Majalisar Tarayya ta nemi Gwamnatin Tarayya ta karfafi Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Kasa da sauran hukumomin tsaro domin magance yawaitar fasa gidan yari a Najeriya.
Majalisar Wakilai ta yi kiran ne bayan da dan Majalisa Ifeanyi Chudi
Momah, ya bayyana cewa balla gidajen yarin sabon kalubale ne da ya kara ta’azzara barazanar tsaron da ke addabar kasar.
- Fursunoni sun yi bore a babban gidan yarin Kano
- Muna tare da Pantami 100% —Buhari
- Direba da kwandasta sun yi wa mai cutar HIV fyade
- Ya auri kanwarsa da ta bace tun tana jaririya
Momah ya ce hare-haren da fasa gidajen yarin a baya-bayan nan da ake zargin hannun wasu bata-gari daga cikin gida da kasashen waje, an bukatar daukar mataki.
A zaman nata, Majalisar ta bukaci Kwamturola-Janar na Hukumar, da ya gaggauta tura karin jami’ai masu dauke da makamai domin dakile yiwuwar fasa gidajen yari a nan gaba.
Ta kuma yi kira da a yi wa dokar Majalisar Tsaron Kasa gyaran fuska ta yadda za a sanya Kwamturola-Janar na Hukumar a ciki.
Jin kadan da zaman Majalisar, a yammacin ranar Alhamis, fursunoni a babban gidan yarin Kano da ke unguwar Kurmawa a Jihar Kano da tarzoma.
Aminiya ta gano cewa tarzomar ta barke ne a gidan jim kadan da yin bude baki, bayan da fursunoni suka ta da kayar baya saboda kwace wata tabar wiwin da aka yi musu fasakwaurinta.
Hukumar dake Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS) reshen jihar Kano ta tabbatar da lamarin, amma ta ce jami’anta sun yi ta maza wajen dakile yunkurin.