Alkaluman Hukumar Kashe Gobara ta Turai (EFFIS) sun nuna cewa, kadada 660,000 gobarar daji ta cinye tsakanin 1 ga watan Janairu zuwa 13 ga watan Agusta.
Alkaluman sun nuna cewa, an samu karin kashi 56 cikin dari na barnar da gobarar ta yi a tarihin da aka kafa a baya a cikin lokaci guda a shekarar 2017, inda kadada 420,913 suka kone.
- Mutum 16 sun mutu, 21 sun jikkata a hatsarin mota a Turkiyya
- Yajin aikin ASUU: Hana malaman jami’a albashi ba laifi ba ne
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa, muddin aka ci gaba da samun aukuwar gobarar dajin a wannan yanayi da lokaci, akwai yiwuwar ta kone fiye da kadada miliyan daya a bana kadai.
Gobarar dajin ta fi muni a Spain
Kasar Spain ce ta fi fama da matsalar a bana inda gobarar dajin ta lalata filayen da suka kai girman hekta 244,924, sai Romania (kadada 150,528) da kuma Portugal mai hekta 77,292.
EFFIS na amfani da bayanan tauraron dan adam, inda a Juma’ar da ta gabata hukumar ta yi gargadin cewa mafi rinjayen kaso na Yammacin Turai yanzu yana cikin “mummunan hadari.”
Bayanan sun alakanta yankuna da yawa na Spain za su iya fuskantar mummunan hadari ciki har da Andalucia, Castilla y Leon, Castilla La Mancha, Catalonia, Aragon da yankunan Valencia.
An kashe gobarar Faransa
A makon jiya ne Faransa ta ce ta dakatar da bazuwar wutar daji a kusa da Bordeaux da ke Kudu maso Yammacin yankin Gironde na kasar.
Jami’an kwana-kwana a Faransa dai sun yi ta fadi-tashin shawo kan gobarar mafi muni da ta tilasta wa fiye da mutum 10,000 sauya matsugunnai.
Hukumar Kashe Gobarar ta Faransa ta ce ta gano bakin zaren wutar dajin da ta yi barna sosai a yankin Kudu maso Yammacin Faransa a ranar Juma’a, inda ta bayyana cewa wannan rana ta kasance mai wahalar gaske ga ma’aikanta.
Da yake zanta wa da manema labarai, Mataimakin Shugaban Hukumar yankin, Ronan Leaustic, ya ce wutar da ta mamaye tsawon kilomita 40 na sassan Gironde da Landes da ke kusa da Bordeaux ba ta ci gaba ba sosai ba, amma yanayin zafi da ya kai maki 37 a ma’aunin Celsius ya tilasta suyi taka tsantsan.
Kimanin jami’an kashe gobarar Faransa 1,100 ke aikin, yayin da suka samu karin abokan aikinsu 361 daga kasashen Jamus da Poland da Austiria da Romania, tare da daukin jiragen feshin ruwa da dama daga rundunar Tarayyar Turai.
Tuni hukumar da ke sa ido kan tauraron dan adam ta Tarayyar Turai ta sanar da cewa, gobarar da ta kona dubun-dubatar kadada da dazuzzukan kasashen Faransa da Spain da Portugal, ta ayyana shekarar 2022 a matsayin mafi muni a yankin Kudu maso Yammacin Turai.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Birtaniya ta ayyana aukuwar fari a wasu sassan Ingila, a wani mataki da kungiyar EU ta kwatanta shekarar 2022 a matsayin mafi munin yanayin zafi da kudancin Turai ya taba fuskanta.
Gobarar daji ta kone gidaje 50 a Rasha
’Yan kwana-kwana kusan 300 suka yi kokarin kashe wata gobarar daji da ta tashi tun ranar Litinin ta kuma ci gaba da ci har Talata wacce ta kone gidaje akalla 60 a Kudancin Rasha.
A cewar wasu rahotani na kafafen yada labarai na yankin, gobarar ta tashi ne tun a ranar Litinin a dajin Ust-Donetsk da ke Arewacin Rostov, inda ta kwana tana ci.
Gobarar ta kone kimanin kadada 136 na filayen noma a safiyar ranar Talata, inda ta yi barna a wasu kauyuka uku.
Kamfanin Dillacin Labarai na gwamnatin Rasha TASS ya ce, Ma’aikatar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasar, ta sanar da cewa, ta kwashe ilahirin mazauna kauyukan zuwa tudun mun tsira.
Ma’aikatar ta samar da jirgi mai kashe gobara da karin wani jirgin mai saukar ungulu guda daya da masu aikin kashe gobara 300 da kuma kayayyakin aikin kashe gobara daban-daban har guda 90.
Fari ya tilasta rage yawan wutar lantarki
Haka kuma a makon da ya gabata ne Birtaniya ta ayyana samun fari a wasu sassan Ingila, mafi muni tun a shekarar 1935, biyo bayan karancin ruwan sama da aka samu na tsawon watanni da kuma yanayin zafi da ba a taba ganin irinsa ba a ‘yan makonnin nan.
Fari da ake ci gaba da fuskanta a kasashen Turai na haifar da cikas ga kamfanoni da dama, yayin da bangaren makamashi na yankin ke kara shiga cikin matsi.
Yanayi na rani ya jawo karfin samar da lantarki ta hanyar amfani da madatsun ruwa ya yi kasa da kashi 20 cikin 100.
A kasashen Italiya da Sifaniya da suka fi shan wahalar raguwar kwararan ruwa a kogunansu, sun rage yadda ake amfani da ruwan daga rafuka wajen sanyaya cibiyoyin sarrafa nukiliya.
A Birtaniya, masana sun ce an samu rauni kan yadda cibiyoyin samar da karfin wutar lantarki masu amfani da gas ke aiki saboda wahalar da ake sha wajen sanyaya na’urori.
Kazalika, su ma farantan samar da karfin wuta ta amfani da hasken rana sun rage abin da suke samarwa.
Gobarar daji za ta iya durkusar da kasuwanci
Mummunan yanayin zafi da aka fuskanta a bayan nan ne ya haifar da gobarar daji a fadin Turai a wannan bazarar, lamarin da ke barazana da dumamar yanayi da matsaloli na kasuwanci.
Fari dai na haifar da asarar kayayyakin amfanin gona da sauran kayan abinci a daidai lokacin da karancin wadatar kayayyaki da yakin da Rasha ke yi da Ukraine ya haifar da tashin gwauron zabi.
Tafkin Garda na Italiya ma na ci gaba da kafewa fiye da yadda aka taba gani, yayin da ruwan da ke kusa da kogin Rhine na Jamus ke fuskantar wannan hadari wanda zai iya zama abin fargaba ga jigilar kayayyaki – ciki har da makamashi.
Tuni dai zirga-zirgar ababen hawa ta soma tafiyar hawainiya a Turai.