✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda garkuwa da mutane ta bunkasa a wata biyar

Jami’an tsaro su yi aiki tare, kada a rika samun gasa da rashin jituwa a tsakaninsu. Su hada kansu su yi aiki tare.

Karuwar garkuwa da mutane a wasu sassan jihohi kasar nan alama ce da ke nuna akwai sauran jan aiki a gaban bangaren tsaro na kasar nan a kokarinsa na kawo karshen matsalar.

Duk da cewa shugabanni ba su yi magana ba a kan wannan rahoto har zuwa wallafawa, Aminiya ta gano har yanzu akwai daliban Jami’ar Gusau da aka sace a dakunansu a safiyar 22 ga watan Satumba da suke hannun ’yan fashin daji.

Jami’an tsaro sun samu ceto wasu daga cikin daliban, amma babu bayani a kan makomar sauran daliban saboda har yanzu Hukumar Jami’ar da jami’an tsaro ba su yi karin bayani ba.

Akwai wasu dalibai mata biyu da su ma aka sace a Jami’ar Jihar Nasarwa da ke Keffi a watan Oktoban nan a garin Keffi.

Alkaluman da Aminiya ta samu sun nuna cewa an yi garkuwa da mutum 1,158 daga watan Yuni zuwa ranar 9 ga Oktoba.

Wannan ya wuce alkaluman da aka samu a baya daga watan Janairu zuwa Mayu a karkashin mulkin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Wata bayan wata alkaluman yawan garkuwa da mutane da aka yi na nuna a watan Satumba kadai an yi garkuwa da mutum 498 inda watan Agusta ke biye da mutum 213 sai Yuni da ke da da mutum 178.

Haka kuma a watan Yuli an samu rahoton sace mutum 176 sannan a watan Oktoba zuwa ranar 9 ga watan an sace mutum 93.

Alkaluma sun kuma nuna cewa daga watan Yuni zuwa Oktoba, Jihar Kaduna ce a kan gaba wajen yawan wadanda aka sace da mutum 162, Jihar Zamfara ke biye da 133 sai Taraba mai 126.

Sauran su ne Neja da mai mutum 119 da Bauchi mai mutum 82, Borno mutum 75 sai Abuja mutum 64.

Daga yanki zuwa yanki kuwa alkaluma na nuna cewa a Arewa maso Tsakiya an samu rahotannin sace mutane sau 64 a karkashin mulkin Shugaba Bola Tinubu idan aka gwada da lokacin mulkin Buhari da aka sace mutane sau 62.

A Arewa maso Yamma an samu rahotannin sace mutane sau 51 a lokacin Tinubu maimakon 38 lokacin Buhari.

A yayin da Arewa maso Gabas ke da rahotanni 22 lokacin Tinubu da 8 lokacin Buhari.

Bayanai sun nuna cewa yankin Kudu maso Yamma an samu rahotannin sace mutane sau 20 a karkashin Tinubu idan aka hada da 21 a mulkin Buhari.

Kudu maso Kudu kuwa an samu rahotanni 23 a lokacin Tinubu sabanin 21 a lokacin Buhari.

Ita kuwa Kudu maso Gabas an samu rahoto 14 a lokacin Tinubu sabanin 19 a lokacin Buhari. Arewa maso Tsakiya ta kunshi Babban Birnin Tarayya Abuja, Nasarawa, Kwara, Kogi, Neja, Benuwai da Filato.

Arewa maso Yamma kuwa ta kunshi Kano, Kaduna, Jigawa , Katsina,Kebbi, Sakkwato da Zamfara.

Arewa maso Gabas ta hada Adamawa, Gombe, Borno, Yobe, Bauchi da Taraba.

Yankin Kudu maso Yamma shi ne Legas, Ogun, Osun, Ondo, Oyo da Ekiti.

Kudu maso Kudu kuwa ya hada jihohin Akwa Ibom, Kuros Riba, Bayelsa, Edo, Delta da Ribas. Jihohi Abiya da Yobe ne kawai ba su da rahoton garkuwa da mutane a shekarar nan.

