Akalla wayoyi 17 ne wasu barayi suka sace a ginin dakin kwanan dalibai mata na Ramat da ke sabuwar Jami’ar Bayero ta Kano.
Lamarin ya faru da misalin karfe 2 na daren ranar Litinin, wanda hakan ya haifar da rudani mai a tsakanin daliban mata.
- Shekara 8 da rasuwan Sheikh Auwal Albani Zariya
- ‘A kan idon sojoji ’yan bindiga suka sace mana mutum 50’
Wata daga cikin daliban da ta bukaci a sakaya sunanta, ta ce wasu daga cikinsu sun farka cikin dare ne suka iske wayoyinsu sun yi batar-dabo yayin da suke shirin yin karatun dare da misalin karfe 3 na daren ranar.
Ta ce sun rufe kofar dakinsu kafin su yi barci, amma abun mamaki sai suka farka suka iske kofar a bude.
A cewarta bayan faruwar lamarin nan take suka sanar da jami’an tsaron da ke ginin dakin kwanan dalibai, wanda aka ce su shigar da kokensu ga ofishin jami’an tsaron jami’ar.
Wata daliba ta ce sun yi mamakin yadda jami’an tsaron jami’ar suka kasa yin komai game da faruwar lamarin, amma suka zargi wadanda aka sace wa wayoyin da yin sakaci.
Ta ce, “Wasu daga cikin wayoyin da aka dauke na makudan kudade ne, wasu wayoyin iPhone sabbin fitowa ne kuma in har barayin waya za su fita ba tare da an cafke su ba akwai yiwuwar masu shigowa don yi wa dalibai fyade za su iya tsira, wannan shi ne dalilin damuwarmu.”
Har wa yau, wasu bayanai sun bayyana cewa bayan an kira wasu daga cikin wayoyin da aka dauke an ji muryar namiji ce ke amsawa, amma daga bisani sai aka kashe wayoyin.
Ko da aka tuntubi mai magana da yawun Jami’ar, Lamara Garba, ya yi alkawarin gudanar da bincike tare da yi mana karin haske.
Sai dai wata majiya daga mahukuta jami’ar ta bayyana cewa an gano wayoyi 12 ne aka sace, kuma ana zargin daya daga cikin dalibai matan ce ta dauke su, saboda babu wata alama da ta nuna an yi amfami da karfi wajen shiga dakin kwanan daliban.
Amma ya ce ana ci gaba da gudanar a bincike kan lamarin, don gano hakikanin abin da ya faru a ranar.