’Yan bindiga sun kwashi kashinsu a hannun jami’an tsaro a kan Babbar Hanyar Kaduna zuwa Abuja, a lokacin da bata-garin suka yi yunkurin yin garkuwa da mutane.
Jami’an tsaron hadin gwiwar sun ragargaji ’yan bindigar tare da kashe daya daga cikinsu ne a musayar wuta da suka yi a lokacin da jami’an tsaron suka kai dauki bayan ’yan bindigar sun kai wani hari a ranar Lahadi.
- 2023: Bayan shekara 23 a Majalisa, Ahmad Lawan ya yi biyu babu
- Rasha ta ci ribar Yuro Biliyan 98 a kwanaki 100 na yakinta da Ukraine
Kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige ya ce, “Jami’an tsaron sun yi nasarar kwato bindiga kirar AK47 da harsasai da kuma babur din ’yan bindigar.”
Ya ce ganin irin ragargazar da jami’an tsaron suka yi musu, sai ’yan bindigar suka ranta a na kare zuwa cikin daji.
“Sojoji da jami’an tsaron rundunar hadin gwiwar kuma na ci gaba kokarin tabbatar da kariya da aminci ga matafiya da sauran masu amfani da hanyar,” in ji shi.
Ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Yekini Ayoku, ya yaba wa jami’an tsaron bisa wannan namijin kokari, tare da ba su tabbacin cewa ba za a taba mantawa da abin da suka yi ba.