farfaganda da jita-jita su ne manyan abubuwan da suka jawo duniya take mummunan zato ga Musulmi, kuma Allah Ya haramta hakan a cikin fadinSa: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku nisanci abu mai yawa na zato. Lallai sashin zato laifi ne.” (K: 49: 12). Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ya ishi mutum zama makaryaci ya bayar da labarin duk abin da ya ji.” Kuma domin Musulunci ya toshe hanya ga masu yada jita-jita da masu kulla makirci, sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ko in ba ku labarin mafi sharrin mutane a cikinku? Sai sahabbansa suka ce, “Eh, ka ba mu Ya Manzon Allah!” Sai ya ce “Su ne annamimai masu hada gaba a tsakanin masoya.”
Ya ’yan uwa Musulmi! Jita-jita da farfaganda, sun haifar da bala’o’i ga al’ummu da dama; sun wargaza gidaje, sun ruguza dauloli da kasashe tare da jawo yake-yake. Masu yada su miyagu ne, masu miyagun manufofi, kuma gaba daya ba su da dabi’a ta mutanen kirki. Ba su girmama gaskiya, sun dauki karya ta zame musu abar ado. Burinsu su jawo rashin zaman lafiya a kasa, kuma mutane da dama suna rasa rayukansu saboda miyagun ayyukansu.
Tarihi cike yake da misalan farfaganda iri-iri da karairayi domin a dakile gaskiya daga isa ga mutane. A zamanin Manzon Allah (SAW), mushirikai sun yi iyakar kokarinsu don dakile yaduwar Musulunci ko hallaka Annabi (SAW) ba tare da sun samu nasara ba. Sun jefe shi da miyagun maganganu domin su hana mutane sauraren sakonsa. Sun kaddamar da yakin tunani don karya shi tare da sahabbansa, amma duk a banza.
Daya daga cikin rukunin mutanen da suka kaddamar da yakin farfagandar su ne Yahudawa, wadanda sanannu ne wajen yi wa Mahalicci tawaye da kashe Annabawan Allah da aka aika musu. Sun yi wa Annabi Isa da mahaifiyarsa (AS) mafi munin kazafi, kuma sun yi wa Annabi (SAW) mugun kulli a Madina ta hanyar kirkirar karya.
Yahudawa sun hada kai da munafukai suka kirkiri karya suka jefe Uwar Muminai A’isha (Allah Ya yarda da ita), cewa ta yi zina domin su ci zarafi da zubar da girman Annabi (SAW), ta yadda za su kawo cikas ga yaduwar sakonsa. Kan haka ne Allah Ya yi gargadi na tsoratarwa ga Musulmin da ba da niyya ba suka rudu da wannan farfaganda, inda Ya ce: “Kuma don me a lokacin da kuka ji shi, (kazafin) ba ku ce ba, “Ba ya yiwuwa a gare mu, mu yi magana a game da wannan. Tsarki ya tabbata a gare Ka (Allah). Wannan kiren karya ne mai girma?” Allah Yana yi muku gargadi kada ku koma ga irinsa, har abada idan kun kasance muminai.” (K: 24: 16-17).
’Yan uwa a Musulunci! Yakin farfaganda a yanzu yana cin kasuwarsa yadda ya so, saboda kayayyakin sadarwa na zamani da na’urori masu saurin kai sako ga mutane da makiya suke amfani da su domin su addabi mutane ta yakar tunani da zukatansu tare da raunana kyawawan halaye ta hannun miyagun cibiyoyinsu. Farfaganda da yada jita-jita, miyagun abubuwa ne na cutar da addini da al’umma da kuma kyawawan dabi’u. Hakika babban abin bakin ciki ne ganin yadda dubban mutane suke gaskata ire-iren wannan jita-jita da farfaganda. Ya kamata Musulmin da suka samu kansu a irin wannan haramtacciyar dabi’a, su tuna cewa suna iya rasa imaninsu idan ba su daina ba. Shin ya dace mu Musulmi mu yi watsi da ginshikan addininmu, kuma mu rika mugun zato ga malamanmu da sauran ’yan uwanmu, saboda jita-jitar da muka ji game da su?
Akwai bukatar malamai da dalibansu a duniyar Musulmi su tashi haikan su yaki wannan muguwar dabi’a. Ya kamata su fahimci cewa su ne ake nufi da wannan yaki. Don haka wajibi ne su yi riko da Littafin Allah da Sunnar Manzon Allah (SAW) kamar yadda magabatansu suka yi a zamaninsu. Masallatai da makarantu da gidaje da kafafon watsa labarai na Musulmi suna da bababar gudunmawa da za su bayar wajen yakar farfaganda da jita-jita. Don haka akwai bukatar a kara kokari bisa kyakkyawar niyya domin a cimma nasarar da ta dace.
’Yan uwa a Musulunci! Addininmu ya tsara ka’idojin bi wajen yaki da jita-jita da farfaganda, babba daga cikinsu shi ne jin tsoron Allah da tantance gaskiyar labari kafin amincewa da shi. Sannan ya umarce mu da yin adalci a cikin kowane al’amari.
’Yan uwa a cikin imani! Ba za mu kammala wannan huduba ba, face mun la’anci yakin farfaganda da cin zarafi da kafafen watsa labarai na Turai da ’yan korensu suka kaddamar a kan Musulunci da Musulmi. Akwai bukatar mu hada hannu, mu yaki wannan farfaganda, mu zage dantse mu nuna wa makiyanmu ba za mu taba sassauci a kan ginshikan addinimu ko kyawawan dabi’unmu ba. Kuma wajibi ne mu yi riko da koyarwar addininmu a dukkan bangarorin rayuwa, kuma mu ba malamanmu da shugabanninmu na Musulunci cikakkiyar dama ta magance duk wata matsala da ta taso.
Allah Ya yi mana gafara ni da ku.