Shekara shida ke nan Mariya Aliyu na fama da kuncin rayuwa da fargaba saboda rashin sanin inda danta yake ko halin da yake ciki. Duk kokarin da ta yi na sanin inda ya ke ya ci tura.
Mariya, wacce ke zaune a Samaru da ke birnin Zaria a jihar Kaduna, ta bayyana yadda “wasu sojoji suka yi awon gaba da danmu cikin dare.
“Bayan gari ya waye, mun yi yawon neman inda yake kuma mu san laifin da ya aikata, amma har yau babu wani bayanin da muka samu”.
Kafin sojojin su kama shi kuma daga bisani su mika shi ga hukumar tsaro ta SSS, Isa Umar yana aji uku ne a Sashen Kimiyyar Adanar Littatafai da Bayanai na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
Wani abokin Isa Umar wanda suke karatu tare a jami’a, Anas Adamu, ya shaida wa Aminiya cewa tun bayan kama shi, mahaifiyarsa mai shekaru 60 take fama da rashin lafiya wanda ke da alaka da damuwar da ta shiga, har ta kai ga an kwantar da ita a asibitoci da dama.
‘Saninmu da Isa’
Anas ya ce tare suka samu gurbin shiga jami’a kuma suka kwashe shekaru uku tare. amma bai san Isa Umar da wani mugun hali ba.
“Tun daga yarinta har zuwa lokacin da aka kama shi, mu ba mu san Isa da wani tarihin aikata mugun laifi ba.
“Mutumin kirki ne kuma malami a wata makarantar Islamiyya da ake kira Madrasatu Tarbiyyatil Islamiyya wa Lugatil Arabiyya, wadda aka fi sani da Danraka a Samaru”, inji Anas.
Wani wanda bai so a ambaci sunansa ba ya bayyana wa Aminiya cewa Isa Umar ya yi sa-in-sa da wasu malaman addini wadanda ke zarginsa da tsatsauran ra’ayi a unguwar da yake zaune.
“Sa-in-sa ta shiga tsakaninsa da malamai a makarantar da yake koyarwa inda aka tattara wasu kudade saboda gudanar da wasu al’amuran makarantar.
“Wasu daga cikin malaman suka bukaci su raba kudin a tsakaninsu amma Isa Umar tare da wasu abokan aikinsa suka ki amincewa.
“Hakan ya sa suka fara yada jita-jita a kansu cewa suna da tsatsauran ra’ayi.
“A karon farko tare aka kama su da sauran kuma sai da aka kashe N300,000 kafin a sake su” inji majiyar.
A karo na biyu
Kwanaki kadan bayan faruwar hakan ne dai ma’aikatan tsaron suka sake kama shi ba tare da bayani a kan laifin da ya aikata ba.
Mahaifiyarsa ta ce sun bincika ofisoshin rundunonin tsaro daban-daban ba tare da samun bayanin inda yake ba.
“Munje ofishin DSS da ke Kaduna suka ce mu je Abuja. Da muka je Abuja suka dawo da mu na Kaduna.
“Ofisoshin biyu suka yi ta juya mu ba tare da cikakken bayani ba”, inji mahaifiyar Isa.
Saboda rashin cikakken bayani a kan dalilin kama shi, danginsa suka garzaya kotu a kan lamarin.
Hukuncin kotu
A ranar 7 ga watan Mayu na shekarar 2017, Mai Shari’a Emeka Nwita na Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna ya umurci hukumar ta DSS da ta saki Isa Umar wanda ya ke tsare tun shekarar 2014.
Kotun ta yanke hukuncin ne a karar da ‘yan uwan Isa suka shigar a gabanta mai lamba FHC/KD/CS/66/2016).
Kotun ta kuma ci tarar hukumar naira miliyan daya da dubu hamsin a matsayin fansar rike shi da aka yi ba bisa ka’ida ba.
Sai dai kuma a cewar ‘yan uwan Isa, hukumar ba ta mutunta hukuncin kotun ba saboda ta ci gaba da tsare shi.
Takardar da ke dauke da hukuncin da kotun ta yanke ta nuna cewa ci gaba da tsare Isa take hakkinsa ne kuma ya saba wa sashe na 34, 35 da 36 na Kundin Tsarin Mulki.
Ga duka, ga tsinka jaka
“Bayan faruwar hakan, wani ma’aikacin DSS a ofishinsu da ke Kaduna ya karbi N70,000 a wurinmu inda ya yi mana alkawarin fito da shi, amma bai yi hakan ba – wannan ne dalilin da ya sa muka daina sake jiki da duk wanda ya zo mana da batun.
“Rabonmu da jin duriyar Isa tun lokacin da kungiyar Red Cross ta kawo mana sako wanda na tabbata da kanshi ne ya rubuta”, inji dan uwansa Aliyu Isa.
Mahaifiyar ta yi kira ga hukumar DSS da ta saki danta tun da kotu ta ba da umurnin hakan.
Lauyan iyalan Isa, Kamaluddin Umar, ya ce akwai lauyan da ya wakilci hukumar ta DSS a shari’ar da kotun ta gudanar wanda tuni aka mika mishi hukuncin da kotun ta yanke.
Korafi ga Majalisar Kasa
Kamaluddin Umar ya ce bayan hukumar ta DSS ta ki bin umurnin kotun ne dai suka rubuta takardar korafi zuwa ofisoshin DSS dake Kaduna da Abuja inda suka bukaci a aiwatar da hukuncin.
“Abin da muke so da su shi ne su bi umurnin kotu. Hukuncin yana nan tunda har yanzu ba su daukaka kara ba kuma wata kotu ba ta soke shi ba. Mafi tsawon lokaci da ya dace a tsare wanda ake zargi shine awa 48”.
Lauya Umar ya kuma ce ya rubuta takardar korafi ga Majalisar Tarayya saboda ta sa baki a lamarin yana mai cewa tsare Isa Umar da hukumar ta yi ya gurgunta karatun da yake yi .
Da aka tuntubi DSS a kan lamarin, mai magana da yawunta Peter Afunanya ya ce, “Babu wani abu mai kama da haka a ofishin hukumar da ke jihar Kaduna”.