Mazauna garin Jos, sun koka kan karancin kayan abinci da sauran muhimman abubuwa a yankunansu sakamakon dawo da dokar hana fita gaba daya a yankin.
Mazaunan sun kuma koka game da yadda dawo da dokar ta jawo hauhawar farashin kayayyakin abinci da sauran kayan masarufi.
- Kashe-kashe: ‘Mutanen Filato su tashi su kare kansu’
- ’Yan bindiga sun sako Daliban Bethel Baptist 32
Gwamnatin Jihar Filato ta sake sanya dokar hana fita gaba daya ne bayan kisan gilla da mahara suka yi wa ’yan kabilar Anaguta a unguwar Yelwan Zangam da ke karamar hukumar Jos ta Arewa a daren Laraba.
Wakilinmu da ya zagaya ya ce mazauna yankin da suka fito neman abinci sun koka kan halin da dokar ta jefa su a ciki.
Wani mazaunin unguwar Janta Adamu mai suna Yakubu Busari ya ce lamarin ya jefa mutanen yankin cikin kunci.
A cewarsa, duk da cewa dokar hana fitar tana da mahimmanci, ta haifar da wahalhalu a yankin.
“Samun abinci yana da wahala sannan yawancin mutane ba su da kudi saboda sai sun fita suke samu kudin cefane.
“Sannan ba a samun katin waya saboda yawancin shaguna an rufe su.
“Yanayin na iya haifar da sace-sace da sauran ayyukan laifi a cikin al’umma,” inji shi.
Shi kuma wani mazaunin unguwar Laminga, Peter Azi, ya ce: “Dokar hana fitar na shafar mazauna unguwarmu sosai ta kowane fanni na rayuwarsu.
“Mutane ba za su iya zuwa gari don su duba lafiyarsu ba, sannan kayan abinci da sauran kayan masarufi sun yi karanci sosai saboda yawanci masu sayar da kayan galibi suna zuwa gari ne su sayo, ga shi kuma an kulle garin.”
A Unguwar Rogo, Hamza Musa ya ce, “A ganina yanzu ya kamata gwamnati ta sassauta dokar hana fita, saboda mutane na fama da yunwa kuma ya kamata a bar su su fita su samo abinci su ci.
“Idan yunwa ta kai matakin da ba za a iya jurewa ba, har mutane suka yanke shawarar fita, gwamnati ba za ta iya hana su ba.”
Yayin da suke kira da a dage dokar hana fitar, mazauna garin na Jos da dama sun bukaci gwamnati da ta tura jami’an tsaro a duk wuraren da akwai yiwuwar samun tashin hankali don kare rayuka da dukiyoyin jama’a.