Juyin wainar yajin Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) da Gwamnatin Tarayya ta sanya dalibai kokawa.
A farkon makon nan ne ASUU ta zarce da yajin aikin da take ciki da karin mako takwas.
Aminiya ta zanta da wasu dalibai daga jami’o’in Najeriya, inda suka bayyana damuwarsu kan yadda yajin aikin ke kawo musu koma baya ga harkar karatunsu.
Ina shiga jami’a aka fara yajin aiki
Auwalu Adamu da ke ajin karshe a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya cewa ya yi:
“A 2018 na samu gurbin karatu a aji biyu a fannin lissafi, saboda haka shekara uku zan yi, wato zan kara a 2021.
“Daga karbar takardar shaidar shiga jami’ata, kafin na fara karatu aka tafi yajin aikin wata uku, daga watan Nuwamba zuwa Fabrairu.
“Bayan an dawo daga yajin aiki aka sake tafiya wani na sati daya, wanda daga nan kuma Gwamnatin Tarayya ta bada sanarwar kullen COVID-19 wanda ya dauki tsawon tara zuwa goma.
“A yanzu kamata ya yi a ce muna yin hidimar kasa, amma ga shi sai yanzu muke a ajin karshe, yanzu kuma an tafi wani yajin aikin na wata daya.
“Ban tafi gida ba saboda ina tsammanin za a iya samun matsaya a kan matsalar, sai ga shi kuma ana cewa an kara wata biyu, to ni zan tafi gida saboda idan na zauna ban san lokacin da za a daina yajin aikin ba, domin na ga kamar gwamnati ta yi wa [lamarin] rikon sakainar kashi,” a cewar dalibin.
‘Gaskiya ban ji dadi ba’
Shi kuwa Hussaini Muhammad Muhammad da ke shekararsa ta biyu a Jami’ar Bayero ta Kano cewa ya yi: “Gaskiya ban ji dadi ba, mu da muke so mu yi mu gama, kuma ai ta tafiya wannan yajin aiki haka ai ba dadi, ai ba wanda zai ce ya ji dadi kan wannan lamari.
“Abin da zan yi kawai shi ne addu’a zan yi Allah Ya sa hakan ya zama shi ne mafi alheri.
“Kuma zan dukufa wajen nema don ganin na rufa wa kaina asiri kafin lokacin da za a dawo, na dan nazarin abubuwan.”
‘Neman kudi kawai zan rika fita’
Musa Ibrahim Umar, dalibi ne da ke ajin karshe a fannin karantar Ilimin Koyar da Kwamfuta a Jami’ar Jihar Bauchi da ke Gadau ya shaida wa Aminiya cewa:
“Gaskiya bayan ASUU ta kara wa’adin wannan yajin aikin mun tsinci zuciyoyinmu a cikin bacin rai da bakin ciki, saboda wasu suna so su kammala karatunsu, wasu kuma yanzu suka fara.
“Kuma mu matasa ne da muke da tsari a rayuwarmu, wasu ba su da sana’a sun fi so sai sun kammala karatu su samu aikin yi, amma ka ga duk an dakatar, komai ya tsaya, saboda Allah da yawanmu ba mu ji dadin wannan al’amari ba.
“Ni yanzu shirin da na sa a gaba shi ne zan rika fita neman kudina kawai na kuma kwantar da hankalina, duk lokacin da ASUU ta dawo sai na koma na karasa abin da ya rage min.
“Na watsar da lamarinsu na kama abin da ya fi min muhimmanci,” inji shi.
Ba su damu ba saboda ’yaransu na karatu a waje
Ita kuwa Aisha Muhammad Danlami, daga Sashen Nazarin Aikin Noma a Jami’ar Bayero ta Kano cewa ta yi: “Yawancin malaman da jami’an gwamnatin ba za su damu ba saboda ’ya’yansu ba a kasar nan suke karatu ba.
“Misalin idan ka duba a watan Fabrairu ana tsaka da yajin aiki, tsohon Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Abubakar Adamu Rasheed, ya je Landan wajen bikin yaye dansa daga jami’a, saboda Allah ta yaya za su damu da karatun dan talaka?”
Na bar wa Allah komai
Maryam Ilu daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil a Jihar Kano, ta bayyana damuwarta kan yadda yajin aikin ASUU ya sa har yanzu ba ta kammala karatu ba.
“A baya COVID-19 ta hana mu gama karatu, yanzu mun dawo an tafi yajin aiki, an sake yin wani.
“Yanzu abin da ya rage min na kammala karatun shi ne a duba min kundin bincikena da nake aiki da a kai.
“Ni yanzu na bar komai a hannun Allah, zan koma gida tunda azumi na karatowa na je na yi ibadata cikin nutsuwa, tunda abin ya zama haka,” inji ta.
Ina da abubuwan yi
Tasiu Sani daga Jami’ar Alqalam da ke Jihar Katsina, ya ce in dai yajin aikin ASUU ne to umma ta gaida assha.
“Ni fa ba zan damu ba saboda komai suke yi ba don mu ake yi ba, suna yi ne don biyan bukatar kansu.
“Ina da abubuwa da dama da nake yi, ka ga kuwa ba zan tsaya ina jiran tsammani ba, ya rage nasu, su dawo ko kar su dawo.”
Gwamnatin ta yi sakainar kashi
Ita ko Hanifa Ismail Sagir, daga Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Jihar Bauchi, ta fi ganin laifin Gwamnatin Tarayya a takaddamar yajin aikin.
“Ni fa gaba daya na fi ganin laifin gwamnati kan wannan yajin aikin; Misali idan aka duba yadda shi kansa ilimin ke samun koma baya a duk lokacin da aka zo yin kasafin kudi.
“Sai nake ganin kamar gwamnati ba ta damu da bangaren ba, amma ko ma mene ne yana da kyau a ce ana duba makomar rayuwar ’ya’yan talakawa.
“Amma muna fata Allah Ya sa su yi sulhu ta yadda za a dauki lokaci mai tsayi ba tare da an sake shiga wani yajin aikin ba, saboda ni yanzu ma na fara karatun,” cewar Hanifa.
A faron watan Fabrairu ne ASUU ta sanar da shiga yajin aikin mako hudu, kan rashin biyan wasu bukatunta da Gwamnatin Tarayya ta yi.
A farkon makokn nan kuma ta sanar da tsawaita wa’adin yajin aikin da wata biyu domin a cewarta ta ba wa gwamnati damar kammala aikin da take son yi kan bukatun kungiyar, wanda gwamantin ta ce za ta kammala a cikin mako shida.