A watan Yunin bana ne Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid ta saki dan wasanta dan kasar Beljiyum, Eden Hazard, wanda shi kuma a ranar Talatar da ta gabata ya yi tabbatar da ritayarsa daga buga wasa yana mai shekara 32 kacal.
A sanarwarsa ta yin ritaya, ya bayyana cewa, “Dole ka saurari jikinka, domin ajiye wasa a lokacin da ya dace.
- ‘Yan sama-jannati sun shafe kwana 371 a sararin samaniya
- An ceto wasu daliban Jami’ar Gusau da aka sace a Zamfara
“Bayan shekara 16, inda na buga sama da wasa 700, na yanke shawarar yin ritaya daga kwallon kafa.
“Lallai na samu damar cika burina na buga kwallo a filayen kwallo manya na duniya.
“A lokacin da nake taka leda, na samu sa’ar samun horo a karkashin zaratan kocikoci, sannan na buga kwallo tare da zaratan ’yan wasa.
“Ina godiya ga dukkansu. Godiya ta musamman ga kungiyoyin da na bugawa kwallo irin su Lille da Chelsea da Real Madrid da kuma kasata Beljiyum.
“Ina kuma matukar godiya da jinjina ga ’yan uwana da abokan arziki da mashawarta da masoya baki daya wadanda suke kaunata.”
Hazard ya yi ritaya ne bayan ya kwashe shekara hudu a Real Madrid, inda kungiyar ta dauko shi domin ya maye gurbin fitaccen dan kwallon nan na duniya, Cristiano Ronaldo.
An dauko shi yana matukar tashe a Kungiyar Chelsea, inda ya lashe gasar Firimiya ta Ingila sau biyu, ya kuma zura kwallo 110 a wasa 352.
Sai dai zuwansa Real Madrid za a iya cewa kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, inda tun zuwansa yake ta tangal-tangal da rarrafawa.
A shekara hudun da ya yi, kwallo bakwai kawai ya zura, sannan ya taimaka aka zura kwallo 12 a wasa 76 kacal da ya buga a kungiyar.
Lallai ko shakka babu, kwallo bakwai a shekara hudu ga wanda ya zo ya maye gurbin Ronaldo abin kunya ne.
Aminiya ta taba ruwaitowa a lokacin da ya koma Real Madrid cewa shi da Neymar Jnr ne ake sa ran su iya maye gurbi tare da rufe taurarin Messi da Ronaldo da suka dade suna tashe a harkar kwallon kafa.
Sai dai a daidai lokacin da Messi da Ronaldo suka bar Turai, suka koma domin ba wasu matasa damar cinye harkar kwallo a Turai, shi Hazard ya yi ritaya ne, shi kuma Neymar ya bi sahun Ronaldo wajen tafiya Saudiyya da taka leda.
Hakan ya sa yanzu aka fi yin maganar Mbappe da Haaland, wadanda watakila za su iya danne Messin da Ronaldo, kan kuma za su iya yin karko na zaratan ’yan wasan.
A shekarar 2021 ce duk da dan wasan yana fama da rashin tashe, kasarsa ta Beljiyum ta sanya shi a cikin ’yan wasanta da za su buga Gasar Nahiyar Turai, inda aka yi tunanin a gasar ce zai dawo da martabarsa, amma kash! Rauni ya masa yankar kauna.
A lokacin hada-hadar cinikin ’yan wasa na Yulin 2021 ne, Real Madrid ta yi yunkurin mayar da shi Chelsea, amma kasuwancin bai kullu ba.
Bayan zuwan koci Ancelotti a matsayin sabon mai horar da Real Madrid, sai aka yi zaton dan wasan ya warware, inda a wasannin farkon kakar Hazard ya fara da kyau, har ya ci wajen Vinicius Jnr, amma nan ma aka koma gidan jiya, inda bai dade yana tashen ba ya sake salancewa.
Haka ya ci gaba da tatata har zuwa lokacin da Real Madrid ta sallame shi daga duk da yana da sauran lokaci a kwantaraginsa.
Bayan barin sa Real Madrid, rahotanni sun ce kungiyoyi da dama daga Saudiyya sun yi zawarcinsa, amma babu wadda ya amince ya je.
Haka kuma an ruwaito cewa zai zabi wata karamar kungiya a kasar Beljiyum domin ya ci gaba da taka leda kasancewar ana ganin yana da sauran lokaci a matsayinsa na mai shekara 32, amma wannan ma bai yiwu ba.
Ana cikin haka ne kwatsam ya sanar da ritayarsa daga harkar kwallo baki daya, inda ya ce zai mayar da hankalinsa a kan kula da iyalansa da sauran harkokinsa na yau da kullum.