✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda COVID-19 ke kawo cikas a gasar Firimiyar Ingila

Akalla mutum 103 ne na gasar Firimiyar Ingila suka harbu da COVID-19.

Cutar COVID-19 na ci gaba da kawo koma baya a harkokin yau da kullum, ciki har da gasar kwallon kafa ta Firimiyar Ingila, inda ake ci gaba da dage wasanni.

Tun a satin da ya gabata ne aka fara dage wasannin gasar sakamakon yadda cutar ke yaduwa a tsakanin ’yan wasan kungiyoyi.

Wasu sabbin alkaluma sun bayyana cewa ’yan wasa da ma’aikatan gasar 103 ne suka kamu da COVID-19 a cikin mako guda.

Hukumar Kwallon Kafar Ingila na duba yiwuwar dakatar da gasar ko kuma hana ’yan kallo shiga filayen wasanni, sai dai kungiyoyi sun yi watsi da wannan shiri.

An yi wa mutum 15,186 gwajin cutar daga ranar 20 zuwa 26 ga watan Disamban 2021, a yayin da hukumomin gasar suka sake kaddamar da matakin yin gwaji a kullum kan ’yan wasa da ma’aikata.

An soke gudanar da manyan wasannin gasar Firimiya a watan Disamba saboda yadda cutar ke addabar ’yan wasan kungiyoyin gasar.