Bisa dukkan alamu za a yi dauki ba dadi kan kujerar Sanatan Abia ta Kudu a Zaben 2023 tsakanin gwamnan jihar, Okezie Ikpeazu na Jam’iyyar PDP da Sanata mai ci, Eyinnaya Abaribe na APGA.
Tun a matakin yakin neman zabe, kafin a je akwatin zabe masu lura da harkokin siyasar jihar na hasashen kusan kunnen doki ’yan takarar za su yi a zaben da ke tafe.
- Mai hada wa ’yan ta’addan Katsina maganin bindiga ya shiga hannu
- Abba Gida-gida ya yi barazanar kauwara ce wa yarjejeniyar zaman lafiya a Kano
Abaribe: Zango 4 a Majalisa
Abaribe sanannen dan Majalisar Dattawa ne da ya shekara 16 a jere yana wakiltar Abia ta Kudu.
Kafin sauya shekarsa daga PDP zuwa APGA, ya kasance Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar, inda a matsayinsa na jagoran ’yan adawa a majalisar ya rika caccakar Gwamnatin Jam’iyyar APC — har ya taba neman Shugaba Buhari ya yi murabus kan karuwar matsalar tsaro a Najeriya.
Caccakar da yake wa gwamnati da tsayawarsa kai da fata kan wasu abubuwan da suka shafi kasa sun kara masa farin jini a wurin jama’ar Abia ta Kudu da uwar Jam’iyyar PDP da ta jihar da ma yankin Kudu maso Gabas baki daya.
Farin jininsa a yankin ya kara karuwa bayan ya yi ta kiraye-kirayen neman a saki Shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, wanda gwamnati ke tsare da shi — sannan ya tsaya a matsayin mai karbar belinsa.
A wani taron kaddamar da littafin tarihin Abaribe mai suna ‘Made in Aba’ da aka gudanar a Abuja, Ikpeazu ya yaba wa kyakkyawan wakilcina ga Mazabar Abia ta Kudu da ma daukacin yankin Kudu maso Gabas.
Yadda suka yi baram-baram
Ba a jima ba, aka yi hannun riga tsakanin Eyinnaya Abaribe da abokinsa Gwamna Ikpeazu a PDP, bayan Sanatan ya gaza samun tikitin takarar gwamnan jihar a jam’iyyar.
Zaben dan takarar gwamnan da jam’iyyar ta yi ya bar baya da kura, inda wasu jiga-jiganta suka zargi gwamnan da yin dauki-doran dan takara.
Abaribe da sauran ’yan takarar da suka janye daga zaben na ranar 25 ga Mayu, wanda Farfesa Uche Ikonne ya lashe, asun bayyana abin da aka yi a matsayin dodo-rido — inda “aka yi amfani da wani kwamitin je-ka-na-yi-ka mai mutum uku, a maimakon daleget din da doka ta tsara.”
Daga baya Abaribe ya bar PDP ya koma APGA, kan abin da ya kira, “rashin ta-ido wajen yi wa doka da tsarin dimokuradiyya hawan kawara, bayan tattarawa jama’ar mazabata.”
Sai dai kuma, tun kafin zuwan APGA, jam’iyyar ta riga ta cika, ta tumbatsa da manyan masu neman takarar gwamna, kuma bisa dukkan alamu ba zai kai labari ba, don haka ya yanke shawarar neman komawa kujerarsa ta Sanata.
Za a yi karon batta
A PDP kuma Ikpeazu, wanda wa’adinsa na biyu a matsayin gwamna ke karewa a 2023, na neman kujerar ta Sanatan Abia ta Kudu — domin kara wa mazabarmu kusanci da Gwamnatin Tarayya, a cewarsa.
“A matsayin gwamna ba komai ne ko kowa ne ya iya biya wa bukata ba
“Ina bukatar goyon bayanku domin in je jin wakilce su a Majalisar Dattawa, in jawo Gwamnatin Tarayya zuwa zuwa ga jama’ar jiharmu da kuma mazabata.
“Daga cikin matsalolin da na yi fama da su a matsayin gwamna akwai rashi mutanen da za su jawo Gwamnatin Tarayya zuwa Jihar Abia” in ji shi.
Ikpeazu da Abaribe a kan sikeli
Farin jinin Ikpeazu
Gwamna Ikpeazu ya samu da farin jini a wurin ’yan kabilarsa ta Ngwa, bayan ya ba su mukaman siyasa da kuma shirinsa na koya wa matasa sana’ar hada takalma, wanda magoya bayansa suka yi amanna ya samu gagarumar nasara.
Yana kuma bugun kirji da nasarorin da gwamnatinsa ta samu, za su sa jama’ar Abia ta Kudu su zabe shi domin kashi 70 cikin 100 na ayyukan raya kasa na gwamnatinsa a jihar, ta yi su ne a mazabar.
Kazalika ayyukan da shirin ofishin matarsa a mazabar aka yi su; ciki kuwa har da gina gidajen ga masu karamin karfi da biyan kudin maganin mata da kananan yara.
Sannan jam’iyyarsa ta PDP ke da rinjaye a jihar, inda a zaben 2019 ta lashe biyu daga cikin kujerun sanata uku da ke jihar.
