A ranar Lahadin da ta gabata ce wani magidanci mai suna Alhaji Lauwali Zugana Matawallen Salame, ya samu kansa a cikin damuwa da bakin ciki, bayan da hadari da Keke NAPEP ya ci rayukan matarsa da surukarsa da ’ya’yansa hudu.
Babur mai taya uku da ake kira Keke NAPEP ko A Daidaita Sahu ya kama da wuta ne ya kone iyalan nasa inda aka kai su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman Dan Fodiyo inda a can suka cika.
Alhaji Lauwali Zugana ya shaida wa Aminiya cewa “Ina shagona zan yi ci abinci da rana sai aka kira ni a waya aka fada min cewa matata Hajiya Hadiza mai shekara 42 da surukuwata Malama Murja mai shekara 52 da ’ya’yana hudu, mace daya da maza uku sun yi hadari kan babur mai kafa uku a hanyar Gabacin Sakkwato, inda ban yi wata-wata ba na tafi wurin.”
Matawallen Silamen ya ce “Da na isa wajen na samu lamarin ya baci hankalina ya tashi na shiga damuwa da kaduwa irin yadda na ga Ummu Sulaim ‘yar shekara daya da rabi da Abubakar Sadik da Usman da Yahaya ‘yan shekara takwas da shida da biyu, sun kone kurumus ba abin da ake iya yi musu sai dai akwashi tokar kasusuwansu kai ka ce ba mutane ba ne suka kone. A gefe daya matata da suraukuwata da wani mai babur da ya jawo hadarin din jikinsu ko’ina ya kone, amma suna da ransu. Haka muka dauke su muka tafi da su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman Dan Fodiyo, tun da muka kai su aka hana kowa zuwa wurinsu sai ni kaDai, an rika ba su magani da kulawa, na kashe fiye da Naira dubu 500 kafin shekaranjiya (ranar Asabar da ta gabat) su rasu bayan kwana shida da rasuwar yaran.”
Ya ce ya samu labarin yadda hadarin ya auku iyalinsa cewa sun shiga babur din ne daga unguwarsu a Gidan Igwai zuwa Kofar Aliyu Jodi Kwanni sai mai babur din ya bi hanyar zagaye da su saboda yana son ya sayi man fetur. Ya ce bayan ya sha mai suna tafiya sai ga wani mai babur dauke da jarkar man fetur a gabansa ya yi aron hannu, mai dauke da su bai gan shi ba suka yi arangama nan take wuta ta kama ta kone su tare da wanda yake dauke da man, amma shi matukin babur mai kafa ukun bai samu rauni sosai ba. “Lamarin da ya yi sanadiyar rasa rayukan mutum bakwai,” inji shi.
“Wannan kaddara ce ba abin da zan yi sai hakuri sun fito ne za su wajen bikin sunan dan da ’yata ta haifa, abinka da ajali a wuri daya sai surukuwata matar mahaifin matata da take gidana a yanzu ta zo nan suka tafi tare gaba daya ashe tare za su bar duniya. Hajiya da ’yar utarta sun tafi lokaci daya sun bar mu ni da ’ya’yanta cikin bakin cikin rashinsu da tunanin halayenta nagari har ta bar duniya ba ta taba saba mini ba. Tana da kirki fatana Allah Ya gafarta musu gaba daya amma mun yi rashi,” inji Lauwali Zugana.