Dakile masu kai kudaden fansar mutanen da aka sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya san ’yan bindigar yi wa fasinjojin da ke hannunsu bugun dawa.
Daga sace mutanen a ranar 28 ga watan Maris, an sako akalla mutum 20 daga cikin 60 da maharan suka yi garkuwa da su, bayan sun kashe wasu mutum tara a jirgin.
- Ba gudu ba ja da baya kan zanga-zangar bai daya a Najeriya —Ma’a’ikatan Jami’a
- Ku Shirya Wa Aukuwar Ambaliya —NIMET Ga ’Yan Najeriya
Wasu majiyoyi sun shaida mana cewa an sako wadanda suka kubuta ne bayan an biya kudin fansa miliyan N100, sauran mutum 40 kuma har yanzu suna hannun maharan.
Aminiya ta gano cewa yunkurin biyan karin kudin fansa don a sako karin mutanen ya samu tasgaro bayan jami’an tsaro sun hana masu kai kudaden da aka yi yarjejeniya.
Hakan ne ya fusata ’yan ta’addan inda a ranar Asabar suka fitar da wani bidiyo mai tsawon miti 11 suna yi wa mtuanen bugun dawa tare da barazanar kashe su.
A bidiyon, ’yan ta’addan sun kuma yi barazanar sace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Yemi Osinbajo da Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da sanatoci da sauran shugabannin siyasa.
A bidiyon an ji wani dan ta’addan na zargin gwamnati da yin karya game da kwamitin tattaunawa da kuma kokarin amfani da karfi waje kwato fasinjojin jirin.
Daya daga cikin fasinjojin da aka nuna a bidiyon, Mukhtar Shuaibu, ya tabbatar cewa masu garkusa da su sun fusata da yadda gwamnati ta hana a kai musu kudade.
“Ba mu san me muka yi wa gwamantin kasar nan ba, mu ’yan kaasar nan ne, amma kwananmu 120 a nan, gwamnati ta kasa kubutar da mu.
“Wane laifi muka yi mata? An shirya za a saki wasu daga cikinmu amma jami’an tasro sun hana ’yan uwanmu wucewa su je su karbe mu,” inji shi.
Dan uwan wani daga cikin fasinjojin ya ce masu garkuwar su sun fara tattaunawa da iyalansu kai tsaye, har sun amince su sako wani da ke fama da rashin lafiya.
Ya ce, “’Yan uwansa sun kusa kaiwa mahadar da aka yi alkawari, sai suka hadu da sojoji da suka hana su shiga dajin, har da barazanar tsare su,” tare da shaida musu cewa biyan kudin fansa babban laifi ne.
“Wannan ne ya sa ’yan ta’addan suka yi sabon bidiyon suna zane su a matsayin sako, har suna barazanar sace manyan jami’an gwamnati,” in ji shi.
Shi ma wani wanda dan uwansa ke hannun masu garkuwar ya ce: “Kwana 120 ke nan muna cikin tashin hankali ba tare da wani taimkako daga wurin gwamnati ba.
“Gwamnati ta ki ta ceto ’yan uwanmu, yanzu kuma tana dakile yukurin da mu muke yi, to yaya suke so mu yi?
“Sun ce mana mu shirya biyan kudi, amma ba su fito sun ce ga abin da za a ba su ba.
“Wasu sun sayar da gidajensu, wasu gonakinsu, wasu wuraren sana’arsu; mun shirya sayar da ranmu mu shiga daji ku karbo ’yan uwanmu amma ga abin da gwamnati ta yi.
“Yanzu gwamnati ta mayar da hannun agogo baya,” in ji shi.
Daga Sagir Kano Saleh, Muideen Olaniyi Idowu Isamotu (Abuja), Lami Sadiq, Mohammed I.Yaba (Kaduna)