Wani mutum ya shiga hannu bisa zargin sa da kokarin kwakule idanun wani jariri domin hada layar bata a unguwar Hotoro ta Karamar Hukumar Nasarawa, Jihar Kano.
Dubun bokan ta cika ne bayan ya yi wa wani mutum romon baka cewa zai ba shi kyautar Naira miliyan takwas da babbar mota matukar ya kawo masa jariri dan uwansa domin a kwakule masa idonsa na hagu don yin tsafi.
- An cafke mata bisa zargin satar jariri dan wata shida
- Cinikin jariri: Masarautar Kano ta kori mai anguwar Fagge
Hakan ce ta sa wanda aka yi wa romon bakan zuwa gidan yarsa da nufin daukar danta ya kai wa bokan, yana mai shaida mata cewa saura kiris su kudance.
Jin hakan ne ya sa hankalinta ya tashi har ta yi kokarin ganin hankalinsa ya dawo jikinsa saboda girman abin da bokan ke kokarin sa shi ya aikata tare da nuna masa cewa romon baka ne kawai ake masa.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce tuni bokan ya shiga hannunta kuma tana fadada bincike a kansa.
Kakakin Rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an cafke bokan ne bayan wanda aka fara zargin ya je wurinsa ne da nufin neman lafiya.
Kiyawa ya ce, “Bayan mutumin ya je wajen bokan sai [bokan] ya ba shi wani magani ya kuma umarce shi da ya rika hadawa da fitsarinsa yana wanka da shi na tsawon kwana uku.
“Da ya dawo bayan kwana uku sai [bokan] ya ba shi wani rubutu ya yi amfani da shi, wanda yin hakan ne ya sa kansa ya juye ya fara yin duk abin da bokan ya umarce shi, har zuwa ranar da ya ce ya je ya samo jaririn da za a kwakule wa idanu domin hada layar batar.
“Da jin hakan sai ya fada wa yayarsa abin da ake ciki, yana rokon ta bayar da dan cikinta domin a yi amfani da shi wajen hada wa wani soja layar zana.
“A nan ne hankalin yayar tasa ya ta shi inda ba su yi wata-wata ba suka kai shi kara ofishin ’yan sanda”, inji Kiyawa.
Ya ce daga nan ne suka kai wa ’yan sanda bokan kara wanda su kuma ba su yi wata-wata ba wajen cafke shi.
Jami’in ya ce sun samu likkafani, kasa, kwarya dauke da rubutu da sauran ababuwan tsubbu a lokacin da suka kama shi bokan.
Kiyawa ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Habu Sani ya umarci a fadada bincike kuma da an kammala za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya.