✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda gurgu ke kasuwanci a titin Abuja

Aminiya ta gana da wani gurgu a Abuja, wanda duk da nakasarsa amma ya jajirce da kasuwancinsa, inda yake sayar da turaren mota a gefen…

Aminiya ta gana da wani gurgu a Abuja, wanda duk da nakasarsa amma ya jajirce da kasuwancinsa, inda yake sayar da turaren mota a gefen titin Solomon Lar da ke Unguwar Utako. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya: Ko za ka fara da gabatar da kanka?
Sunana Alhaji Aliyu Muhammad kauran Zamoda. An haife ni a unguwar Tungar Rairai da ke karamar hukumar kauran Zamoda ta Jihar Zamfara kimanin shekara 37 da suka wuce. Na yi karatun addinin kwarai da gaske, amma ban samu na yi karatun boko ba.
Aminiya: Kamar wadanne kaya kake sayarwa?
Ina sayar da turaren nan ne da ake sanya wa a gaban mota wanda ake kira Air Freshener a harshen Turanci.
Aminiya: Wane lokaci ka zo nan Abuja?
A gaskiya na dade ina zuwa nan Abuja kusan tun ina yaro nake zuwa nan.
Aminiya: Me ya ja hankalinka zuwa wannan sana’ar?
Abin da ya ja hankalina zuwa wannan sana’ar shi ne gaskiya ba na kaunar bara. Wannan ya sa na zauna na roki Allah Ya ba  ni  sana’a wadda zan iya dogaro da kaina, ba tare da na kaskantar da kaina ga wani bawansa ba.
Aminiya: Ka taba yin bara a baya?
Eh, na taba yin bara a Jihar Legas da kuma sauran yankunan Yarbawa.
Aminiya: Bayan wannan sana’ar ka taba yin wata?
Eh, na taba yin sana’ar suyar doya da kwoi. Saboda ban a kaunar bara ya sa na fara gwada wannan sana’ar.
Aminiya: Kana da wani kira ga sauran jama’a?
Eh, kiran da zan yi ga sauran jama’a musamman mutanenmu ’yan Arewa shi ne sai mutum ya ratsa yankin kudancin ne, ya ga yadda suke tafiyar da rayuwarsu da ’yan uwansu. A gaskiya su ma suna na da nakasassu kamar yadda muke da su, amma ba sa wulakantasu kamar yadda mu muke yi.
Aminiya: Akwai wani kalubale da kake fuskanta?
Babu. Kodayake, akwai jami’an da suke hana tallace-tallace a titunan Abuja wato (AEPB), wadanda idan na gamu da su sukan ce na ja gefe. Amma ba su taba kama ni ba.
Aminiya: Wace fa’ida ka samu albarkacin wannan sana’ar?
Babbar fa’idar dai ita ce ban taba rasa abin da zan ciyar da kaina da kuma iyalina ba.
Aminiya: Kana da wani buri?
Babban burina shi ne na ciyar da iyalina (matana biyu da ’ya’yana uku) da kuma mahaifiyata. Tun da mahaifina ya rasu tun ina karami.
Aminiya: A lokacin da kake gabatar da kanka na ji ka ce “Alhaji”, ka taba yin aikin hajji ne?
Eh, na taba zuwa kasar Saudiyya, inda na sauke farali kimanin shekara takwas da suka wuce ke nan.