Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun na farautar wasu daliban makarantar sakandaren High Community School da suka sa ’yan daba suka lakada wa malamansu dukan tsiya.
Ana zargin daliban ne da daukar hayar wasu bata-gari da suka shiga makarantar, suka ji wa malaman nasu rauni, a Karamar Hukumar Yewa ta Jihar.
- Iyaye sun fara sayar da ’ya’yansu don sayen abinci a Afghanistan
- Hankalina ba zai kwanta ba sai na gaji Buhari a 2023 — Yahaya Bello
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ranar Litinin din da ta gabata, kuma malamai biyu sun sami rauni a sakamakon haka.
Maharan da aka yi hayarsun dai sun yi amfani da muggan makamai wajen dukan malaman, inda suka kira harin a matsayin wani mataki na yi wa malaman ‘gyaran hali’.
Wata majiya, ta bayyana cewar maharan sun mamaye makarantar da misalin karfe 10:45 na safiyar Litinin din, inda suka yi amfani da makamai irin su adduna da gatari.
Kakakin ’yan sandan Jihar, Abimbola Oyeyemi, ya ce tuni aka cafke tare da gurfanar da mutanen da suka kai farmaki makaranta a gaban kotu.
Lamarin dai ya biyo bayan wani malami ya hukunta wasu dalibai masu surutu a lokacin da yake koyarwa.
Rahotanni sun ce daya daga cikin dalibin da malamin ya hukunta ne ya yi hayar ’yan dabar wadanda suka yi aika-aikar.