✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda daliban Kano suka yi zanga-zangar adawa da yajin aikin ASUU

Daliban sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda yajin aikin ke kawo musu koma baya.

Dalibai a Jihar Kano da sauran sassan Najeriya sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadinsu kan yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ta shiga.

Zanga-zangar ta biyo bayan da umarnin da uwar Kungiyar Daliban Najeriya (NANS) ta bayar.

A Jihar Kano dalibai sun fara zanga-zangar ce daga karkashin gadar Kofar Nassarawa, sannan suka shiga Gidan Murtala don isar da sakonsu ga kwamishinar da ke kula da manyan makarantu.

An samar da jami’an tsaro na DSS da ’yan sanda daga Kofar Nasarawa zuwa dukkannin mahadan zuwa Gidan Gwamnatin Jihar Kano, da karkashin gadar Kofar Nassarawa.

A makon da ya gabata ne kungiyar NANS ta ce za ta kaddamar da zanga-zanga a manyan biranen Najeriya kan yajin aikin ASUU.

Daliban sun koka kan yadda ASUU da Gwamnatin Tarayya suke kawo wa harkar karatu koma baya, lamarin da suka ce na kashe harkar ilimi a kasar nan.

A jihohin Neja, Filato, Taraba da birnin tarayya Abuja, dalibai sun gudanar da zanga-zangar kin jin tsunduma yajin aikin gargadi na wata guda malaman jami’a suka shiga.