✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda Isra’ila ke ragargazar Fadasdinawa a Gaza

Isra’ila ta yi wa Falasdinawa lugude da jiragen sama da tankokin yaki da bindigogin atilare a safiyar Juma’a.

Isra’ila ta yi wa Falasdinawan Zirin Gaza luguden wuta da jiragen sama 160 da tankokin yaki da bindigogin atilare da sanyin asubahin Juma’a.

Rundunar Tsaron Isra’ila (IDF) ta ce ta kai hare-haren ne da zummar tarwatsa hanyoyin karkashin kasa na Falasdinawa domin kassara hare-haren rokoki a kan garuruwan Yahudawa.

A cikin mintina 40, kafin wayeware gari, Isra’ila ta kashe Falasdinawa akalla 13, ciki har da wata uwa da ’ya’yanta uku da aka ciro gawarwakinsu daga baraguzan gidansu, inji jami’an kiwon lafiya a Gaza.

Kakakin sojan Isra’ila, Laftanar Kanar Jonathan Conricus ya ce Isra’ila ta Isra’ila ta lalata ramukan karkashin kasa masu nisan kilomita da dama da mayakan Falasdinawa suka yi amfani da su.

Falasdinawa sun mayar da martani da luguden rokoki a kan Kudancin Isra’ila cikin hanzari a kwana na biyar na fada mafi muni tsakanin Isra’ila da mayakan Gaza tun daga 2014.

Wani jami’in sojan Isra’ila ya ce an harba rokoki sama da 2,000 daga Gaza zuwa cikin Isra’ila tun lokacin da aka fara rikicin.

Kasar Masar ce ke jagorantar kokarin kasa da kasa don ganin an tsagaita wuta tare da tabbatar da cewa rikicin bai yadu ba.

Majiyoyin tsaro sun ce kawo yanzu babu wani bangare da ya nuna yarda amma wani jami’in Falasdinawa ya ce tattaunawar ta kankama a ranar Juma’a.

Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a tsagaita wuta nan take.

“Yakin yana iya kawo rashin tsaro da matsalar jin kai da kuma karfafa tsattsauran ra’ayi,” inji kakakin Majalisar, Stephane Dujarric.

Shi ma yayin ganawa ta tarho da Fira Ministan Isra’ia, Benjamin Netanyahu, Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci bangarorin su koma kan teburin sulhu.

Hamas, kungiyar Islama da ke mulkin Gaza, ta kaddamar da hare-haren rokokin ne a ranar Litinin, a matsayin ramuwar gayya ga arangamar da ’yan sandan Isra’ila suka yi da Falasdinawa a kusa da Masallacin Kudus, wuri na uku mafi tsarki a Musulunci.

Tashin hankali ya bazu zuwa biranen da Yahudawa da Larabawan Isra’ila tsiraru ke zaune kusa da juna.

Kazalika an yi arangama tsakanin Falasdinawa masu zanga-zangar da jami’an tsaron Isra’ila a yankin Yammacin Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye, inda jami’an kiwon lafiya suka ce Falasdinawa 10 aka kashe a ranar Juma’a.