✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda dangantaka tsakanin Najeriya da Kamaru take bunkasa

A shekaraniya Laraba ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyarar aiki na tsawon kwanaki biyu a Kamaru. Ziyarar ta Shugaban Najeriya ta zo ne…

A shekaraniya Laraba ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyarar aiki na tsawon kwanaki biyu a Kamaru.

Ziyarar ta Shugaban Najeriya ta zo ne a wani mawuyacin yanayi, inda kungiyar Boko Haram take ta rubanya kai hare-haren kunar bakin-wake a lardin Arewa-mai-Nisa na Kamaru mai makwabtaka da Najeriya. Saboda haka batun tabbatar da tsaro a tsakanin kasashen biyu har da kuma a duk fadin yankin tafkin Chadi ya mamaye tattaunawar da Shugabannin biyu suka yi.
Ana fatan fara samun haske game da dangantakar da take a tsakanin Kamaru da Najeriya. Hakan zai samu tabbata karkashin sakin jiki da Gwamnatin Kamaru za ta yi wurin bai wa jami’an tsaron kasashe makwabta masamman ma Najeriya daman shiga Kamaru har idan akwai bukata domin farautar duk wasu masu ta da tarzoma. Samun haka kuma zai ba da tabbacin cewa rundunar hadin gwiwa da kasashen suka kafa da ake dakatar ganin ta fara aiki, ba za ta fuskanci matsala ba wurin yin zobe a duk fadin kasashen da suka kafa tafkin Chadi. Wannan ziyara ta Shugaba Buhari ita ce ta shida da wani shugaban Najeriya yake kawo wa Kamaru tun shekarar 1999. Hakazalika, shi ma Shugaban kasar Kamaru ya kai ziyara Najeriya a shekarar 1983 kasar da ya fara kai wa ziyara ke nan bayan an rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a shekara guda daga bisani. Har ila yau, kuma ya sake kai wata ziyara a shekarar 1991. Sai shekarar 2003 ya halarci taron kungiyar CommonWealth da aka yi a Abuja, ba ya ga haka kuma a cikin wannan shekara ya sake koma wa Najeriya, inda ya halarci bikin rantsar da Shugaba Obasanjo. A shekarar 2007 ya sake koma wa Najeriya domin halartan makamancin bikin a wannan karo na marigayi Shugaba Umaru Musa ’Yar Adu’a. Bugu da kari, ya sake kai ziyara Najeriya domin halartan bikin cika shekaru 50 samun ’yancin kasar a watan Oktoban shekarar 2010.
Ta fuskar hulda a tsakanin kasashe biyu kuma Kamaru da Najeriya sun sa hannu a kan yarjejeniyoyi kusan 15 a kan fannonin da suka danganci tsaro, shari’a, kai kawon jama’a da kuma dabi’u. Kamaru da Najeriya kasashe biyu ne da suka raba iyaka mai tsawon kilomita 1,600 murabba’i da ya tashi daga Tafkin Chadi zuwa yankin Nije Delta. Wannan iyakar kuma ta bude wa al’umomin kasashen biyu damar yin shiga da fice daga wannan kasar zuwa wancan. Baya ga haka kuma ya sake haifar da harkokin kasuwanci.
A yau dai ana cewa Najeriya ce kasa ta biyu da take shigo da kayan haja Kamaru a yayin da Kamaru ita ce kasa ta 14 wurin sayan kayayyakin da suke shigo wa daga Najeriya. Sai dai kuma wannan harkar ta samu dan tangarda tun lokacin da hare-haren kungiyar Boko Haran ta kunno kai ta kan iyakokin kasashen biyu masamman a yankin arewacin kasashen biyu. A shekarar 2013 darajar daukacin kayayyakin da Najeriya ta shigo da su ta kama makudan kudaden da yawansu ya kama Biliyan 452 da Miliyan 18 na kudin CFA. Darajar kayayyakin da Kamaru ta shigar Najeriya kuma sun haura CFA Biliyan 39 da Miliyan 531. Akasarin kayayyakin da Kamaru take saya daga Najeriya sun hada da man fetur da dangoginsa, kayayyakin gina gidaje, atamfofi, yaduna da wasu kayayyaki na aikace-aikace. Kashi hudu na daukacin kamfanonin da suke kafe a Kamaru na ‘yan asalin Najeriya ne. Ita kuma Najeriya na sayen kayayyakin abinci, da awakai, da man girki da sabulai. Domin karfafa shigowar kayayyakin kasuwanci a tsakaninsu, Gwamnatocin Kamaru da Najeriya sun sanya hannu a kan wata yarjejeniya a ranar 11 na watan Afrilu a shekarar 2014 wadda ta fadada kayayyakin kasuwanci da kuma sawaka shigowa da wasu. Hakan ya dada bunkasa adadin masu saye da sayarwa a kan mutane miliyan 190.
Ana kiyasta cewa akwai mutane sama da miliyan hudu ’yan asalin Najeriya wadanda suke rayuwa a Kamaru. Akasarinsu kuma duk ‘yan kasuwa ne wadanda suke tafiyar da harkokin sayar da karafan motoci. Hakannan ma akwai ‘yan Kamaru da dama mazauna Najeriya wadanda karatu ne akasarinsu suke yi a jami’o’in Najeriya daban-daban. Al’umomin kasashen biyu kuma na cudanya da juna sosai ta fannin al’adun gargajiya, zamanta kewa har ma da auratayya a tsakaninsu. Hausawan Najeriya da Hausawan Kamaru, Fulanin Kamaru da Fulanin Najeriya. Ejagham Najeriya da Ejagham na Kamaru da sauran kabilu daban kuma masu cudanya a tsakaninsu.