Alkawuran magance matsalar tsaro

Aminiya ta ruwaito lokacin da Shugaba Tinubu ke takara a Jam’iyar APC, a ranar 20 ga Oktoban 2022, ya fitar da muradunsa mai shafi 80 yana bayanin manufofinsa takwas.

Kan gaba a manufarsa ita ce batun tabbatar da tsaron kasa da tattalin arziki da noma da samar da wutar lantarki da gas da kuma man fetur da inganta sufuri da ilimi.

Wannan kundin manufa an yi masa take da Sabunta Manufa (Renew Hope 2023) domin ci gaban Nijeriya.

Kuma ya yi alkawarin daukar sojoji su kai 750,000 tare da kara yawan ’yan sanda zuwa miliyan daya.

A kan batun manufarsa a fanin tsaro Tinubu ya ce “Za mu ci gaba da yaki da ’yan ta’adda ta hanyar canza tsarin yaki da su.

“Salon yaki da ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyuka zai ta’allaka ne ga wannan tsari namu.

“Za mu kara yawan sojoji da sauran jami’an tsaro da ’yan sanda. Za mu samar wa jami’an tsaronmu kayayyakin sadarwa masu inganci da motoci da jiragen sama domin inganta ayyukansu.

“Ta wannan hanyar da wasu matakai za mu sanya ido tare da bibiyar wadannan miyagun mutane don kawar da su a duk inda suke.

“Ba za su taba samun natsuwa ba har sai sun mika wuya,” in ji manufar.

Har ila yau, Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa da Babban Hafsan Sojin Kasa Manjo Janar Taoreed Lagbaja a lokacin da suka bayyana a gaban majalisa don tantance su sun yi wa ’yan Nijeriya alkawarin cewa a karkashin jagorancinsu za su tabbatar da sojoji sun samu kwarewa ta musamman da kayan aiki domin gudanar da aikinsu.

Sun tabbatar da cewa rundunar soji ta kasa za ta kare martabar iyakokin kasar nan da kuma tsarin dimokuradiyya da tsaro domin samun tabbataccen ci gaba a kasa.

Janar Musa ya ce rundunar sojin za ta tabbatar da sa Nijeriya kan gaba wurin tabbatar da ci gabanta.

Ya kara da cewa, “Ina tabbatar wa jami’in tsaro maza da mata kyawawan manufata ga jin dadinsu da kuma samar masu da kayan aiki daga dan abin da muke da shi a hannu domin su samu damar gudanar da ayyukansu cikin sauki kamar yadda dokar kasa ta tanada.

“Zan kuma inganta alaka da sauran kasashen waje da hadin kai a bangaren tsaro domin inganta kwarewar jami’anmu don gudunar da ayyuka a wajen Nijeriya.

“Wannan mataki na bukatar inganta jin dadin jami’an domin yaki da kuma samun nasara ga kasarmu don ba da kariya a kan iyakokin kasar nan ta kasa da sama da ruwa ta hanyar hadin gwiwa,” in ji shi.

Har yau, ’yan Nijeriya suna jira a cika masu wadannan alkawura da shugabanni tsaro da Shugaban Kasa suka yi musamman a yanzu da matsalar tsaro ke ci gaba da tabarbarewa.

Tsohon Kwamishinan ’Yan sanda ya ba da mafita

A tattaunawa da daya daga cikin wakilanmu, tsohon Kwamishinan ’Yan sandan Abuja Lawrence Alobi ya dora alhakin karuwar sace mutane ne a kan rashin wayar da kai da Hukumar Wayar da Kai ta Kasa (NOA) ba ta yi.

Tsohon dan sandan ya bayyana NOA wadda hukuma ce ta Gwamnatin Tarayya da aka samar domin ilimantarwa da wayar da kan ’yan kasa a kan yadda za su ba da gudunmawarsu wajen bin doka a cikin al’umma amma ba ta aikinta yadda ya kamata.

