✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda gobara ta yi barna a babbar kasuwar jihar Edo

Gobara ta tashi a babbar Kasuwar Obaka da ke kwaryar birnin Benin na jihar Edo inda ta cinye kaya na miliyoyin naira, bayan shafe awanni…

Gobara ta tashi a babbar Kasuwar Obaka da ke kwaryar birnin Benin na jihar Edo inda ta cinye kaya na miliyoyin naira, bayan shafe awanni tana ci ta kuma kone kusan daukacin kasuwar.

Shaidu sun ce gobarar ta tashi ne bayan karfe 12.00 na dare kuma ta yi ta ci har bayan zuwan hukumomin kashe gobara inda ta kai safiyar Litinin kafin a samu nasarar shawo kanta.

Mataimakin Kwanturolan Hukumar Kashe Gobara ta Kasa da ke Asaba a jihar Deltar mai makwabtaka da Edo, Samson Karebo, ya tabbatar da iftila’in, wanda ya ce sun kawo daukin kashewa bayan hukumomin jihar Edo sun nemi agaji daga wurinsu.

“Na da samu labarin gobarar sai na yi maza na zo ko zan samu in kwashe kayana kafin wutar ta kai shagona amma ko da na isa sai na iske shagon nawa ya kone kurmus”, inji Habiba, wata mai shagon sayar da kayan kwalliya a kasuwar.

Ita ma Osasuwa Anthony da ke da kanti a kasuwar ta ce, “wuraren 1.00 na dare aka kira ni cewa kasuwar Oba na ci da wuta. Nan take na fito amma na zo na iske komai ya kone a shagona”.

‘Yan kasuwar da abin ya shafa sun bayyana damuwa tare da kira ga gwamnatin jihar da ta tallafa musu.

Tashin gobarar na zuwa ne kwanaki kadan bayan ‘yan kasuwa sun koma gudanar da harkokinsu a kasuwannin da suka saba, bayan gwamnatin jihar ta rufe makarantun da aka yi amfani da su a lokacin kullen COVID-19 a matsayin kasuwannin wucin gadi.

Karebo ya ce sun yi aikin kashe gobarar kasuwar Obaka ne da hadin gwiwa ‘yan kwana-kwana daga rundunar sojojin sama da na kada da Jami’ar Benin (UNIBEN) da kuma hukumar NNPC.

Ya kara da cewa za su gudanar da cikakken bincike domin gano hakikanin abin da ya haddasa gobarar.