Manoman Ƙaramar Hukumar Mokwa da ke Jihar Neja sun koka kan ƙaruwar kisan da maciji ke yi a gonakinsu a lokacin da suke girbe amfanin gona.
Ɗan majalisar da ke wakiltar Ƙaramar Hukumar Mokwa a majalisar dokokin jihar, Ndagi Zakari ne ya bayyana haka a madadin manoman da ke mazaɓarsa a zauren majalisar, inda ya ce abin mamaki ne yadda ake yawan samun mace-macen jama’a sanadiyyar cizon maciji.
- ’Yan ta’adda sun kashe manyan hafsoshin soji 6 a Chadi
- Manoman Benuwe sun samu sabuwar manhaja don bunƙasa hanyoyin samun kuɗin tallafi
Ya ce, waɗanda lamarin ke rutsawa da su macizan na kai masu farmaki ne a kan hanyarsu ta zuwa gona.
Ɗan majalisar ya ce, duk da yawan saran maciji da ke haddasa asarar rayuka, ba a samun allurar riga-kafin dafin maciji a asibitocin ba saboda tsadar allurar, inda ya ce ta kai kimanin Naira 200,000, wanda manoman ba su da kuɗin da za su saya.
Ya yi nuni da cewa, lokacin girbi a kan sami yawaitar matsalar saran maciji, inda ya bayyana cewa macizan kai farmaki ga manoman da suke girbin amfanin gona.
Ya nuna takaicinsa a kan yadda waɗanda abin ya shafa kan yi amfani da hanyoyin gargajiya, wanda a ganinsa ba ta da aminci kuma ba abin dogaro ba ce sakamakon rashin samun magani.
A cikin ƙudurinta, majalisar ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta shiga tsakani ta hanyar samar da alluran rigakafin dafin kyauta ga cibiyoyin kiwon lafiyar jama’a a faɗin jihar domin rage yawan mace-mace.