Wata daliba da ke karatun aikin jinya a makarantar City College of Science and Tecnology da ke Zariya, ta rasa ranta sanadiyyar daba mata wuka da wani da ake zargin barawon ne, a yunkurinsa na kwace wayar da take rike da ita a hannunta.
Dalibar mai suna Fauziya Bello mai shekara 19, wadda ’yar asalin Jihar Neja ce, tana shekarar farko ne a makarantar kafin ta gamu da ajalinta.
Binciken da Aminiya ta gudanar kan kisan gillar da aka yi wa Fauziya, ta fahimci cewa a ranar Juma’ar da ta gabata ce da misalin karfe tara na dare, marigayiyar tare da abokiyar karatunta suka fita zuwa wajen da ta bayar da cajin wayarta, inda a kan hanyarsu ta komawa gida ne sai kawar ta lura cewa akwai wanda ke bin su, kuma ba ta gamsu da shi ba. Sai ta shaida wa marigayiyar cewa ba ta yarda da yanayinsa ba. Sai marigayiyar ta ce mata ba abin da zai faru.
A cewar majiyar tamu, sai kawai mutumin da ke biye da su, a daidai Unguwar Madaci ya kama jakar da Fauziya ke goye da ita bisa tunanin ta sanya wayar da ta karbo daga caji a ciki, inda kokuwa ta kaure a tsakaninta da shi, ita kuma abokiyarta ta ruga da gudu tana kururuwar neman dauki daga jama’a. Sai dai a cewar majiyar kafin a kai mata dauki, mutumin ya daba mata wuka a kahon zuciyarta, inda ta fadi cikin jini. Shi kuma ya dauke jakar wadda littattafai da sauran muhimman takardunta ke ciki, ya gudu ba tare da ya samu nasarar kwace wayar da ke hannunta ba.
Bayan da aka kai wa ’yan sanda rahoton abin da ya faru Fauziya Bello ne suka dauke ta zuwa asibiti, inda likita ya tabbatar musu da cewa rai ya yi halinsa.
Irin wannan hadari da dalibai ke tsintar kansu a daidai wurin da aka kashe Fauziya shi ne kusan na 20, inda ake sukar dalibai da wuka a kwace musu kayayyaki a Unguwar Madaci.
Dalibai da dama da Aminiya ta zanta da su a kan kisan Fauziya sun nuna takaicinsu ne kan yadda a kullum ake tare dalibai a wannan wuri, al’amarin da ke kara yawaita a lokaci-lokaci.
Kodayake a baya daliban sun taba kama daya daga cikin masu tare su, suka mika wa ’yan sanda aka kai shi kotu da nufin doka ta yi aiki a kansa, a cewarsu abin mamaki, kasa da mako daya da kai shi gidan yari, sai ga shi ya fito yana yawo a gari.
Aminiya ta ziyarci ofishin ’yan sanda na Dan Magaji, inda DPO Daniel Moses Pam ya ce bayan sun samu labari sun je inda lamarin ya faru suka dauki dalibar zuwa asbiti, inda likita ya tabbatar da mutuwarta; sannan aka dauke ta zuwa gida domin yi mata jana’iza. Ya ce zuwa lokacin hada rahoton nan ba su kama kowa ba amma suna bin diddigin lamarin. Ya ce ya sanar da babban ofishinsu da ke Kaduna kan lamarin.
Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, DSP Yakubu A. Sabo don sanin inda aka kwana, sai ya nemi a ba shi dan lokaci domin ya gana da Kwamishinan ’Yan sandan jihar, domin yi mata bayanin halin da ake ciki. Amma har zuwa hada wannan rahoto bai ce komai ba.