✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin kasa ya kashe sojan Najeriya

Jirgin kasa ya kashe soja a daidai wurin da jirgin kasa ya kashe mutum 6, ya jikkata wasu 80 a cikin motar ma'aikata a Legas

Wani soja ya gamu da ajalinsa a yayin da jirgin kasa ya kade shi a yankin PWD da ke Ikeja a Jihar Legas.

Jirgin kasan ya kashe sojan ne a daidai wurin da wani jirgin kasa jirgin kasa ya kashe mutum shida, ya kuma jikkata wasu 80 a cikin motar jigilar ma’aikatan Gwamnatin Jihar Legas a kwanakin baya.

Shaidu sun ce, sojan mai mukamin Sajan, ya gamu da ajalinsa ne a bayan ya yi kokarin tsallake titin jirgin kasa a kan babur dinsa, amma aka yi rashin sa’a, jirgin, wadan ya taso daga Ibadan zuwa Legas ya kade shi.

Lamarin na ranar Laraba ya faru ne wata uku daidai, bayan jirgin kasa ya kade motar ma’aikatan gwamnatin jihar Legas, a ranar 9 ga Maris, 2023.

Wata majiya ta ce an sanar da Birged na 9 na Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, inda sojan yake aiki, kuma sun dauke gawar mamacin zuwa Asibitin Sojoji da ke Yaba a jihar.

Wakilinmu ya yi kokarin yin magana da kakakin Babbar Rundunar Soji ta 81 da ke kula da jihohin Legas da Ogun, Laftanar-Kanar Olabisi Olalekan Ayeni, a kan lamarin, amma jami’in bai amsa kiran waba.