✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda bikin Ranar Shan Fura ta Duniya zai gudana

Qungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore ta ayyana 13 ga watan Disamba a matsayin Ranar Bikin Shan Fura ta Duniya domin farfaxo da kyawawan…

Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore ta ayyana 13 ga watan Disamba a matsayin Ranar Bikin Shan Fura ta Duniya domin farfaɗo da kyawawan al’adun Fulani a Nijeriya da dama duniya baki ɗaya.

Shugaban Kungiyar, Alhaji Bello Badejo, ya shaida wa wakilin Aminiya cewa sun shirya tsaf domin kaddamar da bikin ranar a bana.

Bello Bodejo wanda ya ne rangadin Legas domin kaddamar da sabbin shugabannin kungiyar a Jihar, ya ce daga wannan lokaci za a ci gaba da yin bikin a duk shekara domin farfado da kyawawan al’adu na Fulani.

“Za mu qaddamar da wannan buki ne a Kasuwar Shanu ta Maliya da ke Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa, kuma muna sa ran Fulani daga sassan Nijeriya da ma kasashen masu maqwbataka za su hallara domin gudanar da wannan buki na al’ada,” in ji shi.

Ya ce Fulani makiyaya a Nijeriya mutane ne masu dadadden tarihi, kuma a matsayinsa na shugaban qungiyar raya al’adun gargajiya na Fulani a kodayaushe, yana kokarin jaddada kyawawan al’adun Fulani, “domin abin da ake so a shugabanci shi ne bijiro da abun da zai bunkasa al’umma da kawo ci-gaba tare da dakile abubuwa marasa kyau.

“Faman fura jigo ce a al’adun Fulani, kuma a yanzu hatta wadanda ma ba Fulani ba ne suna sha’awar ta, suna sha a matsayin abinci ko abun sha.

“Don haka wannan buki zai ba da gudunmawa sosai wajen wanzuwar hadin kai a tsakanin al’ummar Fulani da abokan zamansu a duk inda suke.”

Bello Bodejo ya kuma yi kira ga daukacin shugabannin kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore na jihohi da suyi koyi wajen farfado da al’adun Fulani su kuma tabbatar da hadin kai da zaman zaman lafiyar al’ummarsu.

A cewarsa, zai ci gaba da fafutukar wanke kashin kaji da aka goga wa al’ummar Fulani, a fadin qasar nan, domin Fulatanci yana nuna kawaici da kunya ladabi da kuma biyayya da bin doka, wannan ita ce al’adar Fulani ta asali, kuma ba za su gushe ba za su ci gaba da asassa wannan kyakyawar al’adar.