✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda datse sadarwa ta shafi kasuwanci a Zamfara

Mazauna jihar sun koka cewa matakin ya gurgunta harkokin kasuwancinsu.

Mazauna Jihar Zamfara sun nuna damuwarsu kan datse layukan tarho da na intanet da hukumoni suka yi a jihar, matakin da suka ce ya gurgunta harkokin kasuwanci.

Duk da haka, mazauna yankunan da matsalar tsaro ta fi kamari a jihar sun ce suna maraba kuma za su jure duk matsalolin suke fuskanta a yanzu idan har matakin zai kawo dorewar zaman lafiya da kawo karshen ta’addanci.

Tasirin rufe layukan sadarwa

Rahotannin daga Zamfara na nuni da cewa a halin yanzu wasu mazauna jihar na tururuwa zuwa jihohin makwabta don kiran danginsu da abokan kasuwancinsu.

Rufe layukan sadarwar ya sa harkar banki ta tsaya cak, hakazalika harkokin kasuwanci sun ragu, mutane kuma na nuna damuwa saboda matakin ya hana su sanin halin da ’yan uwansu ke ciki a a sassan jihar.

Wasu ’yan jihar sun bayyana sun ce sun sha wahala tun daga ranar Juma’a da aka sanya dokar da ta sa suka kasa cirar kudi daga bankuna ko kiran waya.

Wasu daga cikinsu da BBC ta zanta da su  sun ce, “Daga Dansadau a Karamar Hukumar Maru, na je Funtuwa a Jihar Katsina don samun damar kiran waya da gudanar da kasuwancina saboda rashin sadarwa”.

Ita ma wata kwararriya kan kafafen sa da zumunta, wadda ta yi balaguro zuwa wata jiha ta ce katse layukan sadarwan ya yi tasiri sosai a harkar kasuwancinta.

“Yawanci ina gudanar da harkokina a kafafen sa da zumunta; Ina dora abin da nake sayarwa a kafar WhatsApp da Facebook, kun ga wannan ya shafi rayuwata sosai tunda an dakatar da komai, to ta ina zan fara?”

A gefe guda kuma, mutanen da ke zaune a wajen Jihar Zamfara su ma matakin ya hana su shiga cikin danginsu da ke zaune a jihar da abin ya shafa.

Duk da haka, mutane da dama a Jihar sun ce idan hakan zai kawo zaman lafiya da kawo karshen ta’addanci, to suna maraba kuma da hsi za su jure.