A wani abu mai kama da ba saban ba, a bana an samu mace Bahaushiya ’yar asalin Jihar Kano da ta zama sojar Najeriya.
Amina Nuhu, ’yar shekara 21 na daga cikin sojoji 452 da aka yaye a diba ta 79 daga Makarantar Horar da Kuratan Sojojin Najeriya da ke Zariya.
Amina wadda ita ce kadai Bakanuwar da aka yaye a bana ta ce ta shiga aikin soja ne goyon bayan mahaifiyarta mai burin ganin an samu soja a zuri’arta.
Dalilin barin ’yata ta shiga aikin soja –Mahaifiyar Amina
A tattaunawarta da Aminiya, alama Maryam Sani wata mahaifiyar sojar ta ce diyar tata ta dadewa tana son ta bauta wa kasa.
“Tun tana karama take ce min tana da burin ta ga ta hidimta wa kasa, to ko lokacin da ta fara nema nakan yi addu’a in fada wa Allah in dai akwai alheri a ciki Allah ya tabbatar, in kuma babu ya musanya mata da mafi alheri”, inji mahaifiyar.
Ta kara da cewa, “A ranar da ta kawo min takardun shaidar ta samu, na yi mata addu’a da fatan alheri. Ni duk abun da dana yake son ya zama ko ya karanta matukar ba sabon Allah ba ne zan bar shi.
“Su bakwai ne ’ya’yana kuma Amina ce ’yar autarsu.
“Ba mu samu wata matsala daga ’yan uwa ko dangi ba a lokacin da ta samu aikin sojan, hasali ma sai san-barka da fatan alheri da muka yi ta samu”, inji Malama Maryam.
‘Abin da ya karfafa min gwiwa’
A hirarta da wata jaridar kafar sadarwa ta zamani mai suna Kano Focus, sojar ta ce mahaifiyarta ta yi tsayuwar daka wajen ganin burin nata ya cika.
“Da ma ni kuma na dade ina son shiga aikin, amma abun da ya kara karfafa min gwiwa shi ne yadda mahaifiyata ta karfafa min gwiwa, wanda ba kasafai ake samu a tsakanin Hausawa mata ba”, inji Amina.
Ta ce hakan ya ba ta kwarin gwiwar ta shiga aikin, tana mai alkawarin yin bakin kokarinta wajen ganin ta zama abin alfahari.
Ba kasafai ake ganin mata Hausawa Musulmai na shiga aikin soja ba musamman a jiha irin Kano wadda yawancin al’ummanta Hausawan ne.
Hakan ce ta sa wasu ke tantamar ko Amina cikakkiyar Bahaushiya ce.
‘Ni Bahaushiya ce gaba da baya’
Da take katse wa masu wancan tunani hanzari, Amina ta ce ita cikakkiyar Bakanuwa ce kuma haiffiiyar Kano.
“Mahaifina dan asalin garin Dan-Hassan ne a Karamar Hukumar Kura, mahaifiyata kuma ’yar asalin unguwar Fagge ce, saboda haka ni Bakanuwa ce gaba da baya.
“Ni kuma haifaffiyar unguwar Gyaranya ce da ke Karamar Hukumar Gwale da ke cikin kwarar birnin Kano, don haka idan na ji masu cewa ni ba Bahaushiya ba ce sai dai kawai in yi dariya”, inji ta.
Ta yi makantar firamare a unguwar Warure, sai kuma makarantar sakandaren ’ya’yan sojoji da ke Kano, inda a nan ta fara sha’awar aikin soji.
Aure a gidan soja
Ga msu tunanin yaya za ta yi aure tana soja kuwa, ta ce tuni aka yi musu baiko da wani soja abokin aikinta, kuma nan ba da jimawa ba za su sha biki.
Kan batun kalubalen da take fuskanta daga masu suka kan shigar ta soja, musamman a kafafen sada zumunta, Amina ta ce ko a jikinta.
Ta ce, “Tun lokacin da na zama cikakkiyar soja bayan fitowa daga sansanin ba da horo, jama’ar unguwarmu ke ta nuna farin cikinsu da alfahari da ni, suna kuma kara karfafa min gwiwa.
“Mutane sun yi ta tururuwa zuwa gidanmu don yi min fatan alheri, kai idan na fita ma har mutane ke tara ta suna so su dauki hoto tare da ni, wannan yana burge ni matuka”, a cewarta.
Amina wacce marainiya ce ta ce aikin zai ba ta damar kula da kanta da ma mahaifiyarta.
A nata bangaren kuwa, mahaifiyar sojar ta yi kira ga sauran iyaye Hausawa da su daure su rika kyale ’ya’yansu mata da suka nuna sha’awar shiga aikin don bayar da tasu gudunmwar.
Ta ce babban burinta a rayuwa shi ne ta ga diyar tata ta zama abin kwatance ba a tsakanin takwarorinta.