Masu sharhi na hasashen baya ga farin jinin PDP da zai taimaka wa Ikpeazu, a matsayinsa na gwamna mai ci, zai iya amfani da karfin ikonsa wajen ganin ya cim-ma burkina na zama Sanatan a 2023.
Abaribe na neman tazarce
A yayin da Sanata Eyinnaya Abaribe ke nema komawa kujerarsa, yana da kwarin gwiwar dadewarsa a majalisa da kuma farin jininsa wurin jama’a za su kara masa damar cin zabe.
Al’ummar Ibo, musamman matasa na tune da rawar da ya taka wajen ganin a saki Nnamdi Kanu, wanda suke ganin babu wanda ya taba yin hakan.
Sannan mutum ne mai yawan babatu a majalisa kan duk abin da yake ganin zalunci ne ko wariya ne ga al’ummar Ibo, wanda wasu ke ganin rashin irinsa a Majalisar na iya sa mazabar ta rasa wakilci na gari da take bukata.
Sai dai kuma sauya shekarsa zuwa APGA, mai fama da rikicin shugabanci da raguwar farin jini na iya hana cikar burkina na yin tazarce.
Rikicin shugabanci APGA a matakin Jihar Abia ya sa wasu kusoshinta ficewa, yawancinsu suka koma Jam’iyyar LP.
Dan takarar gwamnan Jam’iyyar LP a jihar na daga cikin tsoffin jiga-jigan APGA da suka sauya sheka saboda rashin gamsuwa da hukuncin kotu kan rikicin cikin gidan APGA a jihar.
Sannan a halin yanzu guguwar Peter Obi — dan takarar shugaban kasa na LP — na tafiya da abin da ya rage na farin jinin APGA a Jihar Abia.
Masu bibiyar harkokin siyasar jihar na hasashen jam’iyyun PDP da LP ne manyan jam’iyyun da za su fata a zaben Majalisar Dokoki ta Tarayya a jihar a 2023.
Zakaran gwajin dafi
Ana ganin zaben 2023 zakaran gwajin dafi ne tsakanin Sanata Abaribe da ya yi zango hudu a jere (shekara 16) a kan kujerar da kuma Gwamna Ikpeazu da ke ganin jama’ar mazabar sun fi son shi.
Wani jigo a PDP a jihar, Dokta Sampson Orji, ya shawarci Ikpeazu ya hakura, domin ba zai iya kayar da sanatan mai ci ba.
Dokta Sampson Orji, wanda a ya nemi takarar gwamna a zaben dan akarar da PDP ta yi na arnar 25 ga watan Mayu, a halin yanzu suna kotu, inda yake kalubalantar jam’iyyar da kuma takarar Farfesa Uche Ikonne.
A cewarsa, idan aka ba shi zabi tsakanin Gwamnan Ikpeazu da Sanata Abaribe, “Abaribe zan zaba,” domin kamar ni zabi ne tsakanin kwararre ne da kuma dan koyo.”
A gefe guda kuma, Sakatare-Janar na Kungiyar Al’ummar Ibo ta Ohanaeze Ndigbo, Okechukwu Isiguzoro, ya ce kungiyar na bayan Ikpeazu saboda ya “nuna jarumta wajen kwato ’yancin ’yan kabilar da kuma yakar wariyar da ake nuna wa yankin Kudu maso Gabas, hadi da kokarinsa na hada kan ’yan kabilar a yankin Neja Delta.
“Bayan nazarin abin da ke wakana a yankin Abia ta Kudu, kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta Duniya, na kira ga Sanata Enyinnaya Abaribe ya janye saboda gazawarsa wajen yin abin da al’ummarsa ke so.
“A matsayinsa na wanda ya fi karancin gabatar da kudurori a cikin sanatoci 15 na Kudu maso Gabas, gazawar wakilcinsa ga al’ummar Ibo musamman matasa a bayyane take, don haka akwai bukatar sabon jini mai kwarewa da iya siyasa da zai kawo ayyukan cigaba,” in ji sanarwar kungiyar.
Don haka ya ce kungiyar tana bukatar samun sabon wakilci a 2023 ba ’yan amshin shata ba.
“Al’ummar Ibo na kira ga Abaribe ya janye a zaben Sanatan Abia ta Kudu a 2023 domin samun wani mukamin Gwamnatin Tarayya nan gaba, ya bar wa Ikpeazu wanda ya nuna jarumta wajen kare manufofin al’ummar Ibo da kawo karshen wariyar da ake nuna wa yankin Kudu maso Gabas da kuma hada kan masu amfani da harshen Ibo a yankin Neja Delta da dangoginsu.
“Abaribe ya yi bakin kokarinsa a tsawon shekara 16 (zuwa 2023) a Majalisar Dattawa, amma kujerar ba ta gado ba ce, amma duk da haka ana fata ya koma wani matasyin a 2023.
“Al’ummarsa na kukan karancin ayyukan ci gaban mazabar da rashin samun ganin sa a shekara 16 da ya yi a Majalisa,” in ji sanarwar.
Daga Sagir Kano Saleh, Abdullateef Dalai (Abuja) & Linus Effiong (Umuahia)