✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda harin ’yan bindiga ya tilasta rufe sansanin sojoji a Neja

Sojojin sun janye ne daga yankin a wani mataki da Sakataren Gwamnatin Jihar ya kira da salon yaki.

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta rufe sansaninta dake yankin Zagzaga a Karamar Hukumar Munya ta jihar Neja bayan ’yan bindiga sun sake kai masa hari.

Ta kuma kaddamar da bincike tare da tallafin mazauna yankin da nufin nemo daya daga cikin sojojin da ya bace sakamakon harin da aka kai.

Matakin na zuwa ne bayan ’yan bindigar wadanda adadinsu ya kai kimanin 60 sun yi wa sansanin sojojin kawanya tare da yi wa sojojin ciki kofar rago sannan suka yi ta musayar wuta da su.

Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa an kashe da dama daga cikinsu, amma ko daya ba a ji wa rauni ba daga sojoji, in ban da wanda ya yi batan dabo.

Sojojin sun janye ne daga yankin a wani mataki da Sakataren Gwamnatin Jihar ya kira da salon yaki.

Sa’o’i kadan bayan janyewar sojojin daga yankin kuma, ’yan bindigar sun sake kaddamar da hari a yankin, kamar yadda wata majiya ta tabbatarwa da Aminiya.

Rahotanni dai sun ce an sace mutum 15 a wani hari da aka kai da daddare, lamarin da ya tilastawa mazauna yankunan yin kaura zuwa makwabtan kauyuka.

Garuruwan da sabbin hare-haren na ranar Laraba suka shafa sun hada da Zagzaga da Zhani da Guni da kuma Maraban Daudu, kuma tuni mazaunansu suka yi kaura inda matasa ne kawai yanzu suka rage a cikinsu.

Da aka tuntubi Sakataren Gwamnatin Jihar, ya ce tashin sansanin sojojin na wucin gadi ne saboda wasu kwararan dalilai, inda ya ce tun da farko an girke su ne a yankin kimanin shekaru biyar da suke shude saboda yanayin kalubalen dake tattare da shi.

%d bloggers like this: