✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda gwamnoni suka yi wa kananan hukumomi shakar mutuwa  

– Hukumar NFIU ta dauki aniyar ceto su Karamar hukuma na daya daga cikin rukunan gwamnatoci guda ukku da muke da su a Tarayyar Najeriya…

– Hukumar NFIU ta dauki aniyar ceto su

Karamar hukuma na daya daga cikin rukunan gwamnatoci guda ukku da muke da su a Tarayyar Najeriya wacce ta fi kowacce kusanci da talakan kasa kuma manufar da ta sa aka kirkiro da kananan hukumomi ita ce a kusanto da talaka zuwa ga gwamnati, domin samun ayyukan raya kasa cikin hanzari kamar kananan asibitoci da makarantun firamare da karamar sakandare da magudanan ruwa da kananan hanyoyi da harkar noma da samar da tsaftataccen ruwan sha da sauran al’amuran yau da kullum, wadanda talakan yake da bukatarsu a kusa da shi.

Amma a yanzu abun ya sauya salo domin kananan hukumomi sun koma hedkwatar talauci da samar da baragurbin matasa cikin al’umma, suna fama da cututtuka, rashin ruwan sha, tabarbarewar ilimi da rashin tsaro da sauran matsaloli masu tarin yawa.

Kamar yadda binciken Aminiya ya tabbatar, a shekarun baya, kananan hukumomi sun taka muhimmiyar rawa wajen inganta rayuwar al’umma ta hanyar gudanar da ayyuka da suka kawo ci gaba, sabanin abin da ke faruwa a yanzu inda gwamnoni suka samu damar hada asusun ajiya da kananan hukumomi.

A yanzu haka kananan hukumomi baya ga biyan albashin ma’aikata ba su iya aiwatar da wasu ayyuka kamar gyaran makarantu, yin kwalbati ko gyaran kasuwanni da ke yankunansu.

Sai dai ga alama, an sanya danba wajen ceto kananan hukumomin kasar nan daga mallakar gwamnonin jihohi, musamman ganin matakin da Hukumar Sa Ido Kan Hada-Hadar Kudade ta Kasa (NFIU) ta dauka na ganin cewa daga watan Yunin bana, sun fara samun dauninsu na kudade daga Gwamnatin Tarayya, kai tsaye. Kodayake Kungiyar Gwamnoni ta shigar da korafi ga Gwamnatin Tarayya, domin ganin ta dakile wannan kuduri.

A nata bangaren, Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi  (NULGE) ta bakin shugabanta Kwamared Khalil Ibrahim, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta yi watai ta takardar kungiyar gwamnonin ta shigar.

NULGE ta ce tun shekarar 2003 gwamnonin kasar nan suka sanya lalitar kananan hukumomi cikin aljihunsu.

Aminiya ta gano cewa matsanancin halin da kananan hukumomi ke ciki a yanzu a kasar nan ya sa suka rasa martabarsu a gwamnatance. Wannan ya sa Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Kasa (NULGE) da sauran kungiyoyin ma’aikata suka matsa da cewa ya kamata a maida musu da ’yancin cin gashin kansu kamar yadda suke a shekarun baya.

Hakan ya sa wasu masu fashin baki ke ganin matakin zai kawo ci gaba a gwamnatance, wasu kuma na ganin cewa ko an ci gaba da ba su kudadensu kai tsaye daga Gwamnatin Tarayya, hakan ba zai canza komai ba muddin gwamnoni za su ci gaba da yin katsalandan wajen zaben shugabanin kananan hukumomi a jihohinsu.

Tsohon Kansila a Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, Alhaji Zubairu Sham’una, ya bayyana cewa ko an ba da cin gashin kai ga kananan hukumomi babu abin da zai canza sai har idan an mayar da zaben shugabannin kananan hukumomi da kansiloli zuwa ga hannun hukumar zabe ta kasa watau INEC.

“Ko da can gwamnoni ba sa iya taba kudin karamar hukuma ba tare da shugaban karamar hukumar ya saka hannu ba. Kuma ba shi da zabi sai ya saka hannun tun da dama can gwamna ne ya kawo shi ya dora wa mutane.

“Saboda haka muddin zaben kananan hukumomi zai ci gaba da zama hannun jihohi to kananan hukumomi ba za su taba samun ’yanci ba, domin sai yadda aka yi da su,” inji shi.

Shi kuma wani ma’aikacin karamar hukuma a Jihar Kaduna mai suna Nura ya ce: “Za a samu ci gaba a cikin al’aumma idan kananan hukumomi suna karbar kudadensu kai tsaye daga Gwamnatin Tarayya, domin a yanzu kusan duk lokacin da aka ce an turo kudin karamar hukuma sai ka ga shugabanta da daraktoci suna ta shiga da fita a Ma’aikatar Kananan Hukumomi domin ganin yadda za a yi a sakar musu wani abu,”

Shi ma wani Ma’aikacin Hukumar Shari’a a Jihar Kaduna, Usman Garba, yana cewa: “Kananan hukumomi sun fi kusa da jama’a a kan gwamnatin jiha. Don haka kamata ya yi a rika ba su kudadensu domin jama’a su gane wane shugaban karamar hukuma ke aiki da wanda ba ya aiki. “A yanzu kusan duk ayyukan da gwamnoni ke yi idan ka duba sai ka ga aikin da ya kamata a ce shugaban karamar hukuma ke yi ne. Amma duk gwamnanoni sun karbe aikin daga a hannunsu, wanda kuma hakan ba alheri ba ne ga jama’ar da suka zabe su,” inji shi.

Kwamared Abdullahi Muhammad Gwarzo shi ne Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumoni ta Najeriya (NULGE) a Jihar Kano. Ya bayyana wa Aminiya cewa: “Ni a ganina kusan duk daya ne da yadda kananan hukumomi suke a jiya da kuma yau, illa dan bambanci kadan. A da kananan hukumomi suna da dan tsari na cin gashin kansu kadan, inda ake ba su kudi sai dai za a ba su umarnin abin da za su yi da kudin, sabanin yanzu ba a ba su kudin sai sun roka kuma a wannan tsarin ba lallai ne shugaban karamar hukuma ya sami abin da ya nema ba.”

Ya dora alhakin wadannan matsaloli a kan Kundin Tsarin Mulkin Kasa, wanda shi ya fito da batun samar da asusun hadaka tsakanin kananan hukumomi da gwamnatin jiha.

“Idan aka dauki sadara ta bakwai a Kundin Tsarin Mulkin Kasa, ya ba Majalisar Dokokin Jihohi damar yin dokokin da suka shafi kananan hukumominsu. Wannan shi ya kawo kowacce jiha tana da tsarin yadda ake tafiyar da kananan hukumominta daban da na ’yar uwarta. Duk da cewa karamar hukuma ita ma gwamanti ce mai zaman kanta amma wannan tsari da aka fito da shi ya dabaibaye ta. An wayi gari ana gudanar da kananan hukumomi kamar wani abun mallaka da ke karkashin gwamnatin jiha,” inji shi.

“A shekarar 1992 an taba ba kananan  hukumomin damar  cin gashin kansu. A lokacin shugaban karamar hukuma yana da damar samun kudinsa kai tsaye duk da cewa ana kula da su domin ba su isa su kashe kudin ba bisa ka’ida ba. A yanzu idan har suka sami damar cin gashin kansu za a rage talauci, domin karamar hukuma za ta yi nata aikin a matakinta. Misali, a bangaren taimaka wa al’umma abin da ya shafi lafiyarsu ko iliminsu da sauransu.”

Shugaban NULGE ta Jihar Sakkwato Kwamared Shehu Haliru Shuni ya ce ya goyin bayan Hukumar Kula da Hada-Hadar Kudi ta Kasa (NFIU) dangane da matakin da ta dauka na tura wa kananan hukumomi kudadensu kai tsaye. “Wannan abu ne da muka yi ta fafutika kansa shekaru da suka wuce, yanzu an samu nasara muna fatan a yi amfani da kudaden kamar yadda doka ta nuna,” a cewarsa.

Ya bayyana irin rawar da kungiyarsu za ta taka. “Duk wani tsari da ka sani kungiya ta yi yana nan. Kowace jiha tana da yadda take tafiyar da mulkinta, mu a nan Sakkwato gwamnanmu ya san doka; ba zai yi abin da ya saba wa doka ba, yadda doka ta ce a yi haka zai yi.

