Gini a kan magudanar ruwa ne ya haddasa wata ambaliyar da ta yi sanadin salwantar rayukan mutum biyar da dukiya mai yawa a Karamar Hukumar Gwagwalada ta Yankin Babban Birnin Tarayya.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ce ta bayyana haka yayin wata ziyara da manyan jami’anta suka kai ranar Lahadi wurarern da lamarin ya faru.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ambato Daraktan Tsare-tsare da Bincike na Hukumar, Mista Kayode Fagbemi, wanda ya wakilci Darakta Janar AVM Muhammadu Mohammed yayin ziyarar, yana dora alhakin ambaliyar a kan tare magudanan ruwa.
“Har yanzu dai muna wayar da kan jama’ar da ke zaune a kusa da magudanan ruwa da su tashi saboda yanzu fa watan Yuli ke nan, kuma da sauran ruwan sama a gaba.
“Muna rokon jama’a su share lambatu; lallai ne a kwashe sharar da ta toshe hanyoyin ruwa, mutanne da ke kusa da magudanan ruwa kuma su koma kan tudu.
“Ba ma so mu kara asarar rayuka; ya kamata mutanen su san cewa an yi hasashen ruwa zai yi ambaliya bana”, inji shi.
Uwa da ‘ya’yanta ruwan ya ci
A cewar Mataimakiyar Daraktan Hasashe da Kai Dauki a Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Yankin Babban Birnin Tarayya (FEMA), Misis Florence Wenegieme, mutum biyar ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ta ranar Asabar.
“Mutum biyar ruwa ya ci, amma mun yi nasarar samo gawar mutum daya – da muka zo yau don ci gaba da nema sai muka samu labarin cewa an ga gawar wata mata a kauyen Gomani da ke Karamar Hukumar Kwali.
“Amma dai za mu ci gaba da bincike ko a dace. Wata mahaifiya ce da ’ya’yanta hudu ruwan ya ci – kuma gawar da muka samu jiya ta daya daga cikin yaran ne, ko da yake ba mu tabbatar da ko gawarta ce aka ce an gani a kauyen Gomani ba”, inji ta.
Daya daga cikin mutanen da suka yi asara, Mista Geoffrey Okere, ya ce tun karfe 3.00 na asuba aka fara ruwan da ya haddasa ambaliyar, ya kuma karu da misalin karfe 6.00 na safiyar ranar ta Asabar.