Dogayen layukan mai sun sake dawowa a gidajen mai a Kano, tun a karshen mako saboda karancin man fetur, wanda daidaikun gidajen mai ke sayarwa a halin yanzu.
- Buhari na neman ciyo bashin tiriliyan 11 a 2023?
- Sarkin Kano ya koka kan dabi’ar rashin karantun littafai a tsakanin matasa
A gidajen mai ’yan kalilan da ke da man kuma ba su kara farashi daga N185 ba, da kuma gidajen man NNPC da ke sayarwa a N185, masu ababen hawa sun yi cikar kwari domin samu.
Wani mai tuka babur din A-Daidaita-Sahu, Shuaibu Ibrahim, ya shaida wa Aminiya cewa ya shafe kimanin awa biyu a kan layi kafin ya samu mai.
“Har yanzu ba a kara farashi ba a gidajen man da na sha mai daga jiya zuwa yau (Litinin).
“Suna sayar da lita a kan N185 amma sai da na kai awa biyu kafin na samu, wanda hakan na shafar sana’armu, kuma fasinjojinmu ba za su fahimta ba idan aka yi musu karin kudi.”
“Ban san me ya faru ba, amma na lura akwai karancin mai kuma an kara farashinsa,” in ji wani mai abin hawa, Gambo Shuaibu, a hirarsa da wakilinmu.
Kasuwar ’yan bumburutu ta bude
Wasu daga cikinsu sun bayyana wa Aminiya, “Mu ma sai mun bi layi a gidajen mai da tsakar dare muke samu, kuma sun yi mana karin kudi, saboda haka ba mu da zabi, dole sai mun kara farashi.”
Akwai wadataccen mai
Shugaban zauren, Alhaji Musa Y Maikifi ya ce, “Yanzu rashin kyan hanya ne matsalar, domin a yanzu direba kan kwashe kwana uku a tafiyar da ba ta wuci kilomita 70.
“Wannan shi ne ya haifar da wadannan matsaloli, amma ba mu kara farashi ba har yanzu.”