“Abin da nake son shugabannin kananan hukumomi su fara yi, su dubi matsalar albashi. Maganar gaskiya ma’aikatan kananan hukumomi suna da matsalar albashi, a zo a zauna tsakanin kungiya da gwamnati a yi adalci a fito da ma’aikatan gaskiya a rika biyan su yadda ya kamata,” inji Kwamared Shuni.

Baba Sani, daya ne daga cikin shugabanin kungiyar NULGE a Jihar Gombe. Ya ce a shekarun baya akwai ci gaba sosai a kananan hukumomi, lokacin da gwamnoni ba sU tsoma musu baki. “Sai dai saboda lalacewar lamari, yanzu a kokarin da suke yi na a ba su ’yancin kansu, idan aka ba su ba za su iya gudanar da wasu abubuwa ba saboda yanzu komai ya canja; Kansu kawai za su yi ta ginawa.”

Ya kara da cewa a shekarun baya shugabanin kananan hukumomi suna iya ba da kwangilar gine-gine da yin kwalbatoci da kananan asibitoci da gadoji da sauran su amma yanzu ba su iyawa.

Shi ma wani ma’aikacin karamar hukuma a jihar ta Gombe mai suna Musa Muhammad,  cewa ya yi da ne kananan hukumomi suka amsa sunansu, lokacin da shugabanni suke da karfin ikon gudanar da komai, su ke ba da kwangila ba yanzu da suka zama ’yan amshin shata ba.

“Yanzu kananan hukumomi sun mutu, sun zama ’yaran gwamnoni ko an ba su ’yancin kai yanzu kafin su farfado sai an gyara tsarin yin zabe, ya zama kowa zai iya tsayawa takara idan ya cancanta a zabe shi ba sai wanda yake jam’iyya daya da gwamna ba,” inji shi.

A cewarsa, muddin gwamnoni suna sa baki wajen zaben kananan hukumomi, ko an ba da ’yancin ba za a gani a kasa ba, za a zo ana cewa gara jiya da yau.

A Jihar Katsina kuwa, tun bayan rushe shugabannin kananan hukumomi 34 na jam’iyyar PDP da Gwamnatin Masari ta APC ta yi, bayan darewarsa bisa mulkin jihar, har zuwa yanzu ba a yi wani sabon zaben kananan hukumomi a jihar ba.

Wani tsohon Kansila mai suna Nuhu Aiwa Inwala daga Karamar Hukumar Katsina, ya nuna takaicinsa a kan irin yadda kananan hukumomin suke ciki a yanzu. “Kasancewar masu riko ne a yanzu ba zababbu ba, ba su da kudaden da suke shigo masu kai tsaye kuma ba za su iya yin manyan ayyuka ba saboda haka dole ake ganin koma baya a kananan hukumomi.

“Duk wani abin da za su yi sai dai su je ma’aikatar kula da kananan hukumomi suna neman alfarma a yi musu, ko su roki Gwamna ya sa a yi abin kai tsaye,” inji tsohon Kansilan.

Shi kuwa Shugaban riko na kungiyar NULGE da ke Katsina, Malam Hamza

Bala ya ce kimanin shekaru biyar da suka wuce, kananan hukumomi suna cikin matsalar kudi. Ba su da damar taba kudinsu kai tsaye da ake ba su.

Game da shirin da ake na tura masu kudinsu kai tsaye, ya ce: “ai wannan wata babbar nasara ce a kananan hukumomi, sannan kuma ta haka za a samu damar aiwatar da wasu manyan ayyuka. Gaskiya muna maraba da wannan shawara,” inji shi.

Sai dai kuma shugaban kungiyar ya ce, duk da halin da kananan hukumomin suke ciki, wannan bai hana su zuwa aiki ba musamman a karamar hukumar ta Katsina kuma ma’aikatan suna bakin kokarinsu wajen gudanar da ayyukansu.

Abin jira a gani shi ne, ko hukumar NFIU da gaske take yi kuma a shirye take wajen fara sanya wa kananan hukumomi kudadensu kai tsaye ko akasin haka. Sannan majalisar kasa ita ma tana da tata gagarumar gudunmawar da za ta bayar wajen ceto kananan hukumomi ta hanyar warware tarnakin da Kundin Tsarin Mulki ya yi masu. Lokaci shi ne babban alkali.