Wani yaro dan shekara uku da haihuwa mai suna Muhammad Shamsudeen Aliyu wanda yake zaune a Sobon layi Tudun Wada a karamar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna ya haddace Alkur’ani gaba dayansa.
Muhammad wanda dalibi ne a makarantar Farfesa Ango Abdullahi da ke Zariya, ya kuma ci gasar karatun Alkur’ani ta duniya.
Aminiya ta tattauna da shugaban makarantar da yaron yake daukar darasin addinin muslinci tare da karatun zamani, mai suna Dokta Aliyu Shamsuddeen, inda ya ce, “Ni ne shugaban wannan makaranta mai suna Farfesa Ango Abdullahi, dama a makarantar muna daukar yara ne ’yan shekara daya da rabi zuwa biyu, bayan sun kammala shan nono, an yaye su, to mukan karbe su a matsayin dalibanmu, kuma daga jahohi daban-daban. Don haka lokacin da aka yaye wannan yaro mai suna Muhammad Shamsuddeen sai mahaifinsa ya kawo shi wannan makarantar a matsayin dalibin da zai rika kwana a makaranta kamar yadda aka kawo sauran abokanan karatunsa daga wadansu wuraren. Hikimarmu ta karbar kananan yara ’yan kasa da shekara biyu ita ce saboda kwakwalwarsu ta fi saurin daukar duk abun da aka fadi, walau na kirki ko akasin haka, to don haka idan suna hannunmu duk abin da za su ji ko za su fadi muna fatan kalma ce ta alheri.
Don haka da yaye Muhammad Shamsuddeen sai mahaifinsa ya karbe shi daga hannun mahaifiyarsa, a lokacinnan ita mahaifiyar tasa ta damu kwarai, duk da cewa akwai sa’anninsa a makarantar wadanda suka zo daga jahohin Katsina da Kano, amma duk da haka sai da ta damu. Sai bayan dan lokaci kadan da yaron ya fara fahimtar abubuwa kuma ta fara ganin irin hazakarsa sai ta hakura ta mika dukkan yardarta a kan karatunsa. Cikin lokaci kankani yaron ya haddace Alkur’ani tare da sauran wadansu littafai. Kuma ba shi kadai ba ne ya haddace Alkur’ani a matsayin wannan shekaru a makarantar nan, akwai ’yan uwan karatunsa wadanda shekarunsu kusan duk daya ne duk sun haddace Alkur’ani tare da wadansu littafai. Sai dai bambancinsa da sauran sa’anninsa shi ne, shi ya ci gasar karatun Alkur’ani wanda aka fara tun daga karamar hukumar Zariya a shekarar 2015 ya zo na farko, aka je ta jihar Kaduna, nan ma ya zo na farko, sannan kuma aka yi ta kasa baki daya a jihar Legas a nan ma ya kara yin na farko. Yana cikin wadannda suka wakilci Najeriya a gasar karatun Alkur’ani da aka yi ta duniya a Makka kasar Saudi Arebiya, inda ya yi na biyu a rukunin masu kananan shekaru irin nasa.
Shugaban makaranatar ya ci gaba da bayyana cewa, Muhammad Shamsuddeen Aliyu ya samu kyaututtuka da dama, kamar kyautar Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sunusi da kuma wanda ya samu a kasar Saudi Arebiya. Sannan kuma an ce ya zabi kasa daya da yake so bayan Saudi Arebiya da zai je yawon bude idanu a duniya, don ya je ziyarar gani da ido, sai aka zabar masa kasar Ingila.
Dakta Aliyu ya kara da cewa, “bayan haddace Alkur’ani da ya yi yana dan shekara uku da haihuwa, ya kuma haddace wadansu littattafai na addninin musulunci tare da sanin ilimin boko daidai gwargwado, wanda duk inda ka shiga ka fito a irin matsayin ajin rainon yara na 2 (Nursery 2) za ka same shi ya san abun da yake yi. Ka ji matsayin wannan yaro Muhammad Shamsuddeen da ya haddace Alkur’ani yana dan shekara uku tare da cin gasar karatun gasar Alkur’ani na duniya ke nan.’’
Wakilinmu ya tattauna da yaron bayan kammala jin ta bakin malaminsa inda cikin nishadi yaron ya dunga zuba karatu, duk surar da aka dauko masa daga Alkur’ani sai yaron ya ya cigaba da karanta surar da aka dauko masa tiryan-tiryan, sai dai kawai tsamin baki na yaranta, amma yaron ya karanci Alkur’ani tare da hadisan Mazon Allah (S.A.W.). A halin yanzu dai shekarun Muhammad hudu ne, ya haddace Alkur’ani a shekarar 2015 ne lokacin yana dan shekara uku.
Yadda dan shekara uku ya haddace Alkur’ani
Wani yaro dan shekara uku da haihuwa mai suna Muhammad Shamsudeen Aliyu wanda yake zaune a Sobon layi Tudun Wada a karamar Hukumar Zariya ta…
