✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ambaliyar ruwa ta haifar da tsadar shinkafa a bana

An shawarci kananan manoma su daina gaggawar fitar da abin da suka noma don gudun fadawa cikin matsalar yunwa.

Ambaliyar ruwa ta kara haifar da tsadar shinkafa da sauran albarkatun gona a bana a wasu kasuwannin Jihar Kaduna.

Wakilinmu ya ziyarci wasu daga cikin kasuwannin, inda ya gano cewa, buhun shinkafa mai nauyin kilo 100 ana sayar da shi N19,000 zuwa N21,ooo, maimakon N13,000 a kakar bara.

Shi kuma buhun waken suya ya sauka kasa saboda bara an sayar da shi ne a kan N28,000 amma a yanzu ana sayar da shi N22,000 zuwa N24,000.

Sai kuma buhun masara ana sayar da shi a kan N16,000 ne maimakon N14,000 a kakar bara.

Shi kuwa buhun farin wake, ana samun sa a kan N44,000 saboda ba a shiga kakarsa ba.

Shugaban ’Yan Kasuwar Hatsi na Kasuwar Tudun Saibu da ke Karamar Hukumar Soba, Alhaji Sani Maimasara Soba, ya shaida wa wakilinmu cewa farashin na iya dagawa zuwa nan gaba kadan saboda kamfanoni za su fara saye don ajiya.

Shugaban Kungiyar Manoma da Sarrafa Masara ta Jihar Kaduna, Dokta Mohammed Lawal Mai Shano, ya ce akwai yiwuwar farashin ya karu saboda matsalar tsadar takin zamani da manoma suka fuskanta a daminar bana.

Don haka ya shawarci kananan manoma su daina gaggawar fitar da abin da suka noma don gudun fadawa cikin matsalar yunwa.

Kuma ya yi kira ga gwamnati ta dan tsagaita wa kananan manoman da suka karbi bashin noma saboda ambaliyar ruwa da ta lalata gonakinsu.