Wata Babbar Kotu da ke zamanta a Abuja, ta bai wa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), umarnin karbe Naira miliyan 120 daga hannun wata malamar makarantar firamare, Roseline Egbuha, da abokan aikinta da aka samu a asusun ajiyarta na banki.
Kudaden da aka kwace, da kuma motoci sun kai Naira miliyan 540 da aka gano a wajen matar, wadda malama ce a makarantar firamare ta Ozala da ke Abagana a Jihar Anambra.
- Za mu binciki malamin da ya daki dalibarsa da gora —Gwamnatin Kaduna
- Zargin almundahana: Kotu ta ba da belin tsohon Akanta-Janar Ahmed Idris
Malamar da ke karbar albashin N76,000 duk wata a lokacin da ICPC ta kama ta a 2020, ta boye Naira miliyan 540 a asusun ajiyarta na bankin Guaranty Trust.
Wani bincike da ICPC ta gudanar ya nuna cewa, tana da hannu a almundahanar kudade wanda hakan ya sa hukumar ta sanya wa asusun nata takunkumin hana cire kudi.
Sai dai kuma, an cire takunkumin da aka sanya wa asusun na Egbuha da abokan hularta bayan wani umarnin da wata Babbar Kotu da ke Abuja ta bayar, inda nan take kudaden aka raba su sannan aka tura wasu asusun banki mallakar wasu masu gudanar da harkar canjin kudi.
Lauyan ICPC, Adesina Raheem, a cikin bukatar da ya shigar a 2021 a gaban Mai Shari’a D. U. Okorowo, ya yi zargin cewa an yi amfani da haramtattun kudin wajen gudanar da ayyukan da ba su dace ba, bayan an raba su zuwa gida shida sannan aka tura wa mutane daban-daban.
Sauran abubuwan da aka kwace sun hada da motoci kirar Toyota Lexus da Venza.