Ranar 26 ga watan Agusta ita ce aka ware domin bukuwawan ranar Hausa a kowacce shekara.
An fara bikin ranar ce a shekarar 2015 kuma ta samo asali a kafafen sada zumunta na zamani ta yadda a ranar da masu magana da harshen za su hadu su tattauna ci gaba da kalubalen da harshen ke fuskanta da kuma duba yadda za a kara bunkasa shi.
Taken bikin na bana dai shi ne, “Bukatar Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU da ma Kungiyar ƙasashen Raya Arzikin Yammacin Afirka ta ECOWAS su sanya harshen Hausa a jerin harsuna sadarwarsu”.
A wannan shekarar, bikin ya dauki wani sabon salo inda aka shirya wani gagarumin taro da ya tattaro masana da manazarta kan harshe da kuma adabin Hausawa domin gabatar da makaloli gami da tattaunawa a fadar sarakunan Daura da ke Jihar Katsina da kuma Rano da ke Jihar Kano, biyu daga cikin garuruwan Hausa bakwai masu dimbin tarihi.
Hausa dai an yi ittifakin shi ne harshen da aka fi amfani da shi a nahiyar Afirka Kudu da hamadar sahara.
A al’adance dai a irin wannan rana, masu amfani da shafukan kan tattauna batutuwan da suka shafi Hausawa har ma da wadanda ba Hausawan ba, amma suke magana da Hausa a duniya.
Galibi mutanen kan yi amfani da maudu’i #RanarHausa domin fito da sabbi ko kuma tsofaffin karin maganar da ba kowa ne ya san su ba domin kayatar da mabiyansa.
Masana da manazarta da dama dai na kallon harshen a matsayin daya daga cikin wadanda suka fi saurin yaduwa a duniya.
A ‘yan shekarun da suka gabata wani bincike ya nuna cewa Hausa shi ne harshe na 11 da ya fi yawan masu amfani da shi a duniya inda aka yi hasashen akwai masu amfani da shi sama da miliyan 150 a fadin duniya.
Masu amfani da harshen dai na zaune ne a kasashe kusan 32, gabili a Afrika ta Yamma, wani bangare na Afirka ta tsakiya da ma wani sashe na Arewacin Afirka.