✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda cacar betin ke kashe shauki da kaunar wasan kwallon kafa

kwallon kafa an san ta da hada mutane daban-daban wuri daya. A fagen taka leda babu kabilanci da nuna bambancin addini duk da cawa a…

kwallon kafa an san ta da hada mutane daban-daban wuri daya. A fagen taka leda babu kabilanci da nuna bambancin addini duk da cawa a ’yan kwanakin nan ana samun matsalolin nuna wariyar launin fata.

A duk lokacin da ake buga wasa, masoya kungiyoyi suna nuna matukar sha’awa da burin ganin kungiyar da suke so ta samu nasara a kan abokiyar hamayyarta. Wadansu sukan yi kuka da nuna bakin ciki matuka idan aka doke kungiyar da suke so.

Ana cikin haka ne, sai kwatsam cacar betin ta kunno kai a cikin wasannin. Ita dai cacar ta betin an assasa ta ce domin ta kara shaukin kwallon ga masoya kamar yadda Turawa a kasashen waje suke yi. Ana cikin haka kawai sai aka fara sauya dalilin da ya sa aka assasa cacar.

Yadda ake yin cacar shi ne, mutum zai sayi tikitin cacar a kan  misali Naira 100. Sai ya canki yadda wasan zai kaya. Misali zai iya cewa kungiya kaza za ta samu nasara da ci kaza. Ko ya ce kungiya kaza za ta samu nasara amma ita ma dayar kungiyar za ta zura kwallo koda kuwa za a doke ta. Ko kuma za a yi kunnen doki.

Kowane wasa akwai yanayin kudin da za a samu da ake kira odd. Idan cankar da ka yi ta zamo daidai, sai a duba yanayin odd din da ka canka sai a ba ka kudin da ka samu.

bangaren da ya fi tsada shi ne mutum ya canki yadda wasa zai kaya da wadanda za su zura kwallo da kungiyar da ta fara zura kwallo da ko za a zura kwallon kafin hutun rabin lokaci ko sai an dawo.

A wanan cacar mutum na iya saka Naira 100 ya samu dubban nairori a  cikin ’yan mintuna duk da cewa mutum yakan zabi wasanni da yawa kuma dole sai abin ya da canka ya yi daidai a duk wasannin da ya zaba din. Idan misali ya zabi guda 8, sai 7 suka zama daidai da abin da ya canka, aka samu matsala a daya, to shi ke nan ba zai samu ko sisi ba. Shi ne za a ji suna cewa an yanka min tikiti.

Matsalar da wannan cacar take haifarwa ita ce: duk lokacin da za a buga wasa, kasancewar an dade ana kallon wasannin kowace kungiya, kuma an san abin da za ta iya, musamman idan an san lokacin tana tashe, sai kawai a canki cewa za ta samu nasara.

Masoya kwallon kafa da aka san su da akidar kungiyar da suke kauna tare da kasancewa tare da ita komai wuya ko dadi, sai ga shi yanzu a sanadiyar wannan cacar abin ya sauya.

Idan za a kece raina tsakanin kungiyar da mutum ke so da wata babbar kungiyar, idan mutum ya san cewa wancan kungiyar tana tashe, maimakon ya je da fatar kungiyarsa ta samu nasara, sai kawai ya canki cewa za a doke kungiyarsa, sai kuma ka ga ya je gidan kallo yana fata a doke kungiyarsa domin ya samu kudi. Idan ma ya ga alamar cewa kungiyarsa za ta samu nasara, sai ka ga ya shiga cikin damuwa da rashin jin dadi. Idan kuwa ta samu nasara, maimaikon ya yi murna sai ya shiga bakin ciki da damuwa.

Baya ga bata harkar kwallon kafa da kashe shaukin da ke cikinta, cacar betin tana janyo rikici a harkar. A sanadiyar cacar nan, an sha samun labarin fada ya kaure a tsakanin mutane, a wani lokacin har asarar rai ake yi. Kuma tana janyo tabarbarewar tarbiyya da raini a tsakanin yara da manya. Uwa uba kuma, cacar ta dawo da cacar da addini ya hana cikin wani nau’i da har da wadanda suke kin caca yanzu suna shiga ciki dumu-dumu.