A cewarsa, wani sashe na Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya ba da dama ga hukumar ta rika wayar da kan mutane domin sanin rawa ko gudunmawar da za su bayar domin ci gaban kasa.

“Akwai rashin kula a aikin ’yan sanda a Nijeriya saboda haka akwai bukatar wayar da kan jami’ai.

“Akwai rawar da gwamnati za ta taka. Hukumar NOA ba ta yi abin da ya kamata.

“Wani sashe na Tsarin Mulkin Kasa ya ce kafin mutum ya zama cikakken dan kasa dole sai ya taimaka wa gwamnati wajen tabbatar da doka da oda.

“Har zuwa yanzu ba kowa ya san rawar da zai taka ba a kasar nan, kowa na yi yadda ya so. Al’adar sadaukar da kai domin kasa ta ci gaba tana bacewa,” in ji shi.

Alobi ya shawarci jami’an tsaro su hada kai wajen yi aiki tare domin cim ma manufar inganta rayuwar al’umma da kasa, inda ya ce bai kamata a rika samun gasa a tsakanin jami’an tsaro ba.

Ya ce, “Jami’an tsaro su yi aiki tare, kada a rika samun gasa da rashin jituwa a tsakaninsu. Su hada kansu su yi aiki tare ga kasa.”

Da yake bayanin abin da ya sa garkuwa da mutane ta ki cinyewa sai ya ce a lokacin da yake aiki, “A lokacin aiki dole ne ka tashi tsaye dole ka rika tunani da shirin kota-kwana.

“Ina da kusanci da mutane. Ina aiki tare da mutane saboda haka ya sa mutane ke aiki da ni. Aikin dan sanda ba yana nufin tilasta bin dokar ba ne kadai, dole ka rika tafiya da mutanen yankin da kake.

“Aikin dan sanda na nufin kusanci da mutane. Ya danganta da kusancinka da mutane. A lokacin da nake Kwamishina a Abuja nakan fada wa ma’aikatana yadda za su kula da kannensu maza da mata a kauyakansu haka ya kamata su kula da Abuja.

“Ina kuma ba su umarnin kada su kuskura su taka hakkin mutane. Ina yin haka ne domin nuna masu yadda za su tausaya wa mutane wanda kuma duk a cikin aiki ne.

“Gaskiyar zancen akwai bukatar yin kokari wajen ganin an yi abin da ya dace, dole ka kasance mai tunani da sanin ya kamata kuma yana da kyau ma’aikata su kasance suna daunar aikinsu da muhimmanci.

“Akwai hanyoyin magance wannan matsala, da farko dole a kyautata aikin ’yan sanda, na biyu dole a rika tura su koyon sanin makamar aiki a-kai-a-kai saboda dan sandan da bai sai aiki ba annoba ne ga al’umma da kuma aikin kansa.

Hukumar NOA

Da aka tuntubi Kakakin Hukumar Wayar da Kai ta Kasa (NOA), Paul Odenyi ya ce ba zai iya magana ba a kan kowane batu ba a lokacin saboda garambawul da aka yi a hukumar.

Wakilinmu ya ruwaito cewa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Alhamis din makon jiya ya sauya shugabannin wasu hukumomi da ke karkashin Ma’aikatar Yada Labarai ta Tarayya cikin har da Hukumar NOA.

Sai dai Odenyi ya yi bayanin cewa sai ya samu amincewar wanda ke shugabantar hukumar a yanzu kafin ya iya cewa wani abu domin ya ce sabon Darakta Janar na Hukumar bai fara aiki ba a lokacin.

Haka kuma Shugaban Tsara Bayanai a Ofishin Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Zakariya Usman ya umarci daya daga cikin wakilanmu, kan ya aika masa da sakon abin da yake nema ta shafinsa na WhatsApp a kan batun.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai aiko da amsar sakon ba.