Tun bayan da annobar coronavirus ta barke a Najeriya ne aka rufe makarantu, lamarin da ya tilasta wa dalibai da dama, musamman mata, zaman gida.
Sai dai kuma bai kamata a ce saboda ba kya zuwa makaranta ba, shi ke nan sai ki rika zama dagaje-dagaje.
Da farko dai, mata kun san cewa tsafta da ado su ne ’ya mace. Mace in ba ta kwalliya da tsafta ko babu inda za ta je, ba za ta ji dadin jikinta ba.
Akwai hanyoyi da dama da za ki iya gyara kanki a gida ko ba fita za ki yi ba; ga wasu daga cikinsu:
- Wanka
Yana da muhimmanci a yi wanka akalla sau ɗaya a rana – in so samu ne a yi sau biyu: da safe da kuma yamma.
Idan zai yiwu ki yi amfani da man wanka, wato shower gel, ko sabulu domin tsaftace jikinki.
- Shafa mai
Bayan an sha wanka, yana da muhimmanci a shafa man shafawa wanda zai sanya fata ta yi taushi da kuma kamshi.
Idan akwai hali, zai yi kyau ki yi amfani da shea butter; idan babu kuma sai ki yi amfani da basilin.
- Kula da gashin kai
Bayan jikinki, gashinki ne abu na biyu da ya kamata ki kula da shi.
Zai yi kyau ki yi amfani da sabulun shampoo don tsaftace gashin kanki.
Bayan kin wanke shi sai ki busar da kan sannan ki shafa masa mai ki taje shi.
Idan gashin mai tsawo ne kada ki yi amfani da kayan gashi saboda suna iya lalata maki shi ko kuma su sanya shi ya bushe sosai kuma ya yi wahalar sarrafawa.
- Saka turare
Yana da kyau ki yi kamshi sosai saboda kamshi shi ne mutum ai – ke kanki idan kika yi wanka kika sa turare za ki ji dadi kowa kika wuce a gidan sai ya ji kina kamshi mai dadi ba wai sai za ki makaranta ne za ki sa kayan kamshi ba.
- Tufafi mai kyau
Mata da dama za ku ga ba sa son sa kaya masu kyau. Irin wadannan mata kan ce tun da ba fita za su yi ba me ya sa za su yi ado? Sun gwammace su daura zani iya kirji abinsu.
Yana da kyau ko ba za ki fita ba ki sa kaya mai kyau, ki yi ado.
Ko da kun yi bakin kunya ne za ki iya fita ku gaisa ba sai an yi baki ki fara neman kayan sawa ba.
Za ki iya sa riga da wando, ko doguwar riga, ko riga da zani – duk dai wanda ya kwanta miki a rai.
Bayan kin sa kayanki, sai ki sha daurinki mai kyau, ki shafa hoda – za ki iya amfani da Classic saboda kada fuskarki ta yi maiko kuma ki yi kyau.
Sai ki dan ja ja-girarki; za ki iya sa janbaki in kina so.
Ke kanki za ki ji dadi a ranki kuma za ki yi kyau har ki dau hotuna masu kyau.
Sai dai kuma, kada a manta a rika bitar karatu don kada idan an koma makaranta a sha wahalar fahimta.